Zauren Tunatarwa Gameda Musulunchi.

  • Home
  • Zauren Tunatarwa Gameda Musulunchi.

Zauren Tunatarwa Gameda Musulunchi. MuslimMedia mobilizer

30/09/2023
03/09/2023
07/06/2023

Imam Shafi'i Yana Cewa:

"Kamar Yadda Bakasan Komai Ga me da kowa ba,
Ka da ka Yarda kowa Yasan Komai A Ga me Da kai."

07/06/2023
02/06/2023
Muna Yiwa Malaminmu Al,Sheikh Abdullahi Zakariyya Misau,Sautussunnah Addu,a Allah Yasa Suyi Karbebbiya.
02/06/2023

Muna Yiwa Malaminmu Al,Sheikh Abdullahi Zakariyya Misau,Sautussunnah Addu,a Allah Yasa Suyi Karbebbiya.

01/06/2023

Manzon allah (s a w)yace kuyawaita yimin salati ranar juma'a,

Ya kai dan uwa karka shagala.

01/06/2023

Allah yakawowa talaka dauki yashiga cikin lamarin...

29/04/2021

ABUBUWA 3 SUNA KAUDA FUSHIN ALLAH AKAN BAWANSA:

1- Istigfari
2- Tausayawa waninka
3- Sadaka

ABUBUWA UKU SUNA HANA MUTUM TANADIN LAHIRA:

1- Dogon Buri
2- Rashin karanta Alkur'ani
3- Nisantar sauraron Wa'azi

ZAKA FUSKANCI MATSALA A KABARINKA IDAN KA MUTU DA ABU 3:

1- Hakkin Wani
2- Dabi'ar Annamimanci
3- Hassada

MUTUM3 KADA KA YARDA SU DINGA KUSANTARKA:

1- Munafiki
2- Mazinaci
3- Maras kunya

KA YI KOKARI KA GINA RAYUWARKA AKAN ABU 3:

1- Son Allah da Manzonsa.
2- Gaskiya da Rikon Amana
3- Hakuri da Jarrabawa a Rayuwa

IDAN ALLAH YA BAKA ABU 3 TO KA GODEWA ALLAH:

1- Lafiya
2- Wadata
3- Basira

ABUBUWA 3 KA ROKI ALLAH (S.W.T) YA TSARE KA DA AIKATA SU:

1- Yanke Zumunta.
2- Zagin Sahabbai.
3- Mutuwa da hakkin wani

ABUBUWA3 BA A SON JINKIRTA SU IDAN LOKACIN SU YA ZO:

1- Sallah
2- Aure
3- Jana'iza

MUTANE 3 KADA KA SAURARI MAGANARSU:

1- Makaryaci
2- Magulmaci
3- Malami mai kwadayi da son zuciya

KADA KA YARDA KA AURI MACE MAI DABI'O'I GUDA 3:

1- Mai yawan fushi
2- Maras sirri
3- Marar tsafta (Kazamiya)

22/04/2021

GAME DA SUJJADAR TILAWA

Shaykh ibnu Baaz (Rahimahullah) ya ce; "Zance mafi inganci daga cikin zantukan malamai game da sujjadar tilawa shine ba'a mata sallama, kuma ba'a mata kabbara yayin dagowa, sai dai an shar'anta ayi mata kabbara lokacin yin sujjadar, amma idan ya kasance sujjadar za'a yi tane acikin sallah to yana wajaba ayi mata kabbara yayin tafiya da dagowa".

مجموع الفتاوى ١١-٤٠٦

Note:
Ana fadin abunda ake fadane acikin sujjadar sallah,

Sannan Ana iya fadin
سجد وجهي للذي خلقه وشق سمعه وبصره بحوله وقوته



Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah

21/04/2021

GAGGAUTA BUƊA BAKI 💧

Manzon (SAW) ya ce:
Mutane ba zasu gushe suna cikin alkhairi ba matuƙar suna gaggauta buda baki.
-Bukhari

Shaykh Saleeh Al-Fauzan yake cewa, An so gaggauta buɗa baki lokacin da aka tabbatar da faɗuwar rana ta hanyar gani ko kuma ya yi galaba a wajen sa cewa rana ta faɗi ta hanyar jin labari daga amintacce Imma da kiran sallah ko wanin sa.




Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah

16/04/2021

ABUBUWA GUDA 20 DA BASU KARYA AZUMI

*1-Kwana da janaba a jiki.Annabi ya kan wayi gari da janaba kuma yana mai azumi*

*2-Kurkure ‘baki da shaqa ruwa da yin aswaki*

*3-Sanya tozali da rana*
Bari

*4-Sanya maganin ciwon ido*

*5-Sanya maganin ciwon kunne*

*6-Fitar maniyyi ta mafarki da rana*


*7-Yin qaho*


*8-Rungumar mace da sumbatarta in ba ka da kaifin sha’awa*

*9-Zuba ruwa mai sanyi a fuska ko a kai*

*10-Dandana abinci amma a tofar bayan dandanawar*

*11-Amai ba da gangan ba.*

*12-Maganin da masu cutar ‘ASMA’ ke anfani da shi wato ( Inhaler ) lokacin azumi ba ya karya azumi*

*13*Shaqa maganin mura*

*14-Dibar jini a jikin mai azumi ba ya karya azumi*
-siyam, Uthaymin

*15-Cin abinci da mantuwa.[Allah ne ya ciyar da kai babu komi azuminka na nan]*

*16-Yin asuwaki ko makilin da burushi*
Ramadana na Jamil Zainu

*17-Yin wanka a rafi*

*18-Zuba ruwa a kai domin jin sanyi*

*19-Yin allura a jiki da sunan Magani bata karya azumi*

*20-Cire haqori ko cikesa ba ya karya azumi*
70 Questions on Fasting

Idan mace tana da ciki sai ta ga jini ya zubo mata a gabanta,babu komai domin wannan ba jinin haila ba ne, azuminta yana nan bai lalace ba, ciwo ne ta nemi magani.

Amma da a ce tana haila sai ta ga hailarta ta dauke bayan alfijir ya fito ba zata yi azumi ba.
-siyam, Uthaymin

14/04/2021

ABINDA ZAMUYI A WATAN RAMADAN DAGA MANZON ALLAH (S. A. W)

Annabin Rahama Muhammad (S. A. W) yace 'A cikin wannan watan, ku yawaita ayukka guda hudu; biyu daga cikinsu don neman yardan Allah, biyu kuma domin amfanin k kanku. Aiyuka biyun da za ku yi domin neman yardar Allah su ne, ku yawaita fadin Kalimah Tayyibah watau (LA'ilaha Illallah) kuma ku yawaita yin istighfari, ma'ana ku roki Allah gafara ta hanyar yin istighfari.

Abu biyu kuma da ake so ku yawaita don amfanin kanku sune ku roki Allah ya shigar daku Aljanna kuma ku roke shi da ya kare ku daga azabar Jahannama.

Duk wanda ya ba mai Azumi ruwa ya sha lokacin buda baki, Allah Ta'ala zai shayar da shi ruwa daga wata korama, daga nan ba zai sake jin kishirwa ba har sai ya shiga Aljanna' (Ibn Khuzaimah ya ruwaito shi cikinsahihan Hadisansa).

Muna rokon Allah yasa Aljannar Firdausi itace makomar Mu baki daya. Ameen

Daga Ahmad Musa

14/04/2021

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WANI MUTUM DA YAYI ZINA A JAMI'A AKWAI DARASI MAI AMFANI A CIKIN LABARIN

'Yan uwa na Maza da Mata akwai wata ƙissa da zan bamu, mai matuƙar amfani acikin wannan zamanin namu, ma'abocin ƙissar, wanda abin yafaru dashi, shine yake bayar da Labarin yadda al'amarin ya kansace dashi.

Labarin yana cikin wata Mujallah (Magazine News paper) ta ƙasashen Larabawa, kuma cikin harshen Larabcine, amma zanyi ƙoƙari wajen fassarawa gwargwadon yadda na fahimta, saboda nima din ba gwani bane a harshen Larabci.

Gata k**ar haka:

Mutumin yana cewa:

A lokacin da ina saurayina nasami Admission a Jami'a, bayan nafara karatunne sai na haɗu da wata Budurwa (Girl-friend) acikin Jami'ar tamu muka ƙulla soyayya da ita tamkar ma'aurata, hardai tasami juna biyu, (yai mata ciki kenan).

Da iyayenta s**a gane sai s**a tambayeta wanda yayi mata ciki sai tace nine nayi mata.

Sai yayanta ya taho nema na a fusace yana nufin ɗaukar mataki a kaina, yana zuwa saiya tambayeni kaine kayima ƙanwata ciki ko ???

Sai na amsa masa da cewa:

Wace ce, ni banma taɓa ganinta ba a Rayuwata, ban santa ba.

Sak**akon rashin hujjar da zasu k**ani da ita dole s**a ƙyaleni.

Bayan tsawon zamani, wata rana nadawo gida saina tarar da Mahaifiyata a dur ƙushe tana kuka.

Saina dur ƙusa na ɗaga ta sai tasake yanke jiki tafaɗi ƙasa har sau uku.

Sai na tambayeta a karo na ƙarshe.

"Ya Ummi Man ladzhi haddath (me ya faru mama)?

Sai tace:

Kanwarkace gata can wani yayi mata ciki!

Yace sai naji k**ar an sokeni da mashi, hankalina yatashi na tasa ƙeyarta muka tafi wurin wanda tace yai mata cikin.

Da mukaje sai yafaɗa min maganar data tayarmin da hankali.

Bawata magana bace face wadda na fadama yayan yarinyar da nayi
ma ciki a baya.

(Ban santa ba, ban ma taɓa ganinta ba)!

Bayan zamani yaƙara yin nisa sai nayi nufin yin aure nafara neman aure nasamu matar da nake so kuma akasa lokaci akayi biki, ranar farko dana tare da ita saina sameta ba a matsayin budurwa ba.

Ma'ana tariga tayi zina, tuni hankalina yatashi.

Sai ta faɗamin wata magana mai shiga rai.

"Don Allah karufa min asiri, ka suturta al'amarina kaima Allah sai ya suturta al'amarinka."

Yace sai nace a cikin zuciyata:

Ya Rabby yakfy, yakfy.

(Ma'ana Ya Mahalliccina ya isa haka ya isa haka).
Ya cigaba da cewa:

Bayan mun kwashe shekaru da mata ta sai muka haifi 'ya mace kyakkyawa gata da haske k**ar wata.

A lokacin da tacika shekaru 6 a duniya sai gata wata rana tashigo gida tana kuka.

Me yafaru ?

Ai me gadi ne yayi mata fyaɗe!

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Aljazaa'u min jinsil amal!

Wallahi duk tsiyar da kake sheƙewa idan Allah ta'ala yaga dama sai ya haɗa maka zafi kan zafi irin wannan!

Yanzu kunga shi ya lalata 'yar mutane guda daya tak shi kuma an lalata masa guda uku!

Yaa Allah ka ƙara karemu daga zina, masuyi kuma Allah ka shirya su Amin.

13/04/2021


BAYANI AKAN AZUMI
KARANTA ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI

1. Ridda, wato fita daga Musulunci.

2. Ci ko sha da gangan ba tare da uzuri ba.

3. Haila ko Nifasi, sai dai a kirga kwanakin da aka sha a rama su bayan Ramadan.

4. Jima'i, Tarawa da mutum ko dabba ko ma da me ne ne.

5. Fitar maniyyi dan sha'awa ko da jima'i ko babu.

6. Kakaro amai da gangan.

7. Hauka.

Da sauransu.

Idan namiji da mace s**a sadu da rana a cikin watan Azumi to, azuminsu ya baci, sai su rama kuma su yi kaffara.

Don fadin Abu Huraira (R.A) ya ce, wata rana Manzon Allah (S.A.W) yana zaune sai wani mutum ya zo ya ce, ya Rasulullahi, na halaka, sai Annabi ya ce da shi, mai ya halaka ka? Sai ya ce, na sadu da matata a cikin watan Azumi da rana, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da shi, za ka sami abin da za ka ’yanta bawa? Sai ya ce, a’a, sai ya ce, za ka iya yin Azumi watanni biyu a jere? Sai ya ce, a’a, sai ya ce, shin za ka sami abin da za ka ciyar da miskinai sittin? Sai ya ce, a’a, sai mutumin ya zauna a wajen Annabi har aka kawo wa Annabi buhun dabino.

Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da shi, dauki ka yi sadaka da shi, sai ya ce, ai duk cikin Madina babu wanda ya fi ne bukata.

Sai Manzon Allah (S.A.W) ya yi dariya har sai da hakoransa s**a bayyana. Sannan ya ce, dauki ka je ka ciyar da iyalanka.” (Jama’a da yawa ne s**a rawaito).

09/04/2021

KARANTA SUNNONI GUDA 11 A RANAR JUMA'A DA AKA MANTA DA SU

1. Yin wankan juma'a da sanya turare mai dadin kamshi a ranar juma'a.

Wanda yayi wanka juma'a a ranar juma'a sannan ya sanya Turare ya shafa mai sannan ya taho masallacin juma'a, kuma bai ketara tsakanin mutane biyu sannan ya yi shiru lokacin da liman yake Huduba, an gafarta masa zunubansa tsakanin juma'a zuwa wata juma'ar.

ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ 883

2. Yin shiru lokacin Huɗuba da kuma k**a daga ƙetara mutane idan kazo masallacin juma'a.

Kuma bai ƙetara tsakanin mutane biyu sannan ya yi shiru lokacin da liman yake Huɗuba, an gafarta masa zunubansa tsakanin juma'a zuwa wata juma'ar.

ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ 888

3. Fita zuwa masallacin juma'a da wuri k**ar daga karfe 11:00 ko 10:30am.

Malamai suna cewa "Sammakon ranar Juma'a yana farawa daga fitowa rana zuwa sa'a ta biyar lokacin zaman liman akan Minbari."

Manzon Allah (S.A.W)

Wanda yazo a sa'ar farko yana da ladar wanda ya yi sadaka da rami,a sa'a ta biyu k**ar mai sadaka da saniya,sa'a ta uku k**ar sadakar rago, sa'a ta huɗu k**ar sadaka da kaza, sa'a ta biyar k**ar mai sadaka da kwai, idan liman ya hau mimbari sai a daina ruwatawa.

ﻣﺴﻠﻢ ‏1403

4. Yin barci rana bayan sallar juma'a.

Sahal bin Saad ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ yana cewa" Mu sahabban Manzon Allah (S.A.W) mun kasance muna kwanciya barcin rana a ranar juma'a bayan mun dawo daga sallar juma'a."

ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 5807 )

Yayin Huɗuba

Wannan ya nuna kenan suna yin sallar juma'ar ne da wuri kuma suna fita masallacin juma'a ne da wuri.

5. Mai Huɗuba zai yi nuni da ɗan yatsarsa manuniya a lokacin da yake addu'a acikin Huɗuba.

Manzon Allah (S.A.W) baya karawa akan yin nuni da ɗan yatsarsa a lokacin da yake yin addu'a a cikin Huɗuba.

ﻣﺴﻠﻢ ‏( 874 ‏) ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏( 515 ‏) ﺍﺣﻤﺪ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ ‏( 17219/17221 / 17224/18299 )

Kwalliya ta Musamman Domin Ranar Juma'a

6. Baya cikin SUNNAH ɗaga hannu a lokacin yin addu'a a cikin Huɗuba ga liman ko mamu.

ﺍﻟﻌﻼﻣﺔ ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴﻤﻴﻦ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ

Yana cewa "Ɗaga hannu dan yin addu'a lokacin da liman yake Huɗuba baya cikin SUNNAH".

ﻓﺘﺎﻭﻱ ﺃﺭﻛﺎﻥ ﺍﻹﺳﻼﻡ ‏( ﺹ 393 )

7. Fuskantar liman da kallonsa lokacin da yake Huɗuba.

ﺍﻟﻌﻼﻣﺔ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ

Yana cewa "Fuskantar liman da kallon sa lokacin da yake Huɗuba yana cikin SUNNAR da aka manta da ita".

ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ 5/110

8. Canza wajan zama ko canza yayin zama ga wanda yake gyangyadi a ranar juma'a.

Manzon Allah (S.A.W) yana cewa "Idan ɗayan ku yana gyangyaɗi a ranar juma'a to ya chanza wajan zaman sa".

ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ‏( 1119 ‏) ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏( 526 ‏) ﺍﺑﻦ ﺧﺰﻳﻤﺔ‏( 1819 )

Hikima akan haka shine motsin da zaka yi na canza zama ko gurin zama zai yanke maka gyangyadi dan ka saurari Huɗuba da addu'ar liman lokacin Huɗuba.

9. Yin sallar nafila bayan juma'a.

Sunnane ga wanda ya halarci sallar juma'a yayi nafila raka'a biyu bayan ya koma gida ko raka'a huɗu a masallaci.

ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 937 ‏) ﻣﺴﻠﻢ ‏( 882 )

ﺍﻟﻌﻼﻣﺔ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ

Yana cewa: Malamin mu ibn Taimiya yana cewa"Wanda zai yi nafila bayan sallar juma'a idan masallacin zai yi sai yayi raka'a huɗu, idan kuma sai ya koma gida ne sai yayi raka'a biyu kaɗai, wannan shi ne abin da ya tabbata a SUNNAH.

ﺍﻟﺰﺍﺩ ‏( 1/440 )

10. Yawaita salati ga Manzon Allah SAW a daren Juma'a da yinin juma'a.

ﻣﺴﻠﻢ ‏( 881 )

11. Yawaita addu'a bayan sallar la'asar ta ranar Juma'a zuwa faɗuwar rana dan dacewa da lokacin amsa addu'a ranar Juma'a.

ﺍﻟﺰﺍﺩ ‏( 1/440 )

Karanta Suratul Kahf Ranar Juma'a

A DUK RANAR JUMA'A

Kada muyi ƙasa a gwuiwa wajen yawaita yin Salati ga Manzon Allah (S.A.W)) da Iyalan gidan sa, domin yin Salati ga Manzon Allah(S.A.W.W) da Iyalan gidansa (as) yana nufin:

1. Amsa umarni ne na Allah maɗaukakin Sarki.

2. Samar da haske ne ga kabarin mai yinsa bayan ya mutu.

3. Zikiri ne mafi girma da ɗaukaka.

4. Sinadari ne na rusa zunubai da share lefuka.

5. Ɗaukaka ce ga mai yawaita yin sa.

6. Samun kusanci ne zuwa ga Allah.

7. Bayyanar da Soyayya ne ga Manzon Allah da Iyalan gidansa (A.S).

8. Yinsa a farkon kowanne aikin lada, sirri ne na karɓuwar wannan aikin.

9. Tsarki ne ga ruhi da gangar jikin mai yinsa.

10. Ibada ce karɓabbiya wacce ba a maidowa da wanda yayi.

Yiwa Annabi da Iyalan gidansa Salati, sirrin haske ne a Duniya da lahira, dawwama a cikin hakan kuwa yana nufi dawwama ne a cikin lada da samun yardar Allah (S.W.T)

"اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّد وَآل مُحَمَّد".

Allah ne mafi sani.

Allah ka bamu ikon koyi da Manzon Allah (S.A.W) a cikin dukkan ibadar mu da rayuwar Mu baki ɗaya Amin.

Insha Allahu rubutu nagaba akan MANYAN LADUBBA AKAN MUSULMI GUDA 10 A RANAR JUMA'A

Marubuci: Bashir M. Sulaiman

08/04/2021

Abinda Yake Faruwa Dakai A Lokacin Daka Kwanta Bacci Da Music Batare Daka Sani Ba

Babu wanda zai baka mamaki da tausayi fiye da wanda kafin yayi barci sai ya kunna kiɗa.

GAYU, A DAINA YIN BARCI DA KIƊA KO WAƘA

Barci yana kusanto da bawa ga mutuwa ne. In banda abinka gaye, mene ne amfanin gayyato sheɗanu a lokacin da kake kusantar mutuwa?

Cikin Suratul Zumar, Allah (S.W.T) yace:

اللَّهُ يَتَوَفَّى الْأَنفُسَ حِينَ مَوْتِهَا وَالَّتِي لَمْ تَمُتْ فِي مَنَامِهَا فَيُمْسِكُ الَّتِي قَضَى عَلَيْهَا الْمَوْتَ وَيُرْسِلُ الْأُخْرَى إِلَى أَجَلٍ مُّسَمًّى إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ

“Allah ne wanda ke karɓan rayuka a lokacin mutuwar su, da waɗanda basu mutu ba a cikin barcin su. Sai ya riƙe wanda ya hukunta mutuwa akan sa, kuma ya saki ɗayan zuwa ga ajali ambatacce. Lallai a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu hankali."

Malaman Tafsiri a nan s**a ce Allah ya kan zare ran ɗan Adam a lokacin da yake barci. Sai dai zarewar ba zarewa bane na gaba ɗaya k**ar yadda ake yi lokacin mutuwa. Zarewa ne wanda yake za'a bar wani ɓangare na rai ɗin yana ittiṣali da jikin mutum ittiṣali wanda yake ba sosai ba. Domin haka ne mutum za ka ga yana barci yana numfashi, amman kuma fa a lokacin shi bai san halin da yake ciki ba. Don haka idan Allah ya ƙaddarawa mutum mutuwa a cikin wannan barcin, kawai sai dai a dakatar da numfashin. Shikenan labari ya canza. Mutum ya bar duniyar nan. Ɗan Adam ba a bakin komai yake ba!

Sahabi Abu Juhaifah (RA) yace wata rana Annabi (S.A.W) yana cikin wata tafiya haka wacce s**ayi barci har rana ta fito. Sai Annabi (S.A.W) yace:

إِنَّكُمْ كُنْتُمْ أَمْوَاتًا فَرَدَّ اللَّهُ إِلَيْكُمْ أَرْوَاحَكُمْ ، فَمَنْ نَامَ عَنْ صَلاةٍ فَلْيُصَلِّهَا إِذَا اسْتَيْقَظَ ، وَمَنْ نَسِيَ صَلاةً فَلْيُصَلِّ إِذَا ذَكَرَ

"Tabbas kun kasance matattu, sai Allah ya dawo muku da rayukan ku. Don haka duk wanda ya san sallah ta kuɓuce masa saboda barci, to sai ya sallace ta idan ya farka. Wanda kuma ta kuɓuce masa saboda mantuwa, to ya sallace ta idan ya tuna".

Ingantaccen hadisine wanda Abu-Ya'ala ya ruwaito cikin Al-Musnad.

Waɗannan duk suna nuna cewa rai ya kan fita a lokacin da muka kwanta barci. Idan ajalin mu bai riga yayi ba, sai Allah ya dawo mana da ran. Idan kuwa ajali yayi, shi kenan sai shirye-shiryen jana'iza kuma.

Amman duk da haka shi gaye babu ruwan shi. Madadin ya kwanta yana mai kusantar Ubangijin sa da addu'o'i da zikirai da tadabburin ayoyin Qur'ani waɗanda zasu tausasa mishi zuciya, a'a sai ka ga yana gayyato sheɗanu ta hanyar kunna music da sauran waƙe-waƙe da raye-raye da sauran iskanci iri-iri.

Barci da music muguwar ɗabi'a ce ga duk mutumin da yake taka tsan-tsan da duniyar nan, yake da yaƙinin a kowani lokaci za ta iya kuɓuce mishi. Yana da kyau abokan mu gayu su gyara wannan ɗabi'a.

Marubuci:- Ibrahiym A. El-Caleel

07/04/2021

Shin Ko Kasan Abinda Zai Faru Da Wanda Yake Cin Bashi Amma Baya Biya?

Wasu mutanen sun mayar da cinye bashin da s**a karɓa na kuɗi ko mak**ancinsa hanyar biyan buƙatunsu na rayuwa ta yadda in hulɗar kuɗi ta haɗa ka da su sai dai ka yi haƙuri ko ka nuna babu mutumci, in s**a karɓi aron kuɗi ko wani abu a madadinsa ba za su biya ba, ban da rashin tausayi ba su biya abin da ake bin su a baya ba sai su zo da sunan a ƙara musu wani bashin za su haɗa su biya, kai jama'a!

Wasu kuwa ba sa jin tsoron cinye ƙananan kuɗaɗen da aka biyo su ta hanyar siyayyar da s**a yi ko siyayyar da aka yi a wajensu, in aka biyo su wani kuɗi sai a amince musu da sunan za su bayar saboda mutumcinsu da ake gani, ashe ba haka abin yake ba sai su yi fuska su ƙi biya. Matsalar nan ma ba ta taƙaita ga manya kaɗai ba har zuwa yara; abin ban haushi sai ka jawo yara jikinka da sunan koya musu sana'a wacce za su riƙa samun kuɗin shiga tun kafin su girma ƙarshe sai su cuce ka.

Wasu manyan cuta a kan kuɗi haka ma wasu yaran, wannan ya sa tsoro ya shiga zuciyar masu abin hannu a kan in s**a ɗora wasu a kan dukiyarsu za su wulaƙanta musu ita, hakan ya sa s**a ƙi ɗorawa gudun kada a banzantar musu da abin da s**a sha wahala wajen tarawa. Amma shawarata ga mutane masu abin hannu su yi haƙuri su nemi nagartattun mutane su ɗora su a kan kasuwancinsu, su koya musu yadda za su dogara da kansu ko su ba su jari.

In ka zama dalilin arzikin wani ba ka san iya ladan da za ka samu ba a wajen Allah, lallai akwai mutanen kirki waɗanda babu ruwansu da abin da ba nasu ba, suna tsayawa tsayin daka wajen kulawa da duk abin da aka ɗora su a kansa, ba su san ha'inci ba, ba su san mugunta ba, ba su san cin amana ba, abinda su sani kaɗai a nan shi ne ba a yi wa mutane jam'i duk lalacewarsu domin kuwa tabbas sai an sami na kirki a cikinsu.

Ka'ida ta ƙarshe; duk wanda ya ci kuɗin da ba nashi ba sai ya biya a ranar da ba shi da abin biya sai kyakkyawan aikinsa, zai kuma riƙa gamuwa da bala'i kala daban-daban a cikin kabarinsa tun kafin a tashe shi ranar biya, wannan ƙa'idar ce za ta tabbatar maka da cewa cin dukiyar mutane ba abin yi ba ne ga musulmi na ƙwarai!

Marubuci: Abbati Mai Shago Flg

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zauren Tunatarwa Gameda Musulunchi. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zauren Tunatarwa Gameda Musulunchi.:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share