Shababul mukhtariyyah TV

  • Home
  • Shababul mukhtariyyah TV

Shababul mukhtariyyah TV show casing islamic event

27/02/2025

Amsar tambaya ta daya da Dr sharif Sadiq ya kalubalencemu akai kuma yace inde muka kawo zai bada dubu dari biyar

24/02/2025
24/02/2025

RUBUTU NA SHIDA KUMA GYARA NA BIYAR DAGA CLIP ƊIN SHARIF SADIQ NA HUDU AKAN HADISIN NANA AISHA DA YA KAFA HUJJA DASHI

Maganar Gaskiya nayi mamakin hujjar da sharif ya kawo akan cewa wai ga nana Aisha ta raɓawa annabi kalmar الهوى kuma har yake ganin cewa ya samu lasisin da zai iya gayawa annabi.

Na farko dai kafin na fara magana akan hadisin yana da kyau ace duk fannin da mutum yake da'awar ya karanta a jami'a ko ya mayar da hankalinsa akai to bai kamata ana samun wasu kananun kura-kurai ba daga gurinsa a fannin, abinda yasa nayi maganar nan shine an daɗe ana ce mana sharif sadiq Muhaddithi ne (ma'ana malamin hadisi) sai gashi a matsayinsa na muhaddithi ta bayyana gurin mu almajirai cewa bashi da zurfin bincike a sana'ar sa,kuma bashi da diqqah da tahqeequl masa'il

Sharif ya kawo hadisin nana aisha da yazo a littafin Al-imamul bukhari inda take cewa

ما أَرى ربك إلا يُسارِع في هواك.

"bana ganin ubangijin ka, face yana rige-rige a cikin yardarka" (ma'anar maganar ta dai "Ni gani nake kamar ma ubangijin naka rige-rige yake a cikin yardarka")

duk da shi sharif ya fassara kalmar nan ta الهوى da tazo a hadisin da "son rai" wadda ita ma ba haka malaman hadisi s**a fassara ta ba.

Zanso malam ya duba babban littafin sharhi na Sahihul bukhari mai suna Fathul bariiy na Al-haafiz ibnu-hajar Al'asqalani, wannan littafin fa shine littafin da malamai suke masa kirari da faɗin Annabi cewa

لا هجرة بعد الفتح

Babu hijirah bayan Fathu makkah, ma'ana dai kamar yadda annabi yace babu hijra bayan fathu makkah hakanan malamai na cewa babu wani sharhi da za'ayi bayan fathul bariiy da zai kai shi in dai akan sharhin sahihul bukhari ne

A ciki ne Al-haafiz ibnu hajar yake cewa a karkashin sharhin wannan hadisin

قَوْلُهُ: (مَا أَرَى رَبَّكَ إِلَّا يُسَارِعُ فِي هَوَاكَ) فِي رِوَايَةِ مُحَمَّدِ بْنِ بِشْرٍ: إِنِّي لَأَرَى رَبَّكَ يُسَارِعُ لَكَ فِي هَوَاكَ: أَيْ فِي رِضَاكَ، قَالَ الْقُرْطُبِيُّ: هَذَا قَوْلٌ أَبْرَزَهُ الدَّلَالُ وَالْغَيْرَةُ، وَهُوَ مِنْ نَوْعِ قَوْلِهَا مَا أَحْمَدُكُمَا وَلَا أَحْمَدُ إِلَّا اللَّهَ، وَإِلَّا فَإِضَافَةُ الْهَوَى إِلَى النَّبِيِّ ﷺ لَا تُحْمَلُ عَلَى ظَاهِرِهِ؛ لِأَنَّهُ لَا يَنْطِقُ عَنِ الْهَوَى وَلَا يَفْعَلُ بِالْهَوَى، وَلَوْ قَالَتْ إِلَى مَرْضَاتِكَ لَكَانَ أَلْيَقَ، وَلَكِنَّ الْغَيْرَةَ يُغْتَفَرُ لِأَجْلِهَا إِطْلَاقُ مِثْلِ ذَلِكَ

Faɗarsa cewa :
‎ "ما أرى ربك إلا يسارع في هواك"
acikin riwayar muhammad bin bishrin kuma:
إني لأرى ربك يسارع لك في هواك أي في رضاك
ai ana nufin (fi ridaaka) a cikin yardarka
قال القرطبي :
Al'imamul qurɗubiy yace
هذا قول أبرزه الدلال و الغيرة
wannan zance ne wanda shagwaɓa da kishi ne yasa ta faɗe shi
وهو من نوع قولها ما أحدكما و لا أحمد إلا الله
wannan kuma yana daga cikin nau'in faɗin ta na cewa "bazan gode muku ba (ku biyu) kuma ba zan godewa kowa in ba Allah ba" (domin lokacin da aka yi mata ƙazafi,manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ɗan saurara yaji hukuncin Allah, to bayan Allah ya saukar da aya akan cewa ƙazafi aka yi mata,kuma ya tsarkake ta daga barin ƙazafin da aka yi mata sai aka ce mata taje ta sami manzon Allah, ita kuwa tace baza ta same shi ba kuma baza ta godewa kowa idan ba Allah ba" wanda anan ma malaman hadisi sun ce irin wannan lafazi nata za'a yi mata uzuri akansa duba da sha'anin insaniyyah ta mutum.

sai Al-imamul qurɗubiy ya cigaba da cewa
و إلا فإضافة الهوى إلى النبي لا تحمل على ظاهرها
idan kuwa ba haka ba, to raɓa kalmar الهوى zuwa ga Annabi baza a ɗauke ta a zahirinta ba, kamar dai yadda sharif yake ganin cewa gata tazo a hadisi shi yasa zamu iya raɓawa janibin manzon Allah duk da gashi anan ance ko da a hadisin ne bai kamata a ɗauke ta a zahirin ma'anar ta ba.
sai ya ci gaba da cewa
لأنه لا ينطق عن الهوى و لا يفعل بالهوى
domin manzon Allah baya furuci daga son ransa kuma baya aikata san ransa
و لو قالت إلى مرضاتك لكان أليق
dama nana Aisha radiyyallahu anha cewa tayi "zuwa abinda ka yarda" da yafi dace wa, kamar yadda muma mukace, da sharif yace "RA'AYIN ANNABI" maimakon "son rai" da yayi amfani da shi a maganar sa da yafi dacewa
و لكن الغيرة يغتفر لأجلها إطلاق مثل ذلك
Amma sai dai cewa kishi ana yafiya, sabida hakan ne ta iya faɗin kalmar da ta faɗa (ma'ana kalmar الهوى ) ga halarar annabi...

Qalubalen da muke dashi akan sharif shine

1) Ga Alhafiz ibnu hajar ya naqalto maganar Al-imamul qurɗubiy akan cewa nana Aisha ma uzuri za'ayi mata ne sabida kishi da kuma shagwaba irin ta mata amma idan ba haka ba, bai dace ta gayawa Annabi kalmar الهوى ba domin Allah ya riga ya tsarkake shi, to muna so sharif ya kawo mana malami ɗaya da ya yarda cewa ita wannan kalmar za'a iya amfani da ita ga annabi kamar yadda ya faɗa ?

2) sa'annan kace ita kalmar nan tana cikin shari'a, yanzu shin samun kalma a cikin nassin Alqur'ani ko hadisi shine yake bada lasisin cewa kalmar nan karɓaɓiyyah ce za'a iya amfani da ita akan kowa ?

3) idan amsar ka "eh" ce, to ya zaka yi da ayar
و عصى آدم ربه فغوى
ga shi a cikin alqur'ani tazo amma kuma kai kasan cewa baka isa ka gayawa annabi Adam wannan kalmar ba duk da Allah ne ya bamu labari kuma munsan Allah baya ƙarya, dole maganganun malaman tafsiri zaka komawa kamar yadda muma akan kalmar الهوى muka koma gurin malaman hadisi, to meyasa bakayi yadda mukayi ba ya sharif ? (sai ka tsaya akan cewa ai tinda tazo a hadisi shikenan akwai ta a shari'ah )

4) idan Amsar ka "A'a" ce, to me yasa baza mu dubi Allah mu yarda cewa amfani da kalmar "son rai" a halarar Annabi sallallahu alaihi wa sallam kuskure ne ba?

5) a cikin clip dinka kace duk mutumin da ya san darajar manzon Allah, idan aka ce masa "son ran manzon Allah" ba zai zo masa a kwakwalwa cewa akwai wata ma'anar da take nufin naqsu a kalmar ba, sai nace kenan su Al-imamul qurɗubi da Al-hafiz ibnu hajar da s**ayi wa wannan maganar tawili har suke cewa bata dace a raɓata ga annabi ba,da ma ace nana aisha ta ce "yardar annabi" da yafi dacewa, suma kenan basu san darajar Annabin bane yasa s**a ce kalmar bata dace ba koh ?

6) ya maulana sharif kace wai mun shiga hallaka sabida munce wannan kalmar bata dace ga Martabar Annabi ba, kenan kafin mu shiga hallakar nan da kake faɗa,su Al-hafiz ibnu hajar da Al-imamul qurɗubiy tun tuni s**a shige hallaka tunda suma irin ra'ayin mu ne dasu koh ?

7) sa'annan ka jefe mu da jahilci sabida mun saɓa maka a wannan mas'alar, shin suma su Al-hafiz ibnu hajar da Al-imamul qurɗubiy da muke da ra'ayi irin nasu suma jahilai ne ? (domin kowa yaga cewa sun saɓa maka suma)

Akwai tambayoyi dayawa da suke bijiro da kansu a mas'alar nan amma gudun kada mu matsa maka dayawa, shi yasa zamu takaita anan, amma kuma muna so idan zaka bada amsar wannan qalubalen da muka jefa maka Guda 7 ka haɗa mana da qalubalen da mukayi maka a baya ! ma'ana tambayoyin da muka yi maka a baya duk a hada a bamu amsar su

Allah ya sa mu dace

23/02/2025

RUBUTU NA BIYAR KUMA GYARA NA HUDU DAGA CLIP DIN SHEIKH SHARIF SADIQ NA BIYU AKAN MAGANARSA TA CEWA MUTUM KO FATIHA DA ƘULHUWALLAHU YA IYA ZA'A BASHI LIMANCIN JUMU'A

Duk da munyi magana akan wannan mas'alar a baya, tare da karanto masa sharuɗan da malamai s**a rattabo, sai naga ya kyautu a kara yi masa ilzami da wasu hujjojin daban dan a kara nuna masa cewa wannan fatawar da ya bayar ta saɓawa malaman malikiyyah gaba ɗayan su (abisa binciken da nayi,wallahu a'alam)

Yazo a cikin كتاب الكافي في فقه أهل المدينة المالكي na Abu umar yusuf bin abdillahil qurɗabiy inda yake cewa a karkashin babul imamati (Ma'ana babin limanci)

و ينبغي أن يختار الإمام الراتب فيكون فقيها عالما بأحكام الصلاة محسنا بالقرآن سالما من البدع، و الكبائر،

yake cewa "kuma ya kamata a zaɓo limami ratibi,sa'annan ya kasance Masani (ma'ana Malami) kuma wanda ya san hukunce-hukuncen sallah, wanda ya iya karatun Alqur'ani, kuma wanda ya ƙubuta daga aikata bidi'a, ko kuma manya-manyan zunubai"

To Anan ne nake so na tambayi Sheikh Sharif sadiq shin idan har za'a rattabowa limami ratibi wannan sharuɗan, ashe ba limamin jumu'a bane yafi cancanta da ace ya cike wa'ennan ba ?

to me yasa malam zai ce ko fatiha da ƙulhuwallahu ?
sa'annan dai Sheikh abu umar Alqurɗubiy ya cigaba da cewa

و رب المنزل أولى بالإمامة فيه إن كان يحسن الصلاة من الفقيه و غيره، و لا يتقدمه في منزله أحد إلا بإذنه

"kuma mai gida shi yafi cancanta da yayi jagorancin sallah (a gidansa) idan har ya iya sallar akan malami ko kuma waninsa, kuma kada wani yace zai ja shi sallah a gidansa ba tare da izininsa ba"

Ashe dai maganar da sharif ya faɗa ta cewa idan sarki yazo gidanka shine zai bada sallah, bata da wani asali, idan kuma akwai to malam ya kawo mana wani magabaci da ya fadi hakan...

kuma ina so malam ya sani, hadisin

و لا يؤمن الرجل الرجل في سلطانه

ma'ana kada wani ya bawa wani sallah a inda yake da iko, dashi ne fa malamai s**ayi amfani s**a fitar da hukuncin cewa mai gida shine yake da hakkin bayar da sallah a gidansa, ba wani sarki ba ko wani malami, shi yasa wannan yake kara tabbatar mana cewa mune muka fassara hadisin daidai, shi malam kuwa da ya samu kuskure a fassarar shi yasa lamarin ya hargitse masa...

Na biyu yazo a cikin fathul jawad sharhin askari na shehu yahuza zariya inda shehu yahuza yake kawo sharuɗan limanci yana cewa

و العلم بما لا تصح الصلاة إلا به من قراءة و فقه و عدالة و قدرة على الأركان،

da kuma ilimin abinda sallah bata inganta sai dashi na daga karatun Alqur'ani da kuma sanin fiqihu (ma'ana hukunce-hukuncen sallah) da adalci da kuma ikon kawo rukunan sallah daidai

فالجاهل بالقراءة أو الفقه لا تصح صلاة المقتدي العالم به

ma'ana "sallar malami wanda ya iya karatu kuma yasan hukunce-hukuncen fiqihu bata inganta ba a bayan jahili wanda bai san su ba"

Tambayata anan itace, shin shehu yahuza zariya bai san cewa Za'a iya bawa wanda ya iya fatiha da kulhuwallahu limanci bane, amma ya kawo wannan sharuďan a cikin fathul jawadi ?

Na uku yazo a cikin littafin mu'iinut talameez sharhin risala ta abu zaidinil qairawaniy wanda sheikh uthman bin umar yayi inda ya kawo sharuɗa goma wanda Al-imamus sanhuuriy yayi akan sharaɗin limami a ciki akwai

تطهيره و قدرة منه على....أركانها و علمه عند الملا
بما يصحح الصلاة شغل....في ذمة منه و هذا نقل

daga cikin sharuɗan limami akwai "Ya tsarkake (jikinsa da bagiren sallar sa) kuma ya kasance yana da ikon kawo rukunanta (yadda suke), Sa'annan ya na da masaniya akan abubuwan da suke inganta sallah,(domin) wani nauyi ne a wuyansa da sai ya sauke, kuma wannan abin cirowa ne (daga litattafan malamai)

To shi Al-imamus sanhuuriy bai san cewa za'a iya bawa mutum limanci koda fatiha da kulhuwallahu ya iya ba, da har zai kawo wannan sharaɗin ?

Shi yasa muna kira zuwa ga malam da ya dubi Allah idan za'ayi fatawa a dena fatawa ba tare da anyi zurfin bincike akan masa'ilu ba, akan mas'alar fatiha da kulhuwallahu dinnan akwai maraji'u da dama da zamu iya yiwa malam ilzami dasu, amma kuma zamu taƙaita anan kuma daga karshe duk mai son gaskiya muna fatan ya bibiyi litattafan da muka ambata dan yasan ba ƙarya muke ba, kuma mutum zai iya duba Sharhin ibnu-aashir ta Sheikh Ahmad Mustapha Aɗ-ɗahɗaawiy don neman karin bayani domin shi har bayani yayi akan cewa wanda yake lahani a karatun Alqur'ani ma bai halatta a bishi sallah ba, kamar yadda kuma kowa yaji ayar da sharu sama'ila ya jawo a huɗubar sa ta shekaran jiya, da kuma ayar da ya jawo ta cikin suratul Ahzab a sallah

Allah yasa mu dace

15/02/2025

INA NE MAƘURA ? FADAR SARKI KO KUMA ZAWIYOYI DA MASALLATAN MALAMAI

abin mamaki ne sosai kaga malami yayi gina istidlalinsa (hujjarsa) da karshen aya kuma yace abinda yazo kafin wannan ayar shine hukunci na ƙarshe...

Abinda nake so nace shine,akwai wani clip da yake yawo na wani malami daga malaman Agege wanda a ciki yake kira zuwa ga faɗin Allah cewa

و إن تنازعتم في شيء فردوه إلى الله و الرسول

"idan kun samu jayayya a cikin wani abu, to ku mayar dashi zuwa ga Allah da manzon sa"

sai yake cewa, ai babu abinda yafi dacewa a mas'alar masallacin Agege kamar a koma zuwa gidan sarki, domin Allah subhanahu wa ta'ala yana cewa

يا أيها الذين آمنوا أطيعوا الله و أطيعوا الرسول و أولي الأمر منكم

"ya ku wayenda kukayi imani, kuyi ɗa'a ga Allah, kuma kuyi ɗa'a ga manzonsa da kuma majiɓanta lamuranku"

Har yake cewa jamhurin malamai sun tafi akan cewa ana nufin "sarakuna" kamar yadda yazo a tafsirin ibnu katheer, har ya kara da cewa idan mukayi duba zuwaga ANNAZMUL QUR'ANIY ma yana tabbatar da hakan, domin Allah ya fara jan kunnen bayinsa ne zuwa ga Adalci a ayar da ta gabaci wannan ayar, daga nan kuma sai yayi umarni da yi masa biyayya dashi da manzon sa da kuma masu mulki (wato sarakuna)

sai ni nake gani kamar an chakuɗa takardu a wannan bayanin, domin in har munyi duba dakyau da ANNAZMUL QUR'ANIY (Tsari irin na al'qur'ani) zamuce fasahar Allah ta wuce inda malam ya tsaya, domin Allah yace

إِنَّ اللَّهَ يَأْمُرُكُمْ أَن تُؤَدُّوا الْأَمَانَاتِ إِلَىٰ أَهْلِهَا وَإِذَا حَكَمْتُم بَيْنَ النَّاسِ أَن تَحْكُمُوا بِالْعَدْلِ ۚ إِنَّ اللَّهَ نِعِمَّا يَعِظُكُم بِهِ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ سَمِيعًا بَصِيرًا *** يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنْكُمْ فَإِنْ تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ...

"Lallai Allah yana umartarku ga mayar da Amana zuwa ga ma'abotan ta, kuma idan zakuyi hukunci tsakanin mutane kuyi da Adalci, Lallai madallah da abin nan da Allah yake yi muku wa'azi akan sa, Lallai Allah ya kasance mai ji ne ga abinda kuke faɗa, kuma mai gani ne ga abinda kuke aikatawa"
"ya ku wa'enda kukayi imani kuyi ɗa'a ga Allah kuma kuyi ɗa'a ga manzon sa da masu jibantar lamari daga cikin ku, idan kuma kun samu jayayya a cikin wani abu, to ku mayar dashi zuwa ga Allah da manzon sa....

To anan idan muka duba zamu ga cewa a tsarin yadda allah ya jeranta ayoyin nan guda biyu na farko dai ya fara kiran bayi zuwa ga yin Adalci da kuma mayar da Amana ga masu ita, daga nan kuma sai yayi wa bayin sa umarni da yin ɗa'a ga majiɓanta lamarinsu, idan kuma har Adalcin nan da Allah yace ayi bai samu ba, a gurin shuwagabannin nan naku, sai ku mayar da lamarin zuwa ga Allah da manzon sa, ma'ana a koma gurin malamai su faɗa mai Allah yace mai Annabi yace, anan malamai sune wanda zasu yi Alƙalanci tsakanin mabiya (yen gari) da masu jiɓantar lamarinsu (sarakuna) ta hanyar gaya musu mai Allah da Annabi s**a faɗa, sabanin yadda malam yace wai malamai ne zasu je sarki yayi musu hukunci !!!

Ibnu Aashuur a cikin tafsirin sa na "AT-TAHREER WAT TANWEER" yana cewa

‎ولَمّا كانَتِ الحَوادِثُ لا تَخْلُو مِن حُدُوثِ الخِلافِ بَيْنَ الرَّعِيَّةِ، وبَيْنَهم وبَيْنَ وُلاةِ أُمُورِهِمْ، أرْشَدَهُمُ اللَّهُ إلى طَرِيقَةِ فَصْلِ الخِلافِ بِالرَّدِّ إلى اللَّهِ وإلى الرَّسُولِ، ومَعْنى الرَّدِّ إلى اللَّهِ الرَّدُّ إلى كِتابِهِ، كَما دَلَّ عَلى ذَلِكَ قَوْلُهُ في نَظِيرِهِ ﴿وإذا قِيلَ لَهم تَعالَوْا إلى ما أنْزَلَ اللَّهُ﴾ [النساء: ٦١] . ومَعْنى الرَّدِّ إلى الرَّسُولِ إنْهاءُ الأُمُورِ إلَيْهِ في حَياتِهِ وحَضْرَتِهِ، كَما دَلَّ عَلَيْهِ قَوْلُهُ في نَظِيرِهِ ﴿وإلى الرَّسُولِ﴾ [النساء: ٦١] فَأمّا بَعْدَ وفاتِهِ أوْ في غَيْبَتِهِ، فالرَّدُّ إلَيْهِ الرُّجُوعُ إلى أقْوالِهِ وأفْعالِهِ، والِاحْتِذاءُ بِسُنَّتِهِ

"Tunda kuwa lamarurruka baza su taɓa kuɓuta daga samuwar saɓani tsakanin wanda ake mulka (yen gari) da masu mulki (sarakuna) ba, sai Allah ya shiryar dasu zuwaga tafarkin yanke saɓani ta hanyar komawa zuwa ga Abinda Allah subhanahu wa ta'ala ya faɗa da kuma manzonsa,shi kuma ma'anar mayar da abu zuwa ga Allah shine a duba Alqur'ani mai Allah ya faɗa,shi kuma ma'anar mayar da lamari zuwa ga manzon Allah kuwa shine akai mas'alar gabansa lokacin da yake raye, amma bayan wafatinsa kuma ko faƙuwarsa sai mu koma zuwa ga maganganunsa da ayyukansa ta hanyar bin sunnar sa"

Kaga kuwa babu yadda zamu san me Allah ya faɗa ko kuma annabinsa ba tare da mun koma zuwa ga malamai ba, sabanin abinda aka cewa wai a koma gidan sarki !!!

Shiyasa idan zamuyi amfani da siyaƙin ayar nan da kuma ANNAZMUL QUR'ANIY sai muce
Allah yayi kira zuwa ga Adalci da mayar da amana zuwa ga masu ita,ayayin da shugaba yayi adalci, to wajibi ne a bishi don cika umarnin Allah subhanahu wa ta'ala, ayayin da aka samu sabani tsakanin masarauta da yen gari sai dukkaninmu mu koma gurin Allah da manzon sa, wato mu samu malamai su gaya mana wanene yafi dace wa da yayi limanci a faɗin Allah da manzon sa...

Insha Allahu, a saurari rubutu na biyu akan maganar wanda yafi cancanta da limanci sarki ko Wanda yafi kowa sanin Littafin Allah.

Listen to audio if u dont have time to read

01/02/2025

Labarin gaskiya

29/01/2025

DAGA CIKIN ABINDA KHALIFAN SHEIKH ADAM ABDULLAHI AL-ILORY (MUDIRUL MARKAZ) YA FAƊA GAME DA LIMANCIN MASALLACIN HAUSAWA NA AGEGE

"Shi SARKIN HAUSAWA an yarda (sarki ne) amma ba Malami bane, Shi yasa ya bar aikin malinta ga Malamai, kada ya dinga shiga"

Kaji aikin ilimi da hankali !!!

Address


Telephone

+2349043885218

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Shababul mukhtariyyah TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Shababul mukhtariyyah TV:

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share