03/05/2024
A TAWA FAHIMTAR....
Gwamnati zata iya amfani da BVN din mutanen Nigeria wajen gano wadanda suke transaction din makudan kudade daga Dollar zuwa Naira ko daga Naira zuwa Dollar, mu dai anan Arewacin Najeriya mafi yawan matasan da suke harkokin mining, Airdrop da Farming har ma da Trading zai wahala ka samu mutum daya da yake transaction din Dollar dubu dari, kusan dukkanmu na abunci da bukatu ake nema...
Gwamnati ta mike tsaye wajen toshe kafafoin da ake bi wajen illata tattalin arziki abu ne mai kyau amma ya kamata ayi hakan ba tare da tsorata talakawan da suke kalato Dollar goma ko hamsin da kyar a wajen mining ba...
Matasan nan da suke Mining da Airdrop da Farming suna da yawan da rasa su a siyasance ba zai zama abun alheri ga kowacce Gwamnati ba..
Allah ya saukaka mana...
©Rabiu Biyora✍️