
18/05/2025
Gwamna Zulum ya ziyarci Marte inda zai yi kwanaki Biyu.
Dangane da hare-haren ‘yan tada kayar baya a wasu yankunan Borno da s**a hada da Marte, Damboa, Gajiram, da Chibok.
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci karamar hukumar Marte domin duba halin da ake ciki tare da bayar da tallafi ga al’ummomin da abin ya shafa.
Kafin Marte, Gwamna Zulum ya tsaya a garin Dikwa don ganawa da mazauna Marte da s**a tsere daga harin don neman mafaka.
Ya jajanta wa al’ummar da abin ya shafa tare da ba su tabbacin gwamnatinsa na shirin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Ya kuma bukaci jama’a da su kasance masu taka-tsan-tsan da addu’a a cikin wadannan lokuta na wahala.
Bayan isa garin Marte, Gwamnan ya duba yankunan da ‘yan tada kayar baya s**a kai hari tare da lalata su.
Gwamnan zai kwana biyu a Marte domin ci gaba da tantance halin da ake ciki tare da yin magana da sojoji kai tsaye.
Ziyarar ta Gwamnan za ta hada da tarurrukan dabaru da nufin inganta ayyukan tsaro a yankin.
Gwamna Zulum ya samu rakiyar ‘yan majalisar wakilai guda biyu, Engr. Bukar Talba da Dr Zainab Gimba da kuma shugabannin karamar hukumar Marte na yanzu da na baya da sauran masu ruwa da tsaki.
Hotuna: BORNO community WATCH