Arewa Hausa Media News TV

Arewa Hausa Media News TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Arewa Hausa Media News TV, Media/News Company, Kiyawa.
(2)

An yi ta yada jita-jitar cewa Qatar ta yi fatali da bukatar Tinubu. Karin bayani a sashin sharhi.Hoto: Bola Tinubu/Faceb...
25/02/2024

An yi ta yada jita-jitar cewa Qatar ta yi fatali da bukatar Tinubu. Karin bayani a sashin sharhi.

Hoto: Bola Tinubu/Facebook.

Hotuna 📷 Rijiyar HudabiyaWannan rijiya ta kasance wurin mu'ujizar da Manzon Allah (SAW) ya yi a lokacin zamansa a Hudabi...
24/02/2024

Hotuna 📷 Rijiyar Hudabiya

Wannan rijiya ta kasance wurin mu'ujizar da Manzon Allah (SAW) ya yi a lokacin zamansa a Hudabiya a shekara ta 6 bayan hijira.

Ruwa ya fito daga rijiyar Hudabiya

Manzon Allah (SAW) da Sahabbai sun yi sansani a Hudabiya na ’yan kwanaki a lokacin da ‘Yarjejeniyar Ridwan’ da Hudabiya Haka nan kuma a Hudabiya ne wasu mu’ujizozi s**a faru a hannun Manzon Allah (SAW), wanda hakan ya kara wa yankin tarihi Mai muhimmanci.

Bara'a (رضي الله عنه) yana cewa: Sahabbai sun kai Dubu da Dari hudu a Hudabiya, kuma akwai rijiya daya tilo da ta kafe saboda yawan amfani da ita. Sai Manzon Allah (SAW) ya je bakin rijiyar ya yi tofi da Bakinsa Mai Albarka a cikinta. Nan take ruwa ya fara bulowa daga rijiyar, duk sahabbai sun sami isasshen ruwan da zai ishe su da dabbobinsu.

Ruwa ya fitowa daga yatsun Annabi (SAW).

Wata mu'ujiza kuma a Hudabiya, Jabir (رضي الله عنه) ya ruwaito. Ya ce mutane suna jin ƙishirwa a Hudabiya kuma Annabi (SAW) ne kaɗai ya sami ruwa a cikin bokiti.

Lokacin da ya fara alwala sai mutane s**a kalle shi da tsananin sha'awar ruwan. Ganin sun zuba ido, sai Annabi (SAW) ya tambayi abin da ke faruwa? Da s**a ba shi labarin cewa ba su da ruwan alwala ko kashe kishirwa, sai Annabi (SAW) ya sa hannunsa a cikin wannan bokitin, sai ruwa ya fara fitowa daga yatsunsa Mai Albarka.

Jabir (رضي الله عنه) yana cewa a lokacin duk sun sami isasshen ruwan alwala da sha. Da wani ya tambayi Jabir (رضي الله عنه) ku nawa ne, sai ya ce: “ruwan zai iya isarmu ko da mun kai dubu dari. Duk da haka, mun kai Dubu Daya Da Dari Biyar a Wurin rijiyar.

A Yanzu An rufe rijiyar A Kusa wani wurin masana'antu kusa da Masjid al-Hudaibiah.

Na Samo Daga Tarihin Makkah Mukarramah Na Dr. Muhammad Ilyas Abdul Ghani, Na Fassara.

Duniyar Musulinci ba zasu taɓa mantawa da Jarumtar Yakubu Muhammad Fannami ba.A rana mai kamar ta Yau 25 Ga Watan Junair...
25/01/2024

Duniyar Musulinci ba zasu taɓa mantawa da Jarumtar Yakubu Muhammad Fannami ba.

A rana mai kamar ta Yau 25 Ga Watan Junairu 2017. Wannan Yaron ɗan Aji 1 wato SS1 A makantar ( Darussalam Science and Islamic Academy ) Yakubu Muhammad Fannami Ya ceci rayukan Jama'a masu yawa a wani Masallaci dake Kaleri A Jihar Borno.

Inda yayi kukan Kura ya tunkari wata Ƴar ƙunan Baƙin-wake da ta tunkari masallacin sanda Mutane suke tsaka da Ibada, Inda Bom ɗin da yake jikanta ya tarwatse tare dashi, Ya ceci Rayuwar waɗanda Suke Cikin Masallacin.

Alkalai sun yarda da hukuncin karamar kotu kan rajistar Abba Kabir Yusuf a NNPP, ta ce Abba bai cancanta ya tsaya takara...
17/11/2023

Alkalai sun yarda da hukuncin karamar kotu kan rajistar Abba Kabir Yusuf a NNPP, ta ce Abba bai cancanta ya tsaya takara ba - Karanta cikakken rahoton a sashen sharhi

Hoto: Abba Kabir Yusuf (Facebook)

mai Girma Gwamana Jahar Kano Abba Kabir Yusuf Yayi Sanar Wa Ta Musamman  Game Da Alummar Sa Dasu Kwantar Da Hankalin Su....
17/11/2023

mai Girma Gwamana Jahar Kano Abba Kabir Yusuf Yayi Sanar Wa Ta Musamman Game Da Alummar Sa Dasu Kwantar Da Hankalin Su.

Allah Mu Gode Maka Mun Kara Gode Maka Bisa Wannan Nima Daka Bamu Nayin Wannan Ibada Na Jumaah.Ya Allah Yakarbi Ibadummu Ya Allah Yasa Damu Da Wannan Alkairin Rana Jumaah'ah

Daman Rayuwa Haka Take Dole Sai Kahadu
Da Jarrabawa Inama A Gidan Ka Inma A
Wajan Aikin Ka. Inma A Wajan Kasuwancin Ka. Inma A Siyasar Ka. Haka Allah Yake Lamuran Sa Ba Mai Iya Chanzawa Kaddarar Sa.Sai Dai Kadage Da Addu'ah Kawai Allah Ubangiji Yasa Kaci Jarabawar Lafiya. Ya Allah Yasa Muci Jarabawar Mu Cikin Sauki

Allah Sarki Munci Zabe Amma Wasu Nema Suke Su Kwace Mana Kai Nigeria Wannan Wane Irin Hali Ne Dan Allah. Talakawa Sun Zabe Mu Sunce Muna Suke So Amma Neman Kuke Ku Kwace Musu Abin Dasu Ka Zaba. Ga Gaskiya Amma Neman Kwacewa Kuke. Haba Dan Allah Wannan Aiki Son Kai Ne Da Kuma Son Zuciya.Kullum Ana Talaka Zai Ji Dadi Amma Kullum Cikin Wahala Yake Sha. Mun Fara Kyara Kano Tafarawa Dawowa Dai-dai Amma Neman Kwace Mulkin Mu Kuke. To Kusani Allah Baya Barin Azzalumai Abayan Kasa.

Dan Allah Ma Goya Bayan NNPP Ku Kwantar Da Hankalin Ku Waje Guda Dan Allah. Kar Kusa Wani Abu Aran Ku Kunji Daman Rayuwa Dole Sai Kahadu Da Jarabawa A Rayuwar Sa. Muma Gashi Muna Haduwa Da Kalubale Na Siyasa. Muna Ma Talakawa Aiki Amma Wasu Basa So. Alfarma Annabi Muhammad Sai Makiyan Mu Sunji Kunya A Gaban Mu Insha Allah. Kanawa Ni Abba Kabir Yusuf Insha Allah Har Nagama Shekara Takwas Din Da Zanyi Insha Allah Kowa Sai Yayi Alfahari Dani A Mulki Na.Aiki Ne Babu Fashi Yanzu Muka Fara Wallahi.Duk Bakin Cikin Ku A Gare Mu. Allah Ubangiji Yana Tare Damu. Daman Mun San Ka None Bakwai So. Amma Abin Da Buku Sani Ba Allah Ubangiji Yana Tare Da Mai Gaskiya. Aikin Alkairi Shi Ne A Gaban Mu. Bawai Tara Kudi Ba.

AkY💥❤️

ALLAHÙ AKBAR: Ní Mutum Nè Kamar Kòwa, Bani Da Bambancí Da Talaka Ko Mai Kudi, Cuta Kuma Daga Allah Take, Shi Ke Kashèwa ...
11/11/2023

ALLAHÙ AKBAR: Ní Mutum Nè Kamar Kòwa, Bani Da Bambancí Da Talaka Ko Mai Kudi, Cuta Kuma Daga Allah Take, Shi Ke Kashèwa Kuma Shi Ke Ràyawa, Zan Iya Mutùwa Kuma Zan Iya Rayuwa, Zan Iya Mùtuwa Yau, Zan Iya Mutùwa Gobe.

Zan Iya Mùtuwa Mako Mai Zuwa, Zan Iya Mutùwa Wata Mai Zuwa Ko Shekara Mai Zùwa, Kuma Watakila Zan Iya Rayuwa Har Tsawon Shekaru 90 Allah Ne Kadaí Masani.

- Inji Marigayi Umar Musa Yar’adua.

Allah Ya Jikan Sa Da Rahama…..

Sayyidil mursalina annabi MUHAMMADU s a w❤
11/11/2023

Sayyidil mursalina annabi MUHAMMADU s a w❤

Wannan Matar Kurma ce, tace 'yar Karamar Hukumar Kusada ce Jihar Katsina, Rundunar Hizbah ta jihar Kano ta sameta a t**i...
27/10/2023

Wannan Matar Kurma ce, tace 'yar Karamar Hukumar Kusada ce Jihar Katsina, Rundunar Hizbah ta jihar Kano ta sameta a t**i tana yawo Tareda wannan Yarinyar da kuke gani, basusan inda zasu je ba, Wanda ya santa ko yasan Wanda ya santa ya tuntubemu a wadannan Lambobin.

08060463638
07065119082

YAKU AHLI SUNNAH NA GASKIYA DA GASKIYA  KUZAMO NA DABAN A KOYINKU DA MANZON ALLAH S.A.W A AIKACEIdan wani ya cuce ka  to...
24/09/2023

YAKU AHLI SUNNAH NA GASKIYA DA GASKIYA KUZAMO NA DABAN A KOYINKU DA MANZON ALLAH S.A.W A AIKACE

Idan wani ya cuce ka to katuna da yadda mutanen Da'ifa s**a cutar da Manzon Allah S.A.W yayi hakuri kaima sai kayi koyi da shi kayi hakuri.

Idan aka zageka ka tuna da zagin da Matar Aba Lahab ta dinga yiwa Manzon Allah S.A.W yayi hakuri kaima sai kayi hakuri.

Idan kaga mabukaci ka tuna da yadda Annabi S.A.W yake tallafawa mabukata. kaima sai kayi koyi dashi wajen tallafi.

Idan zaka fadi magana. katuna da yadda Annabi S.A.W yake fadin gaskiya. kaima sai kayi koyi da shi ka fadi gaskiya akan masoyi da makiyi.

Idan zakayi wa'azi ko nasiha katuna da yadda Annabi S.A.W yake kamewa daga zagi ko cin fuskar abin kira kaima sai kayi koyi dashi ka tausasa lafazi.

Idan zakayi ko wacce irin mu'amala da kowa katuna da irin gaskiya da amanar Manzon Allah S.A.W cikin mu'amala sai ka kwatanta koyi da shi.

Idan kaga wani na aikata aiki mummuna kada ka la'anceshi ko ka aibatashi. kayi kokari wajen jawoshi zuwa dai-dai cikin hikima ta hanyar koyi da Manzon Allah S.A.W

Idan zakayi zumunci ka tuna da yadda Annabi S.A.W. ke sadar da zumunci da kowa kaima sai kayi koyi da shi.

ALLAH YA BAMU IKON KYAUTATA KOYI DA MANZON ALLAH S. A. W.

Yusuf kansusi Niass ✍️

Barka da sauka ainil muradiBarka da sauka saifullahi Barka da sauka babullahi Barka da sauka jindullahiBarka da sauka as...
22/09/2023

Barka da sauka ainil muradi
Barka da sauka saifullahi
Barka da sauka babullahi
Barka da sauka jindullahi
Barka da sauka asadulahi
Barka da sauka aminullahi
Barka da sauka siradallahi
Barka da sauka imamullahi
Barka da sauka ruhullahi
Barka da sauka abdullahi
Barka da sauka khairullahi
Barka da sauka khashiful gummati
Barka da sauka Sayyidil Sarah
Barka da sauka Sayyidil mursalina
Barka da sauka Sayyidil auwalina
Barka da sauka Sayyidil alamina
Barka da sauka Sayyidil anbi'i
Barka da sauka Sayyidil ahkirana
Barka da sauka Sayyidina rasulullahi
Barka da sauka sayyidina Abdul hayyu
Barka da sauka Sayyidina abdullahi
Barka da sauka Sayyidina rasulul alamina
Barka da sauka Sayyidina Muhammad
Barka da sauka ya wanda yaga allah
Barka da sauka mai siffofin allah
Barka da sauka mai sulke
Barka da sauka mai kwalkwali
Barka da sauka mai kwagiri
Barka da sauka mai takubbai
Barka da sauka mai mashi
Barka da sauka mai doki
Barka da sauka mai jaki
Barka da sauka mai sojoji
Barka da sauka mai masuna
Barka da sauka mai taguwa
Barka da sauka sirrin allah
Barka da sauka bawan allah
Barka da sauka wakilin allah
Barka da sauka waliyin allah
Barka da sauka tagawar allah
Barka da sauka dangatan allah
Barka da sauka shalelen allah
Barka da sauka nagaban goshin allah
Barka da sauka mai ganin allah
Barka da sauka masoyin allah
Sayyiduna Muhammadur rasulullah (S@W) 🙇🙇🙇

23/03/2023

HAPPY RAMADAN KAREEM TO ALL THE MUSLIM IN THE WORLD 🇳🇬

19/03/2023

Allah Kasa Wannan Kalmar Ita Ce Ƙarshen Furucin mu!
𝘓𝘢 𝘪𝘭𝘢𝘩𝘢 𝘪𝘭𝘭𝘢𝘭𝘭𝘢𝘩𝘶 𝘔𝘶𝘩𝘢𝘮𝘮𝘢𝘥𝘶𝘳 𝘳𝘢𝘴𝘶𝘭𝘶𝘭𝘭𝘢𝘩ﷺ

Ɗan Sani Abacha ya rasuAbdullahi Abacha, wanda shi ne ɗa na biyun-ƙarshe ga  marigayi tsohon shugaban mulkin sojan Nijer...
04/03/2023

Ɗan Sani Abacha ya rasu

Abdullahi Abacha, wanda shi ne ɗa na biyun-ƙarshe ga marigayi tsohon shugaban mulkin sojan Nijeriya , Sani Abacha, ya rasu yana da shekaru 36 a duniya.

Iyalin Abacha sun tabbatar wa DAILY NIGERIAN rasuwar a yau Asabar, inda s**a ce Abdullahi ya rasu ne cikin barci a a gidansu da ke t**in Nelson Mandela a Abuja.

“A daren jiya fa lafiyar sa kalaunya kwanta, amma yau da safe sai gawarsa a ka samu. Ya rasu cikin kwanciyar hankali a cikin barcinsa,” in ji wata majiya daga iyalin Abacha.

DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa za'ayi Jana'izar sa da misalin karfe 4 na yamma a babban masallacin kasa dake Abuja a yau Asabar.

An haife shi a shekarar 1987, marigayin yana daya daga cikin yara tara da marigayi shugaban soji ya bari.

04/03/2023

MUHAMMADU RASULILLAH

28/02/2023

ALLAH KABAMU SHUGABA NAGARI 🇳🇬

ALBARKACIN NABIYYIR RAHAMATI S A W🇸🇦

21/02/2023

Yafi kowa Mutunci : Annabi Muhammadu

Sahara ayankin afirka Masana ❗❗❗
21/02/2023

Sahara ayankin afirka
Masana ❗❗❗

21/02/2023

ANNABI MUHAMMADU

SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM

18/02/2023

Shugaban Masu Gaskiya,
Jagoran Sada Zumunchi, Sarkin Adalchi.

Muhammad Rasulullah ﷺ

16/02/2023

Waye zaitayani Rubuta
Muhammadur Rasulillah

16/02/2023

Assalamualaikum

I need your pray plc

Assalamualaikum jama'a ❗❗❗Ina barar addu'arku
16/02/2023

Assalamualaikum jama'a ❗❗❗

Ina barar addu'arku

Hadin guywa 👌
11/02/2023

Hadin guywa 👌

11/02/2023

Zaka Iya Barin Komai Ka Rubuta 👏S❤️A❤️W👏

Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yariKotun shari'ar Muslunci da ke Filin Hoki a Kano ƙarƙashin mai Shari'a Abdulla...
02/02/2023

Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari

Kotun shari'ar Muslunci da ke Filin Hoki a Kano ƙarƙashin mai Shari'a Abdullahi Halliru ta aike da Ƴar TikTok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan yari.

Lauya Barrister Lamiɗo Abba Soron Ɗinki ya karanto mata ƙunshin tuhume-tuhumen da ake mata wanda ta musanta.

Ana zargin Murja da ɓata suna da barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris wanda dukanninsu abokananta ne.

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 16 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Sai dai Lauyan Murja Barrister Yasir Musa ya nemi a tura ta zuwa Hisbah maimakon gidan Yari sai dai Kotun bata amince ba.

SHEHU IBRAHIM INYAS 9Wata rana Shehu ya je ƙasar Misra zamanin Sarki Jamal Abdulnasir, sai aka ba shi dukiya mai tarin y...
02/02/2023

SHEHU IBRAHIM INYAS 9

Wata rana Shehu ya je ƙasar Misra zamanin Sarki Jamal Abdulnasir, sai aka ba shi dukiya mai tarin yawa saboda yanda suke girmama Malamai, sai wani mai karanta Ƙur'ani ya zo wajen da Shehu yake ya karanta Ƙur'ani, sai Shehu ya ɗauki kuɗin nan duka ya bashi su, makarancin Ƙur'ani kuma ya yi tafiyarsa da kuɗinsa zuwa gidansa, bayan ya je gidan sai ya buɗe kuɗin nan ya ga dukiya mai tarin yawa sai kawai ya dawo zuwa ga Shehu sai yace "Shehu wannan ai hadiyya ce irin ta ku bata dace da mu ba, ta irinku ce, kuma hadiyya ce daga hukuma zuwa gare ku" sai Shehu yace masa "Wannan hadiyya daga Allah take zuwa gare ka saboda girmama Ƙur'ani" sai makarancin Ƙur'anin nan ya tafi da hadiyyar nan yana mamakin irin wannan karramawa ta Shehu akansa.

Haka Shehu yake, ba abinda ya dame shi da duniya b***e abinda ke cikinta.
Yana girtmama Ƙur'ani da abinda ya shafi Annabi, indai ka zo ka karanta Ƙur'ani ko ka nuna soyayya ga Annabi to nan da nan zai baka kan shi baki ɗaya.

Allah Ka ƙara wa Shehu karama
Ameeeeeen.

© Mustapha Ibrahim malumfashi
Daga Taskar tijjaniyya

SAYYADINA ALIYU (R.T.A) YANA CEWA:من أراد زاد فاالتفوى تكفيهDuk wanda ke son guzuri, to tsoron Allah ya ishe shi.ومن أرا...
02/02/2023

SAYYADINA ALIYU (R.T.A) YANA CEWA:
من أراد زاد فاالتفوى تكفيه
Duk wanda ke son guzuri, to tsoron Allah ya ishe shi.
ومن أراد عزا فالإسلام يكفيه
Duk wanda ke son izza, to Muslunci ya ishe shi.
ومن أراد عدلا فحكم الله يكفيه
Duk wanda ke son adalci, to hukuncin Allah ya ishe shi.
ومن أراد جليسا فالقرءان يكفيه
Wanda yake son abokin zama, to Alkur'ani ya ishe shi.
ومن أراد زينة فالعلم يكفيه
Duk wanda yake son ado, to ilimi ya ishe shi.
ومن أراد واعظا فالموت تكفيه
Duk wanda yake son wa'azi to mutuwa ta ishe shi.
ومن أراد أنيسا فذكرالله يكفيه
Duk wanda yake son debe kewa, to zikirin Allah ya ishe shi.
ومن أراد غنى فاالقناعة تكفيه
Duk wanda yake son wadata, to wadatar zuci ta ishe shi.
من أراد جمالا فالأخلاق يكفيه
Duk wanda yake son kyau, to kyawawan dabi'u sun ishe shi.
ومن أراد راخة فالآخرة تكفيه
Duk wanda yake son hutu, to lahira ta ishe shi.
ومن لم يكفه كل هذا فالنار تكفيه
Duk wanda wadannan Abubuwan basu ishe shi ba, to wuta zata ishe shi.
Wannan sakon tana zuwa muku ne daga taskar Umar Chobbe
Happy Maulid Of Sayyadina Aliyu (A.S)
Ya Allah ka bamu ikon kiyayewa Albarkan ANNABI S.A.W

SHEHU IBRAHIM INYAS 6Shehu yana umurtar mu da wasu abubuwa muhimmai wadanda za su taimake mu duniya da lahira. Yana gaya...
02/02/2023

SHEHU IBRAHIM INYAS 6

Shehu yana umurtar mu da wasu abubuwa muhimmai wadanda za su taimake mu duniya da lahira.
Yana gaya mana cewa

من أراد أن يكون معي فى حالي فليمسك طريقى فى الأقوال والأفعال بامتثال الأوامر واجتناب النواهى فى الظاهر والباطن والتعطش والتشوق إلى الوصول إلى مرضاة الله ورسوله

Wanda yake so ya kasance tare da ni a hali na to ya yi riƙo da Ɗariqa {Tijjaniyya} a cikin zance da aikinsa, ya misaltu da abinda aka yi masa umurni, da nesantar abinda aka hana shi a zahiri da baɗininsa, da so da shauƙi zuwa ga saduwa da yardar Allah da Manzonsa.

Mun gode shehu

Allah ya ƙara karamar Barzakhu
Ameeeeeeeeen

📝 Mustapha Ibrahim malumfashi

MANZON ALLAH (S.A.W) YANA CEWA:-DukkanMala'ikun Dake Cikin Al'arshi Sun Kasance SunaLa'antar (tsinuwa) Mutane Guda Takwa...
02/02/2023

MANZON ALLAH (S.A.W) YANA CEWA:-Dukkan
Mala'ikun Dake Cikin Al'arshi Sun Kasance Suna

La'antar (tsinuwa) Mutane Guda Takwas (8):-
(1).Masu Yin Luwadi (guys) (2).Mata Masu Yin
Madigo (le***an) (3).Masu Yanka Dabba Tare Da
Ambaton Wanin Wanda Ba Allah Ba. (4).Wanda
Ke Yin Zina Da Dabbobi. (5).Wanda Yayi Jima'i
Da Uwar Matarsa (koda ta hanyar aure ne).
(6).Wanda Bashi Da Ladabi Baya Jin Kunyar
Kowa Kuma Baya Girmama Kowa. (7).Wanda Ke
Canza Iyakokin Kasa Saboda Zalunci. (8).Bawa
Ko Ma'aikaci Wanda Ya Hada Kai Da Wani
Domin Su CucI Mai Gidansa Ko Ma'aikatarsa
Inda Yake Aiki.

YA ALLAH KA KAREMU DA
ZURIYAMU DAGA AFKAWA CIKIN WANNAN
BALA'IN AMEEN.

📝...Muhammad A baraya Akko
Daga Taskar tijjaniyya
29/1/2023

Address

Kiyawa

Telephone

+2348133628014

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Hausa Media News TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa Hausa Media News TV:

Videos

Share


Other Media/News Companies in Kiyawa

Show All