18/07/2024
SAKO ZUWA GA MASU HANKALI
Yau ina karanta littafin babban malami Muhammad bin Alwaleed Aɗɗurɗushiy (R:52.H) Allah ya jiƙansa, wato:
📗"سراج الملوك*
sai na ci karo da wata maganarsa cike da hikima, da wa'azi, sai na ga ya kamata in kwafo ta kuma in fassara ta domin masu hankali su ƙara natsuwa ta sanadiyyarta.
Ga ta kamar haka:
إذا رأيت إنساناً هجَّاما على أعراض الناس وثلبهم؛ فقد يماثل أخلاق الكلاب، فإن دأب الكلب أن يجفو من لا يجفو، ويبتدئ بالأذية من لا يؤذيه، فعامله بما كنت تعامل به الكلب إذا نبح عليك، ألست تذهب في شأنك وتتركه ولا تخاصمه، ولا تسبّه، فافعل بمن يهتضم عرضك مثل ذلك.
وإذا رأيت إنساناً قد جُبل على الخلاف، إن قلت: لا، قال: نعم، وإن قلت: نعم، قال: لا، فألحقه بعالم الحمير، فإن الحمار إذا أدنيته بعد، وإن أبعدته قرب، وأنت تستمتع بالحمار ولا تسبّه، ولا تفارقه، فاستمتع أيضا بهذا الإنسان ولا تفارقه، ولا تسبّه
وإذا رأيت رجلاً يذكر من عثرات الناس وسقطاتهم فمثله في الآدميين كمثل الذباب في عالم الطير، فإن الذبابة تقع على الجسم فتتحامى صحيحه وتطلب المواضع النغلة منه ذوات المدة والدم، والنجاسة، فاستر ذلك الموضع ولا تخاصمه.
*سراج الملوك صــ١٣٠، ط: عالم الكتب القاهرة.*
*Fassara:*
Idan ka ga mutum ba shi da aiki sai kutsawa cikin mutuncin mutane, yana keta shi, yana kuma aibanta su, to tabbas yana da halin karnuka, domin halin kare shi ne yin wauta ga ga wanda bai ci ba bai sha ba, ya cutar da wanda bai masa komai ba, saboda haka in aka jarrabe ka da irinshi sai ka mu'amalance shi kamar yadda kake mu'amalantar kare idan yayi maka haushi, ba tafiya kake zuwa lamarinka kake yi ka ƙyale shi ba? To shi ma wannan mutumin yi mi shi haka.
Hakazalika in ka ga mutum ɗabi'arsa ita ce son saɓa maka, in ka ce: a'a, sai ya ce: ƴe, in kuma da za ka ce: ƴe, to shi a'a zai ce, to ka haɗa shi da jakuna a hali, domin shi jaki in ka matso da shi sai ya yi nisa, in kuma ka nisantar da shi sai ya matso, amma ai haka nan kake cin gajiyarshi ko? ba ka zaginshi ba ka jayayya da shi, to shi ma wannan mutumin ka ci gajiyarsa, kar ka rabu da shi kuma kar ka taɓa zaginshi.
Kuma har wala yau in ka ga wani mutum aikinsa shi ne ambaton aibun mutane da gazawarsu, to wannan kamar ƙuda yake a cikin halittu masu tashi sama, domin ƙuda ya kan sauka a jiki, sai ya ƙyale lafiyayyen bagire, amma ya hau kan mai gyambo da jini da mugunya da ƙazanta, saboda haka in za ka iya to rufe wajen ciwon, amma kar ka sake ka ja da shi.
✍️ Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria Hafizahullah
Safiyar Litinin
09 Al-Muharram, 1446H
15 Yuli, 2024M