27/07/2024
KU CI GABA DA NEMAN ILIMI DA KOYON SKILLS: Kar ka yarda ka rude
Wannan shawara ce ga irin mu wadanda ba 'ya'yan kowa ba.
Duk yadda Nigeria ta rikice, kar ka yarda ka rude ka dena karatu, neman ilimi ko koyon skills.
Har yanzu a Nigeria akwai Jobs da ake daukar mutane da salary din yafi 700k every months, kuma ba sai ka san kowa ba, kawai skills naka da experience naka zasu sa daukeka.
Kuma babban abunda kake bukata ba kome bane illa abubuwa kamar haka:
- Takardar shedar kammala karatu kowace iri, kowane irin degree kayi kar ka damu, kai dai yakasance kana da takardar karatu.
- Basics Computer skills, kana bukatar ilimin computer, at least ka iya office work da computer, musamman ka iya aiki da MS Word, Excel, PowerPoint da kuma Browsing, programming.
- Working Experience, duk yadda Nigeria ta rikice, kayi iya kokarin ka, ka dinga yin wani abu da zai kara maka experience na rayuwa, ta yadda idan ka zo interview kana da abunda zaka fada a rayuwarka a working experienceda ka samu, bawai ka zauna jiran sai aiki yazo ba, ba mai baka aiki ba kada working experience awanan lokacin.
Me kake jira ? Ka tashi tsaye, ka ci gaba da karatu, da koyon skills, duk yadda Nigeria ta rikice, there is still hope for those with skills and experience, kar ka yadda ka rude.
Stay blessed.
Ahmad Aminu Ahmad esq.