Jakadiya RTV

Jakadiya RTV Jakadiya Radio and Television is a registered internet radio and television with Corporate Affairs Commission.
(1)

Our aims is to ensure credibility of news circulating on our social network platform to help the fight against fake news.

An mika ma Al'ummar Kauyen Kwarago cikin mazabar Galadima (B) dake cikin karamar hukumar Kankia masallacin Juma'a sabo f...
16/01/2025

An mika ma Al'ummar Kauyen Kwarago cikin mazabar Galadima (B) dake cikin karamar hukumar Kankia masallacin Juma'a sabo fil da Ministan gidaje da tsara birane Arc. Ahmed Musa Dangiwa ya gina masu da kudin aljihun sa, domin bunkasa addinin musulunci.

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kankia Hon.Salisu Hamza Rimaye ya Jagoranci mika masallacin tare da Dan takarar shugaban karamar hukumar Kankia Hon. Lawal Gezi Kankia ga Al'ummar Kauyen na Kwarago bayan kammala gininsa.

A jawabin da Dan majalisar ya gabatar yayin da ake mika ma Al'ummar Kauyen na kwarago masallacin, kira ya yi ga Al'ummar da su kula da wannan masallaci ta hanyar tsabtaceshi koda yaushe domin gabatar da ibada cikin shi cikin natsuwa, domin sanin kowane masallaci dakin Allah ne.

Al'ummar Kauyen na Kwarago sunyi tare da fatan alheri ga ministan gidaje da raya birane na Najeriya Arc. Ahmed Musa Dangiwa, akan gina masu wurin ibada da ya yi, Allah ya saka ma shi da alheri ya kuma sanya ladar ga mizani.

16/01/2025

Ƙungiyar Dillalan Man Fetur Ta Ƙasa, IPMAN, Reshen Jihar Katsina, Ta Yi Sabbin Shugabanni

16/01/2025
16/01/2025

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un! Allah ya yi wa Babban Ɗanjarida a Katsina, Lawal Sa'idu Funtua rasuwa

Allah ya jiƙansa da Rahama.

Comrade. Al'amin Rabi'u Mani ya kasance mutum na farkon da ya fara sayen tikitin shedar tsayawa takarar shugabancin kung...
15/01/2025

Comrade. Al'amin Rabi'u Mani ya kasance mutum na farkon da ya fara sayen tikitin shedar tsayawa takarar shugabancin kungiyar matasa ta kasa reshen jihar katsina (NYCN)

A ranar talatan nan kwamitin da zai gudanar da zaben ƙungiyar matasa (NYCN) s**a fara sayar da tikitin shedar tsayawa takarar shugabancin kungiyar inda comrd. Al'amin Rabi'u Mani ya karbi shedar tsayawa takarar domin neman shugabancin kungiyar k**ar yadda doka ta tanadar.

14/01/2025

Da Hon. Sada Soli Jibia Ya ji koken mu da bai zamo cikin wasu komabayan yan majalisa a fannin kawo cigaba mai dorewa ba- Hon Aminu Buhari Kaita

13/01/2025

Duk ranar da Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero ya fito mutane miliyan 1 ne ke binsa ba tare da an ba su ko sisi ba, tsabar soyayya ce kawai, don haka ba fargaba ba ce ta sa muka ɗaukaka ƙara -Inji Sarkin Dawaki, Aminu Babba Dan-angundi

Shugaba Tinubu ya haramta luwaɗi da maɗigo da daudu ga rundunar tsaron NajeriyaShugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ra...
12/01/2025

Shugaba Tinubu ya haramta luwaɗi da maɗigo da daudu ga rundunar tsaron Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan dokar hana luwadi, madigo,
da daudanci tsakanin jami’an sojin Najeriya.

Sabuwar dokar da shugaban ya amince da ita ta kara da haramta wa jami'an tsaron sha ko ta'ammuli da ababen sanya maye a lokacin da suke bakin aiki, kana ta gargade su da su nisanci aiyukan gwalangwaso, da sauya wani bangare na halittar su ta fil-azal, ko yin zanen jiki da ake kira da tatoo a turance.

Wannan dokar na kunshe ne a Sashe na 26 na dokokin aikin Rundunar Sojojin kasar wanda Shugaba Tinubu ya yi wa gyaran fuska a ranar 16 ga Disamba, 2024.

“Neman jinsi ɗaya da sauya halittar Allah ya saba wa dokokin mu da al'adunmu, don haka ba za mu lamunci hakan a rundunar jami'an tsaron kasar mu ba" Inji Shugaba Tinubu.

Shugaban ya ci gaba da cewa:

"Ba zai halatta ga jami'i ko jami'ar tsaron ƙasar mu ya yi ko wace irin hulɗa ta sauya jinsi, ko neman jinsi ɗaya ko ko shiga cikin ayyukan masu wannan ɗabi'a ko kungiyarsu ta duniya da aka fi sani da (LGBTQIA2S+) ko Daudu ba.

“Bai halatta a sami jami’in tsaro a hulɗar rashin ɗa'a da ilahirin jiki ko wani bangarensa ba"
Duk in ji Shugaba Tinubu.

Abinda ake jira a gani shine sabbin hukumce hukumcen ladabtarwar da dokar za ta fitar da zaran an k**a wani jami'in tsaro da laifin karya ta.

11/01/2025

Wani masani ɗan ƙasar Denmark ya ce mutane dubu 71 sun mutu a Najeriya sanadiyyar tarin TB

Ƙarin bayani👇🏻

11/01/2025

Muna gode wa Allah da bai bari mun yi zaɓen timun dare ba, ya zaɓar mana Malam Dikko Umar Raɗɗa a matsayin gwamnan Katsina - Hon. Alh. Yusuf Aliyu Musawa, tsohon ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban gidauniyar Gwagware Foundation

Shirin Kwalliya Ta Biya Kuɗin Sabulu, wanda Hon. Nasir Almustapha Ɗanye Jibia, shugaban APC na ƙaramar hukumar Jibia ke ɗaukar nauyi

YAS GLOBAL PRODUCTION Sun gwangwaje Sunusi Anu Sabuwar Unguwa da lambar girmamawa saboda wakarsa ta GAJERAR MACE.
10/01/2025

YAS GLOBAL PRODUCTION
Sun gwangwaje Sunusi Anu Sabuwar Unguwa da lambar girmamawa saboda wakarsa ta GAJERAR MACE.

10/01/2025

Kotun daukaka ƙara ta ce Kotun Tarayya ba ta da hurumin shiga dambarwar masarautar Kano

Yanzu yaya kenan?

Assalam Jama'a wannan yaro da kuke gani, yace sunan shi UMAR, an tsince shi yau sama da kwana Ashirin ake cigiyar Iyayen...
10/01/2025

Assalam Jama'a wannan yaro da kuke gani, yace sunan shi UMAR, an tsince shi yau sama da kwana Ashirin ake cigiyar Iyayen shi ko wani wanda Allah Ya sa ya sanshi, da cewa su garzayo zuwa Gidan Talabijin na Jihar Katsina KTTV, a tuntubi Yasir Abubakar domin karin bayani, 08064500854, Allah Ya sa a dace Amin, sai mu taimaka wajen Yada wannan sako har Allah Ya sa a dace. Mun gode

09/01/2025

Tambaya

09/01/2025

Bai k**ata ƴan Majalisar dokokin jihar Katsina su bari a yi wnnan aika-aikar ba - Inji Comrade Nura Abbas Katsina

Comrade ɗin ya kuma ba gwamna Dikko Raɗɗa shawara game batun shiga hakokin harajin ƙananan hukumomin jihar shawara

Taimakon Marayu Da Marasa Karfi A Cikin Al'umma Wani Babban Jari Ne Ga Mai Yin Shi - In Ji Shugaban Ma'aikatan Gidan Gwa...
09/01/2025

Taimakon Marayu Da Marasa Karfi A Cikin Al'umma Wani Babban Jari Ne Ga Mai Yin Shi - In Ji Shugaban Ma'aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Katsina

Daga Murtala Sani Malumfashi

Daya daga cikin manyan alamomin shugaba na gari ita ce kasancewa mai tausayi da taimakon al'ummar sa, musamman ma masu rauni da marasa karfi a cikinsu.

Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir, ya samu kyakkyawar shaida a kan irin wadannan ayyuka na jin kai a jihar.

Wannan kyakkyawar shaida kuwa ta fito ne daga bakunan wasu manyan malaman addinin musulunci a cibiyar kula da marayu ta gidauniyar 'Atta'awanu Islamic Foundation' dake Dandagoro a yankin karamar hukumar Batagarawa, inda shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin ya kai ziyara a ranar Talata.

Shugaban cibiyar, Alhaji Kabir Abbas Kankia, wanda ya ce a halin yanzu suna da yara marayu da matan da mazajensu s**a rasu kimanin 257, ya bayyana Abdulkadir Mamman Nasir a matsayin daya daga cikin mutanen dake kan gaba wajen bayar da dimbin gudummuwa wajen tallafa wa cibiyar.

Wasu daga cikin wadanda s**a assasa gidauniyar ta tallafa wa addinin musulunci da kafuwar cibiyar, Sheikh Dr. Ahmad Musa Filin Samji da Alhaji Yusuf Danbaba, sun yaba da yadda al'umma ke bai wa cibiyar gudummuwa a kullu yaumin tare da yin kira ga sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da mutane irin su Abdulkadir Nasir wajen tallafa wa marayu da marasa karfi da ci gaban addinin Islama domin samun babban rabo a duniya da lahira.

Sun kuma yi karin haske a kan yadda ake amfani da tallafin kudaden da ake samu wajen ciyar da yaran da ilmantar da su da tufatar da su gamida kokarin da ake na fadada cibiyar domin ta zamo mai bayar da horon sana'o'i ga yaran da shiga harkar noma da sauran ababen da zasu samar wa cibiyar karin hanyoyin samun kudaden shiga.

Shi ma shugaban kungiyar Izala na jihar Katsina, Sheikh Yakubu Musa Hassan, ya yi dan takaitaccen jawabi inda ya yi addu'ar Allah ya taya Honarabul Abdulkadir Mamman Nasir rikon sabon mukamin da ya samu, ya kuma daukaka marayun su zamo masu amfani ga al'umma da kasa baki daya.

A jawabinsa na babban bako, sabon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Katsinan, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir, ya shirya taron walimar a gidan marayun ne domin nuna godiya ga Allah bisa mukamin da ya samu tareda neman tubarraki da addu'o'in marayun wajen smun sauke nauyin da aka dora masa cikin nasara.

Honarabul Abdulkadir Nasir wanda ya bayyana tallafa wa marayu a matsayin wani babban tarkon lada, ya ce ya zabi taimakon marayun ne domin koyi da fadar Allah da manzonsa dake cewa duk wanda ke tallafa wa maraya, yana da babban rabo a ranar tashin kiyama.

Don haka ya ce ba zai taba yanke alaka da marayu ba har karshen rayuwarsa, yana mai alakanta dimbin nasarorin da yake samu tun a nan duniya da irin wadannan ayyuka na jin kai da yake yi, wadanda ya ce sun fi masa saka jari inda zai samu ribar kudade kadai.

Shugabannin cibiyar da marayunta sun mika kyaututtuka da s**a hada da kwafen Alqu'ani mai girma da lambobin yabo ga Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir da uwar gidansa, Hajiya Maijidda domin nuna gamsuwa da jin dadi a kan irin gaggarumar gudummuwar da suke bayarwa wajen tafiyar da gidan marayun da daukaka addinin musulunci.

An kuma gabatar da addu'o'i na musamman na neman Allah ya taimaki gwamnatin Dikko Radda da shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin a kokarin da suke na inganta rayuwar marayu da talakawa da al'ummar jihar baki daya.

Najeriya Ta yi Nasarar Haƙo Gangar Mai Milyan Daya Da Rabi A Karon Farko Cikin Shekaru HuduNajeriya ta yi nasarar cimma ...
07/01/2025

Najeriya Ta yi Nasarar Haƙo Gangar Mai Milyan Daya Da Rabi A Karon Farko Cikin Shekaru Hudu

Najeriya ta yi nasarar cimma burinta na cike gibin da take samu wajen hako mai wanda Kungiyar ƙasashe masu albarkatun mai OPEC ta kayyade mata na haƙo ganga miliyan 1.5 a kowace rana.

Wannan shine
karon farko cikin shekaru hudu da Najeriya ta sami irin wannan gagarumar nasara tun bayan dawowar matsalar masu fasa bututun mai da gwamtocin baya s**a fuskanta

Wasu alkaluman binciken Bloomberg sun nuna cewa yawan man da Najeriya ke haƙowa ya ƙaru da ganga 40,000 zuwa miliyan 1.51 a watan Disambar bara.

A baya dai ƙungiyar OPEC ta ware wa Najeriya damar haƙo ganga Milyan 1.8 a kowace rana, sai dai ƙungiyar ta rage wannan adadi zuwa milyan 1.5 sak**akon gazawar Najeriya na cike giɓin da take samu wajen haƙar man ta dalilin matsalolinta na cikin gida, hakan ya janyo wa kasar koma-baya a bangaren tattalin arzikin sak**akon raguwar kudaden shiga da masu zuba jari.

Sai dai jim kadan da darewar Shugaba Tinubu karagar mulkin kasar, ya lashi takobin dawo da Najeriya gurbinta ta hanyar magance matsalolin tsaron yankin da ke da arzikin man dama Najeriya baki daya.

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya danganta wannan nasarar da kokarin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi na ganin an kara yawan albarkatun man fetur da s**a hada da jawo jarin kasashen waje da kuma tabbatar da zaman lafiyar al’ummomin da ke zaune a yankunan haƙar mai.

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jakadiya RTV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share

Jakadiya Radio and Television

Domin Samun Sahihan Labarai, da Shirye-shirye managarta.