TCR Hausa

TCR Hausa Sashen Hausa na Jaridar The Citizen Reports

Dan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen, ya lashe kyautar Gwarzon dan wasan maza na CAF (2023).Ya lashe kambun ne bay...
11/12/2023

Dan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen, ya lashe kyautar Gwarzon dan wasan maza na CAF (2023).

Ya lashe kambun ne bayan fafatawa da gwaraza irin su Achraf Hakimi na Morocco, Sadio Mane na Senegal, da Mohamed Salah na Masar, da sauransu.

Dan wasan mai shekaru 24 lallai ya taka rawar gani a tsakanin takwarorinsa.

Wannan kyauta ta zo ne bayan tsawon shekaru 24 rabon da ɗan Najeriya ya same ta, watau tun lokacin da fitaccen dan wasan Super Eagles, Kanu Nwankwo, ya same ta a shekarar 1999.

El-Rufai ya kai wa Buhari ziyara a DauraTsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya gana da tsohon shugaban Najeriya...
11/12/2023

El-Rufai ya kai wa Buhari ziyara a Daura

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya gana da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a Jihar Katsina.

Malam Garba Shehu, mai taimaka wa Buhari na musamman ne ya wallafa wannan a shafinsa na sada zumunta.

Ɗan wasan ƙasar Portugal da kuma ƙungiyar Alnassr a yau ya ci ƙwallo ta 50 ke nan a wannan shekara ta 2023.Shin kuna gan...
11/12/2023

Ɗan wasan ƙasar Portugal da kuma ƙungiyar Alnassr a yau ya ci ƙwallo ta 50 ke nan a wannan shekara ta 2023.

Shin kuna ganin ya yi ƙoƙari?

Motocin bas-bas ke nan da Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar a birnin Maiduguri na Jihar Borno a yau Litinin
11/12/2023

Motocin bas-bas ke nan da Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar a birnin Maiduguri na Jihar Borno a yau Litinin

Zlatan Ibrahimovic ya koma AC Milan a matsayin mai ba da shawara a ɓangaren gudanarwar kungiyar ta Serie A, k**ar yadda ...
11/12/2023

Zlatan Ibrahimovic ya koma AC Milan a matsayin mai ba da shawara a ɓangaren gudanarwar kungiyar ta Serie A, k**ar yadda masu RedBird Capital Partners s**a tabbatar a ranar Litinin.

Ɗaliban jami’a a Nasarawa sun shaƙi iskar ƴanci bayan shafe kwanaki a hannun ƴan bindigaƘarin bayani: https://shorturl.a...
11/12/2023

Ɗaliban jami’a a Nasarawa sun shaƙi iskar ƴanci bayan shafe kwanaki a hannun ƴan bindiga

Ƙarin bayani: https://shorturl.at/jmqTZ

Girona ta koma teburin Laliga bayan ta ragargaji Barcelona 4-2.
10/12/2023

Girona ta koma teburin Laliga bayan ta ragargaji Barcelona 4-2.

Manchester City ta sha da ƙyar a hannun Luton Town a gasar Firimiya
10/12/2023

Manchester City ta sha da ƙyar a hannun Luton Town a gasar Firimiya

Chelsea ta kashi a hannun Everton⚽
10/12/2023

Chelsea ta kashi a hannun Everton⚽

Mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 16 a hanyar Kaduna zuwa AbujaƘarin bayani: https://shorturl.at/yFM...
10/12/2023

Mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 16 a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Ƙarin bayani: https://shorturl.at/yFMTW

Sanatocin Najeriya sun sadaukar da albashinsu na Disamba wa waɗanda harin bam ya rutsa da su a KadunaƘarin bayani: https...
10/12/2023

Sanatocin Najeriya sun sadaukar da albashinsu na Disamba wa waɗanda harin bam ya rutsa da su a Kaduna

Ƙarin bayani: https://shorturl.at/nEGY6

Ƴan sanda sun k**a magidancin da ya yi yunƙurin kashe matarsa a BauchiƘarin bayani: https://shorturl.at/FHO36
10/12/2023

Ƴan sanda sun k**a magidancin da ya yi yunƙurin kashe matarsa a Bauchi

Ƙarin bayani: https://shorturl.at/FHO36

Aston Villa ta ba wa Arsenal mamaki bayan ta yi mata ci ɗaya mai ban haushi a wasan mako na 16 a Firimiya Lik.Wannan ya ...
09/12/2023

Aston Villa ta ba wa Arsenal mamaki bayan ta yi mata ci ɗaya mai ban haushi a wasan mako na 16 a Firimiya Lik.

Wannan ya sa Liverpool ta hau kan teburin Firimiya daram da maki 37, inda ta ba wa Arsenal tazarar maki ɗaya, wacce ita ce ta biyu a teburin.

Abba da Gawuna: Malamai sun yi kira ga Kotun Ƙoli da ta yi adalci a shari’ar zaɓen gwamnaƘarin bayani: https://shorturl....
09/12/2023

Abba da Gawuna: Malamai sun yi kira ga Kotun Ƙoli da ta yi adalci a shari’ar zaɓen gwamna

Ƙarin bayani: https://shorturl.at/oFJ46

Ga waɗanda s**a san wainar da ake toyawa a harkar ƙwallon ƙafa, wannan sak**akon yana iya zama ɗaya daga cikin abubuwa m...
09/12/2023

Ga waɗanda s**a san wainar da ake toyawa a harkar ƙwallon ƙafa, wannan sak**akon yana iya zama ɗaya daga cikin abubuwa mafiya mamaki da s**a taɓa faruwa a ƙwallon ƙafa.

Frankfurt: 5 ⚽⚽⚽⚽⚽

Bayern Munich: 1 ⚽

Manchester United ta sha kashi a hannun Bournemouth.Ga shi kuma ba a jima da ba wa Erik Ten Hag kyautar gwarzon kocin wa...
09/12/2023

Manchester United ta sha kashi a hannun Bournemouth.

Ga shi kuma ba a jima da ba wa Erik Ten Hag kyautar gwarzon kocin watan Nuwamba na Firimiya Lik ba.

An k**a ƴan sandan Najeriya da s**a roƙi kuɗi a wajen wata mai yawon buɗe ido ƴar NetherlandsƘarin bayani: https://short...
09/12/2023

An k**a ƴan sandan Najeriya da s**a roƙi kuɗi a wajen wata mai yawon buɗe ido ƴar Netherlands

Ƙarin bayani: https://shorturl.at/tvAGY

Wata cutar ciwon ciki da zawayi ta k**a sojojin Isra’ila da ke yaƙi a FalasɗinuƘarin bayani: https://shorturl.at/gjqv7
09/12/2023

Wata cutar ciwon ciki da zawayi ta k**a sojojin Isra’ila da ke yaƙi a Falasɗinu

Ƙarin bayani: https://shorturl.at/gjqv7

Yadda rayuwar Nicholas Jackson, Ɗan Wasan Senegal da Chelsea ta sauya a cikin shekaru bakwai?Shin kun yarda da sahihanci...
09/12/2023

Yadda rayuwar Nicholas Jackson, Ɗan Wasan Senegal da Chelsea ta sauya a cikin shekaru bakwai?

Shin kun yarda da sahihancin wannan hoton da yake a shafukan yanar gizo?

TCR Hausa ta yi ƙoƙarin tantance gaskiyar wannan hoto, sai dai ba mu samu bayani game da zaƙaƙurin ɗan wasan gaban da ya shafi shekarar 2016 ba. Amma dai a shekarar 2017 yana buga wasa a wani kulob ɗin ciki gida na Senegal mai suna Tilene, daga bisani kuma Cassa Sport duk a cikin ƙasar, kafin daga bisani ya tsallaka Turai zuwa Villarreal B ta ƙasar Sifaniya a shekarar 2019.

Tun daga lokacin da Jaridarmu TCR Hausa  ta fara wallafa labarai kai haƙiƙanin abinda yake faruwa a Falasɗinu, daga nan ...
09/12/2023

Tun daga lokacin da Jaridarmu TCR Hausa ta fara wallafa labarai kai haƙiƙanin abinda yake faruwa a Falasɗinu, daga nan Facebook su ka tura cewa Jaridar ta shiga kurkukunsu saboda wallafa abubuwan da s**a saɓa da ƙa'dojinsu.

Kuma tun daga nan, idan jaridar ta wallafa wani abu, mutane 'yan kaɗan ne suke iya gani.

A baya duk post yana samun reach na aƙalla mutum 5000 a ranar da aka yi shi, yana haurawa nunkin baninki. Amma yanzu da ƙyar mutum 100 suke ganin wasu post ɗin.

TCR Hausa dai shashen Hausa ne na jaridar The Citizen Reports

UWAR BARI: Majalisar Denmark ta saka hannu kan dokar hana wulaƙanta Al Ƙur’ani a bainar jama’aƘarin bayani: https://shor...
09/12/2023

UWAR BARI: Majalisar Denmark ta saka hannu kan dokar hana wulaƙanta Al Ƙur’ani a bainar jama’a

Ƙarin bayani: https://shorturl.at/fpqLO

Gwamantin Najeriya za ta fara ba da tallafin N50,000 ga ƙananan ƴan kasuwa—shiga domin ganin yadda za ka cikaƘarin bayan...
09/12/2023

Gwamantin Najeriya za ta fara ba da tallafin N50,000 ga ƙananan ƴan kasuwa—shiga domin ganin yadda za ka cika

Ƙarin bayani: https://shorturl.at/aEKOV

Harry Maguire ya zama gwarzo gasar Firimiya Lik na watan Nuwambar 2023.Me za ku ce game da wannan kyauta da ɗan wasan na...
08/12/2023

Harry Maguire ya zama gwarzo gasar Firimiya Lik na watan Nuwambar 2023.

Me za ku ce game da wannan kyauta da ɗan wasan na Manchester United ya samu?

Wane kirari ka sani Hausawa suna yi wa kuɗi?
08/12/2023

Wane kirari ka sani Hausawa suna yi wa kuɗi?

CBN ya yi gargadi wa jama’a saboda yadda jabun takardun naira s**a yawaitaƘarin bayani: https://shorturl.at/AMPTY
08/12/2023

CBN ya yi gargadi wa jama’a saboda yadda jabun takardun naira s**a yawaita

Ƙarin bayani: https://shorturl.at/AMPTY

Rukunnan kungiyoyin da za su kara a gasar Copa America.Su waye kake ganin za su haɗu a fainal?
08/12/2023

Rukunnan kungiyoyin da za su kara a gasar Copa America.

Su waye kake ganin za su haɗu a fainal?

08/12/2023

Ƴan bindiga sun shigo garin Zaria

Rahotannin da suke shigo mana na nuna cewa cikin daren Alhamis 'yan bindiga sun shiga sun yi harbe-harbe da yunƙurin satar jama'a a unguwar Sarki, Tankarau, da ke Dutsen Abba, Zaria.

Labaran da muka samu sun tabbatar da cewa maharan suna da dama, duk da cewa babu cikakken adadinsa ya zuwa wannan lokaci.

Gefe-gefen Zaria ya sha fuskantanr hare-haren 'yan ta'addan daji duk da cewa gwamnati ta sha alƙawarta wa jama'a cewa ana neman mafita ga matsalar tsaron wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a faɗin Arewacin Nigeria.

Amurka za ta taimaka wa sojin Najeriya wajen rage kai hare-hare bisa kuskureƘarin bayani: https://shorturl.at/BHPQ0
07/12/2023

Amurka za ta taimaka wa sojin Najeriya wajen rage kai hare-hare bisa kuskure

Ƙarin bayani: https://shorturl.at/BHPQ0

Wata hukumar hana shan ƙwaya ta kammala bincike a kan dan wasan Faransa Paul Pogba. Ta kuma buƙaci a hana ɗan wasan shig...
07/12/2023

Wata hukumar hana shan ƙwaya ta kammala bincike a kan dan wasan Faransa Paul Pogba.

Ta kuma buƙaci a hana ɗan wasan shiga harƙoƙin ƙwallon ƙafa na tsawon shekaru 4.

Me za ku ce a kan wannan mataki da ake kokarin ɗauka?

A matsayinka na masoyi kuma mai goyon bayan Real Madrid, me kake ji a zuciyarka idan ka ga wannan hoton?
07/12/2023

A matsayinka na masoyi kuma mai goyon bayan Real Madrid, me kake ji a zuciyarka idan ka ga wannan hoton?

Shin United sa'a s**a yi s**a lallasa Chelsea ko kuma zunzurutun iyawa ne?
07/12/2023

Shin United sa'a s**a yi s**a lallasa Chelsea ko kuma zunzurutun iyawa ne?

Shawara zuwa ga ƴan ArewaDaga Malam Aliyu Yakubu YusufKuna so duniya ta san matsalolin da kuke ciki a Arewacin Nijeriya?...
06/12/2023

Shawara zuwa ga ƴan Arewa

Daga Malam Aliyu Yakubu Yusuf

Kuna so duniya ta san matsalolin da kuke ciki a Arewacin Nijeriya? Kuna so ƙorafe-ƙorafenku su je inda kuke so cikin sauƙi? Kuna so shugabanni su fara ɗaukarku da muhimmanci?

To ku tafi manhajar X (wato Twitter) ku buɗe accounts sannan ku dinga posting da harshen Turanci. In ko ba haka ba, to za ku yi ta rubutu ne wanda nisan tafiyar sa ba zai wuce iya Arewa cyberspace ba.

Address

No 30/31 Gadangami Complex. Kabuga
Maiduguri

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TCR Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to TCR Hausa:

Videos

Share

Nearby media companies


Other Media/News Companies in Maiduguri

Show All