![Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta bukaci mahukuntan Najeriya da su gudanar da kwakwaran bincike...](https://img3.medioq.com/830/075/610417478300759.jpg)
24/01/2025
Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta bukaci mahukuntan Najeriya da su gudanar da kwakwaran bincike a game da barazanar da ake yi wa rayuwar Hamdiyya Sidi Shariff da lauyanta Abba Hikima.
Amnesty ta ce ana ci gaba da kiransu ta waya da ma tsare su a hanya ana yi wa rayuwarsu barazana.
Isa Sanusi da ke zama babban darakatan kungiyar a Najeriya ya ce maimakon amfani da karfi wajen dakile fadin albarkacin baki, mahukunta su magance matsalar tsaro da ta addabi al'umma.