Labarun Hausa

Labarun Hausa Dan Allah Kuyi Mana Invite Din Members
(6)

Yan daba sun farmaki shugaban jam’iyyar APC a jihar Ebonyi inda s**a cinnawa gidansa wuta.Stanley Okoro-Emegha ya zargi ...
27/12/2022

Yan daba sun farmaki shugaban jam’iyyar APC a jihar Ebonyi inda s**a cinnawa gidansa wuta.

Stanley Okoro-Emegha ya zargi yan bangar siyasan tsohon ciyaman na karamar hukumar Afikpi ta kudu, Eni Chima, da kai masa harin.

Sake fasalin naira da Babban Bankin Najeriya ya yi ya ja hankalin Bankin Duniya wato World Bank.
27/12/2022

Sake fasalin naira da Babban Bankin Najeriya ya yi ya ja hankalin Bankin Duniya wato World Bank.

Tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame ya ce zamansa a gidan yari ya say a fahimci akwai tsarin shari’a biyu a Najeriy...
27/12/2022

Tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame ya ce zamansa a gidan yari ya say a fahimci akwai tsarin shari’a biyu a Najeriya.

Nyame ya ce tsari daya na aiki ne a kan masu matsayi sannan dayan yana aiki ne a kan mutane marasa galihu.

Darajar Naira ta yi faɗuwa mafi muni bayan sanar da shirin sauya fasalin kudin NijeriyaFarashin takardar kudi ta dalar A...
01/11/2022

Darajar Naira ta yi faɗuwa mafi muni bayan sanar da shirin sauya fasalin kudin Nijeriya

Farashin takardar kudi ta dalar Amurka a Najeriya ya kai kololuwa a kasuwannin musayar kudaden ketare a Najeriya, inda a safiyar yau talata aka rika sauya duk dala daya kan naira 815 zuwa 818, lamarin da ke nuna yadda kudin na Naira ke ci gaba da rasa daraja.

RFi ta rawaito cewa wani bincike ya nuna cewa tun bayan yunkurin babban bankin kasar CBN na sauya fasalin wasu daga cikin takardar kudin Najeriyar ne, aka fara ganin rububin sayen takardar kudin ta dala a kasuwanni, wanda bayanai ke cewa mutanen da ke makare da kudi a ajje suke saurin sayen dalar don kaucewa fuskantar asara.

Kasuwannin musaya na bayan fage dai a yau talata sun wayi gari da karancin dala baki daya lamarin da ya sa rashin daidaituwar farashin kudin na Amurka, dai dai lokacin da sabbin kudin Najeriyar ke shirin fitowa a ranar 15 ga watan Disamba mai zuwa.

A makon jiya ne CBN ya sanar da sake faduwar darajar Naira zuwa 765 kan duk dala guda wanda ke nuna faduwar naira 53 cikin kwanaki 5 mafi kololuwar koma baya da Najeriya ta taba gani a tarihi.

Sabon farashin dalar na CBN ya sanya hauhawar farashin dalar a kasuwannin bayan fage tun gabanin yau talata da aka tashi da ƙamfar ta.

Buhari zai tafi London domin a duba lafiyarsa
31/10/2022

Buhari zai tafi London domin a duba lafiyarsa

Wasu 'yan gudun hijirar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka sun ce ba sa so su koma garuruwansu na asali saboda matsalar tsaro da...
11/10/2022

Wasu 'yan gudun hijirar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka sun ce ba sa so su koma garuruwansu na asali saboda matsalar tsaro da kuma rashin in da zasu zauna idan ma sun koma

Babban lauyan dake kare ASUU a kotu ya bayyana matakin da kungiyar ta dauka bayan umarnin kotu, za ta janye daga yaji.La...
10/10/2022

Babban lauyan dake kare ASUU a kotu ya bayyana matakin da kungiyar ta dauka bayan umarnin kotu, za ta janye daga yaji.

Lauyan ya kuma bayyana cewa, a cikin wasu 'yan kwanaki ne ASUU za ta janye yajin kowa ya koma makaranta.

Sanata Ibikunle Amosun wanda ya yi gwamna tsakanin 2011 zuwa 2019 ba zai marawa magajinsa kuma ‘dan jam’iyyarsa, Dapo Ab...
10/10/2022

Sanata Ibikunle Amosun wanda ya yi gwamna tsakanin 2011 zuwa 2019 ba zai marawa magajinsa kuma ‘dan jam’iyyarsa, Dapo Abiodun baya ba

A zaben da ya wuce, Amosun ya goyi bayan Adekunle Akinlade na APM, daga baya aka ji Akinlade ya koma jam’iyyar adawa ta PDP

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce shugaban kasar Muhammadu Buhari da kansa ne ya hana sanya sunan mataimakonsa Yem...
25/09/2022

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce shugaban kasar Muhammadu Buhari da kansa ne ya hana sanya sunan mataimakonsa Yemi Osinbajo a kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu.

Gwamnan Jihar Rivers a Najeriya Nyesom Wike ya yi ikirarin cewa dan takarar kujerar shugabancin kasar karkashin Jam’iyya...
24/09/2022

Gwamnan Jihar Rivers a Najeriya Nyesom Wike ya yi ikirarin cewa dan takarar kujerar shugabancin kasar karkashin Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya yi masa alkawarin takarar kujerar Majalisar Dattawa idan har ya amince da taimaka masa wajen samun nasarar zabe mai zuwa.

A yau ne alkalan gasar Hikayata suke zaman tantance labaran da s**a ciri tuta daga cikin guda 15 da alkalan s**a zaba.
22/09/2022

A yau ne alkalan gasar Hikayata suke zaman tantance labaran da s**a ciri tuta daga cikin guda 15 da alkalan s**a zaba.

Shugaban BoT-PDP na ƙasa ya jagoranci tawagar mambobi sun kai ziyarar neman sulhu ga gwamna Ortom na jihar Benuwai.Sanat...
21/09/2022

Shugaban BoT-PDP na ƙasa ya jagoranci tawagar mambobi sun kai ziyarar neman sulhu ga gwamna Ortom na jihar Benuwai.

Sanata Wabara yace tabbas komai ya lalace a PDP amma zasu shawo kan matsalar nan ba da jimawa ba. Ortom ya faɗa musu ra'ayinsa ɗaya da Wike.
Labarun Hausa

🗞 🇳🇪 Gwamnatin Amurka ta bai wa jamhuriyar Nijar tallafin wasu motoci 51 wadanda darajarsu ta haura million 13 na dolar ...
21/09/2022

🗞 🇳🇪 Gwamnatin Amurka ta bai wa jamhuriyar Nijar tallafin wasu motoci 51 wadanda darajarsu ta haura million 13 na dolar Amurka domin tallafa ma jami’an tsaron kasar a yakin da suke kafsawa da kungiyoyin ta’addancin Yankin Sahel.

Wata cibiya a Najeriya ta ce sam cin fatan dabbobi bai da wani amfani ko mamora a jikin dan Adam, kawai ana ci ne.Hakan ...
20/09/2022

Wata cibiya a Najeriya ta ce sam cin fatan dabbobi bai da wani amfani ko mamora a jikin dan Adam, kawai ana ci ne.

Hakan da wasu dalilai, ana duba yiwuwar haramta 'yan Najeriya mai da miyau da gandan fatan dabbobi gaba daya.

🗞 🇳🇬 A Najeriya duk da dokokin kare hakkin kananan yara da aka samar a wasu jihohin kasar, masu ruwa da tsaki wajen kare...
20/09/2022

🗞 🇳🇬 A Najeriya duk da dokokin kare hakkin kananan yara da aka samar a wasu jihohin kasar, masu ruwa da tsaki wajen kare hakkin yara na ci gaba da nuna damuwa akan yadda ake samun matsalolin.

Brighton ta sanar da nada tsohon kociyan Shakhtar Donetsk da Sassuolo, Roberto de Zerbi a madadin Graham Potter.
19/09/2022

Brighton ta sanar da nada tsohon kociyan Shakhtar Donetsk da Sassuolo, Roberto de Zerbi a madadin Graham Potter.

Tsarin, wanda ake kira The Merge, an yi shi ne don sauya wa masu korafi da ke ganin kudin kirifto na gurbata muhalli. Et...
18/09/2022

Tsarin, wanda ake kira The Merge, an yi shi ne don sauya wa masu korafi da ke ganin kudin kirifto na gurbata muhalli. Etherium na amfani da makamashi mai yawa a yanzu

Arsenal na kila-wa-kala kan dan kwallon Portugal, Xeka, wanda bai da kungiya a yanzu, bayan da aka yi mata tayin tsohon ...
17/09/2022

Arsenal na kila-wa-kala kan dan kwallon Portugal, Xeka, wanda bai da kungiya a yanzu, bayan da aka yi mata tayin tsohon dan wasan Lille mai buga tsakiya wanda aka gabatarwa da wasu kungiyoyin Premier League

Magoya bayan Peter Obi sun shirya yin gagarumin tattaki a Najeriya, magana ta kai an yi karar ‘Yan takaran LP, DSS, da G...
16/09/2022

Magoya bayan Peter Obi sun shirya yin gagarumin tattaki a Najeriya, magana ta kai an yi karar ‘Yan takaran LP, DSS, da Gwamnan Legas

Wani Lauya yace abin da ya faru bayan zanga-zangar EndSARS a 2021 zai maimaita kan shi muddin aka rabu da ‘Yan Obidients
Labarun Hausa

Liverpool ce kan gaba a rige-rigen da ta ke yi da Manchester United wajen neman dan wasa Borussia Dortmund Jude Bellingh...
16/09/2022

Liverpool ce kan gaba a rige-rigen da ta ke yi da Manchester United wajen neman dan wasa Borussia Dortmund Jude Bellingham mai shekara 19

‘Dan takaran PDP na zaben shugabancin kasa, Atiku Abubakar ya yi bayanin yadda zai farfado da tattalin arzikin kasaIdan ...
14/09/2022

‘Dan takaran PDP na zaben shugabancin kasa, Atiku Abubakar ya yi bayanin yadda zai farfado da tattalin arzikin kasa

Idan gwamnatin tarayya ta koma hannun Wazirin Adamawa a 2023, za a cire tallafin man fetur, a bunkasa MSME, a rage facaka
Labarun Hausa

Kazalika ambaliyar ta haddasa asarar gidaje da dabbobi da kayan amfanin gona da dama a yankin karamar hukumar Zaki ta ji...
13/09/2022

Kazalika ambaliyar ta haddasa asarar gidaje da dabbobi da kayan amfanin gona da dama a yankin karamar hukumar Zaki ta jihar.
Labarun Hausa

Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana 'yan Boko Haram da 'yan damfara kuma masu zamba a kasar nan.Ya kara da bayyana cewa m...
13/09/2022

Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana 'yan Boko Haram da 'yan damfara kuma masu zamba a kasar nan.

Ya kara da bayyana cewa mulkinsa yayi matukar kokari sai dai wadanda ya dace su yaba masa sun tsuke bakunansu.
Labarun Hausa

Mr Ruto ya lashe zaben ne da kashi 50.5 na kuri'u, yayin da Mr Odinga ya samu kashi 48.8. Mr Odinga ya yi zargin cewa a...
13/09/2022

Mr Ruto ya lashe zaben ne da kashi 50.5 na kuri'u, yayin da Mr Odinga ya samu kashi 48.8. Mr Odinga ya yi zargin cewa an tabka magudi a zaben, sai dai Kotun Koli ta yi watsi da zargin.
Labarun Hausa

Labarai sun fara yawo a jiya, ana cewa an samu bata-garin da s**a kai hari ga Peter Obi mai neman zama shugaban kasa a N...
13/09/2022

Labarai sun fara yawo a jiya, ana cewa an samu bata-garin da s**a kai hari ga Peter Obi mai neman zama shugaban kasa a Najeriya

Valentine Obienyem wanda shi ne mai magana da yawun bakin Obi, ya fitar da jawabi a yammacin Litinin, ya fayyace gaskiyar lamarin

Labarun Hausa

KO KUNSAN CEWA SARAUNIYAR INGILA TAREDA MIJINTA ZAA BINNETA?daga Labarun Hausa Philip & Elizabeth II  sun yi aure shekar...
12/09/2022

KO KUNSAN CEWA SARAUNIYAR INGILA TAREDA MIJINTA ZAA BINNETA?

daga Labarun Hausa

Philip & Elizabeth II sun yi aure shekara 75 (1947) da s**a wuce bayan doguwar Soyayya da Ƙauna.

Philip ya yiwa ran ki shi daɗe alƙawarin ko a MACE ko a RAYE ba zai taba rabuwa da ita b, kuma ba zai daina ƙaunarta ba. Kuma zai zama tare da ita cikin tsanani da kuma daɗi.

Philip ya rasu a watan Afirilu, shekarar da ta gabata (2021). Wasiyyarsa guda ɗaya da ya bari lokacin da zai rasu "Ku binne ni ranar da za binne Elizabeth".

Bayan mutuwarsa, aka ɗauke shi zuwa Maƙabarta ta wucin gadi (Royal Vault).

Kwanakin baya kaɗan ran ki shi daɗe "Elizabeth II" ita ma ta rasu (2022). Za a haɗata tare da Mijinta a binnesu don su cigaba da kurbar roman soyayya a Ƙabari.

Yanzu haka, ana shirye-shiryen binne Soyayya mafi tsaho da kuma daɗewa a tarihin ƙasar Birtaniya.

Duka 'ya'yan Sarauniya sun isa wurin da aka ajiye akwatin gawartaLabarun Hausa
12/09/2022

Duka 'ya'yan Sarauniya sun isa wurin da aka ajiye akwatin gawarta

Labarun Hausa

Wolves ta kammala daukar tsohon dan kwallon Chelsea, Diego Costa kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen kakar bana.Lab...
12/09/2022

Wolves ta kammala daukar tsohon dan kwallon Chelsea, Diego Costa kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen kakar bana.
Labarun Hausa

Mutumin Adamawa ya sa bankawa Ango da Amarya wuta saboda amaryar ta yaudaresa bayan sun yi alkawarin aure Wanda aka baiw...
11/09/2022

Mutumin Adamawa ya sa bankawa Ango da Amarya wuta saboda amaryar ta yaudaresa bayan sun yi alkawarin aure

Wanda aka baiwa aikin kisan ya aikata hakan bayan biyansa Naira Dubu Biyar da kwanon shinkafa 4
Labarun Hausa

Za a fara gudanar da al'amura tun daga yau Lahadi har zuwa Litinin 19 ga watan Satumba da za a binne taLabarun Hausa
11/09/2022

Za a fara gudanar da al'amura tun daga yau Lahadi har zuwa Litinin 19 ga watan Satumba da za a binne ta
Labarun Hausa

Shin ko kafafen yada labarai sun soma aiki da umarnin NBC na haramta wakar Ado Issa Gwanja mai taken "Warr"?
10/09/2022

Shin ko kafafen yada labarai sun soma aiki da umarnin NBC na haramta wakar Ado Issa Gwanja mai taken "Warr"?

Sarauniya Elizabeth II ita ce basarakiya da ta fi dadewa a kan kujerar mulkin Birtaniya a yayin da ta rasu tana da sheka...
10/09/2022

Sarauniya Elizabeth II ita ce basarakiya da ta fi dadewa a kan kujerar mulkin Birtaniya a yayin da ta rasu tana da shekara 96.

An santa a matsayin mace mai basira da raha.

Ga wasu hotunanta a yayin da take cikin nishadi a shekaru 70 da ta shafe a kan mulki.

Labarun Hausa

Jami'an rundunar yan sanda a jihar Zamfara sun kai samame mabuyar wasu yan ta'adda da s**a addabi al'umma a kananan huku...
10/09/2022

Jami'an rundunar yan sanda a jihar Zamfara sun kai samame mabuyar wasu yan ta'adda da s**a addabi al'umma a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum.

Yan sanda sun cafke wani kasurgumin dan bindiga da ake nema ruwa a jallo mai suna Isiyaku Babangida a yayin samamen.
Labarun Hausa

Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar tarayya ya wallafa hotunan sallar Juma'a da s**a yi tare da Bola Tinubu da Kashim S...
09/09/2022

Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar tarayya ya wallafa hotunan sallar Juma'a da s**a yi tare da Bola Tinubu da Kashim Shettima a yau a Abuja.

Hotunan sun dauki hankulan mutane a dandalin sada zumunta inda s**a rika bayyana mabanbantan ra'ayoyi.
Labarun Hausa

An yi zabuka watannin baya a jihohin Ekiti da Osun, an fadi sakamakon zabe, an yi sabbin gwamnoni.Sai dai, INEC ta ce ma...
09/09/2022

An yi zabuka watannin baya a jihohin Ekiti da Osun, an fadi sakamakon zabe, an yi sabbin gwamnoni.

Sai dai, INEC ta ce madatsa a nahiyar Asiya sun yi kokarin datsar tashar yanar gizon duba sakamakon zabe.
Labarun Hausa

Basarakiyar ta kwashe sama da shekaru 70 tana kan karagar mulkin kafin ta rasu a ranar Alhamis.Jim kadan bayan rasuwarta...
09/09/2022

Basarakiyar ta kwashe sama da shekaru 70 tana kan karagar mulkin kafin ta rasu a ranar Alhamis.

Jim kadan bayan rasuwarta, 'yan Najeriya sun bayyana hotunan atamfofi masu dauke da hoton sarauniyar matsayin ankon bikin mutuwarta.
Labarun Hausa

Hotunan yadda masu alhini na ci gaba ajiye furanni a wurare daban-daban a fadin duniya Labarun Hausa
09/09/2022

Hotunan yadda masu alhini na ci gaba ajiye furanni a wurare daban-daban a fadin duniya

Labarun Hausa

Shugabannin kasashen duniya da sauran jami’an diflomasiya na ci gaba da nuna alhinin game da mutuwar Sauraniya Elizabeth...
09/09/2022

Shugabannin kasashen duniya da sauran jami’an diflomasiya na ci gaba da nuna alhinin game da mutuwar Sauraniya Elizabeth ta II, wacce ta rasu tana da shekara 96 a duniya.

Sun yaba da yadda ta saudakar da kai wajen gudanar da aikinta da jajircewarta da kuma kasancewarta mai fara’a da kyautatawa.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya jagoranci shugabannin da s**a nuna alhini inda ya tuna da “Sarauniya a matsayin mai kirki” wacce ta kasance abokiyar Faransa”.

Tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya ce Sauraniya ta ja hankalin kasashen duniya a kan yadda ta rika mulki kuma ta rika aiki ba dare ba rana.



"Sau da yawa mun rika ganin yadda take mu’amala da mutane inda take magana da su cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da raha,” a cewar Mr Obama, wanda ya gana da sarauniya a lokuta da dama.

Shugaban Amurka na yanzu Joe Biden ya bayyana Sarauniyar a matsayin sarauniyar da ta kafa “tarihi a zamanin nan.”



Da yake magana a kan ziyararsa a Birtaniya a shekarar 2021 a matsayin shugaban kasa, Mista Biden ya ce “ ta nuna mana hazakarta da kirkinta da kuma hikimarta.”

Sarauniya Elizabeth ta biyu ta gana da shugabannin Amurka 14 a lokacin mulkinta
Labarun Hausa

Babban Dan Sarauniya Elizabeth, Yarima Charles, Ya Zama Sabon Sarkin Ingila, Ya Saki Jawabinsa Na Farko Sauran 'yayanta ...
08/09/2022

Babban Dan Sarauniya Elizabeth, Yarima Charles, Ya Zama Sabon Sarkin Ingila, Ya Saki Jawabinsa Na Farko

Sauran 'yayanta sun hada da Gimbiya Anne, 72, Yarima Andrew, 62, da Yarima Edward, 58.
Labarun Hausa

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II ta rasu, a cewar Fadar Buckingham.Labarun Hausa
08/09/2022

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II ta rasu, a cewar Fadar Buckingham.
Labarun Hausa

Address

Maiduguri

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Labarun Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category


Other Newspapers in Maiduguri

Show All

You may also like