21/08/2024
*INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI’UN 😭😭😭*
*Sakon Ta'aziya Daga Tawagar FAG FIN BORNO MEDIA TEAM Zuwa Ga Al'ummar Musulmi, Da Najeriya Bisa Kisan Gillar Da 'Yan Bindiga S**a Yi Wa Sarkin*
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Muna isar da wannan sakon ta'aziyya ga daukacin al'ummar Musulmi da 'yan Najeriya bisa wannan babban rashi na kisan gillar da 'yan bindiga s**a yi wa mai martaba Sarkin Gobir, Alhaji Isah Muhammad Bawa. Wannan lamari ya girgiza zukatanmu, domin ya kasance babban rashi ga masarautar Gobir da al'ummar Musulmi baki daya.
A madadin shugaban rundunar 'yan agajin kungiyar Fityanul Islam na kasa, reshen jihar Borno, Brig. Gen. Muhammad Abdullahi, tare da dukkan 'yan agajin jihar, muna mika sakon ta'aziyya zuwa ga masarautar Sarkin Musulmi, da masarautar Gobir, dake ƙaramar hukumar sabon birni a jihar Sokoto da dukkan al'ummar Musulmi, da Najeriya. Muna tare da ku a cikin wannan lokaci na alhini da jimami.
Rahotanni daga jihar Sokoto sun nuna cewa har yanzu ana cikin zaman jimami da jiran dawowar wadanda s**a tafi kai kudin fansar marigayi Sarkin Gobir. Wannan kisan gillar da aka yi masa a hannun 'yan ta’adda ya kasance babban rashi da ba za a manta da shi ba.
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya gafarta wa marigayi Sarkin, ya sa ya huta cikin rahamarSa, ya kuma sanya shi a Aljannah Firdaus.
Muna rokon Allah ya kare mu daga sharrin azzalumai, ya kuma tona asirin wadanda s**a aikata wannan mugun aiki na kisan gillar. Allah ya tabbatar da zaman lafiya a cikin kasarmu, ya tsare mu daga dukkan fitintinu, ya kuma jaddada alherin Sa a cikin rayuwarmu.
Amin 🤲
Rabiu Babayo ✍️
*SIGN📝*
Yakubu Mustafa Grema
FAG/FIN/BORNO/MEDIA/TEAM.