22/07/2020
SA'ADATUL ANAAM
--------------------------------
DARASI: 002
---------------------------------------------
--------------------
Asalm alaikum waramatullah wabarakatuh yan'uwa barkanmu da wannan lokaci tare da fata kowa ya tashi lafy Allah yasa haka Ameen , bayan haka insha Allah yauma kamar kullm ne zamu dora inda muka tsaya.
,
shehu yaci gaba da cewa
ﺃﻣﺎ ﺑﻌﺪ :
Bayan haka
ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﺑﻬﺬﺍ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﺍﻟﺴﻨﻮﻱ ﻷﻫﻞ ﻣﺤﺒﺔ ﺳﻴﺪ ﺍﻷﻭﻟﻴﻦ ﻭﺍﻵﺧﺮﻳﻦ ﻭﺧﺎﺗﻢ ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ ﻭﺇﻣﺎﻡ ﺍﻟﻤﺮﺳﻠﻴﻦ ،
Haƙiƙa Allah madaukakan sarki a wannan idi na maulud na wannan shekara ga ma'abota soyayyar shugaban farko da ƙarshe cikamakin Annabawa kuma shugaban manzanni {S,A,W}
ﺃﻭﺟﺪ ﻟﻨﺎ ﻣﺆﺗﻤﺮﺍً ﻳﺠﻤﻌﻨﺎ ﻣﻊ ﺃﺣﺒﺎﺑﻨﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺸﺮﻕ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻤﻐﺮﺏ ﻭﻣﻦ ﺍﻟﺸﻤﺎﻝ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺠﻨﻮﺏ .
Ya samar mana da wani taro daya haɗamu tare da masoyanmu daga gabas zuwa yamma daga arewa zuwa kudu
ﺑﻞ ﻭﻣﻦ ﺍﻷﺭﺽ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﻭﺍﻹﻧﺲ ﻭﺍﻟﺠﻦ ﻭﺍﻟﺤﻴﻮﺍﻥ ﺍﻟﺠﻤﺎﺩﺍﺕ ﻓﺮﺣﺎً ﺑﺎﻟﺤﺒﻴﺐ ﺍﻟﻤﻘﺮﺏ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎً ﻭﺇﺟﻼﻻً ﻟﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ .
Shehu yace ) bari wannan zancen ma har masoyan mu na ƙasa zuwa sama da mutane da aljannu da dabbobi da sandararrun abubuwa
Duk ya haɗa mu dasu cikin nuna farin ciki da samuwar masoyin nan makusancin Allah, ya kuma haɗa mu don girmama wa da kuma manyatawa gareshi {S,A,W}
ﻭﻣﻦ ﺃﺟﻞ ﺍﻟﻤﺤﺒﺔ ﻭﺍﻟﺘّﻘﺮﺏ ﻓﺄﺭﻯ ﺃﻧﻪ ﻟﻤﻦ ﺍﻟﻮﺍﺟﺐ ﺍﻟﻤﺆﻛﺪ ﻋﻠﻲ ﺃﻥ ﺃﺿﻊ ﻟﻜﻢ ﻣﺎ ﻻ ﺑﺪ ﻣﻨﻪ ﻟﻜﻢ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﺴﻠﻮﻙ ﻭﺍﻟﺘﺮﺑﻴﺔ .
To sabida lamarin soyayya yanda yake da kuma kusanci (ku masoya na ne kuma makusanta na ne ) sai naga yana daga abu na wajibi da tilas na in aje muku wani (bayani) da ba makawa kan samunsa gareku a cikin hanyar suluki da kuma tarbiyya
,
ALHAMDULILLAH
Ibrahim salisu minna