Zamani Media Crew

Zamani Media Crew News
Reports
Enlightenment
Entertainment
Photos Videos Editing
Adverts
Documentary
Film Making etc Some Information

Shugaban kasa Tinubu na son majalisar dokoki ta gaggauta amince masa da sabuwar tsarin dokar haraji don fara aiwatar da ...
17/01/2025

Shugaban kasa Tinubu na son majalisar dokoki ta gaggauta amince masa da sabuwar tsarin dokar haraji don fara aiwatar da ita

Ashe a baibai aka baiwa ƴan Arewa bayanan dokar haraji, sai yanzu muka gane gaskiya - Gwamnan Nassarawa Abdullahi Sule, ...
17/01/2025

Ashe a baibai aka baiwa ƴan Arewa bayanan dokar haraji, sai yanzu muka gane gaskiya - Gwamnan Nassarawa

Abdullahi Sule, gwamnan jihar Nasarawa, ya ce an yaudari ƴan Arewa da cewa kudirin sake fasalin haraji zai haifar da karin nauyin kudi da matsin tattalin arziki a ƙasar.

Kalaman Sule na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta goyi bayan kudurin dokar harajin da ke gaban majalisar dokokin kasar.

Da ya ke magana a wani shiri a gidan Talabijin na Channels a jiya Alhamis, Sule ya ce NGF ta amince da sake fasalin haraji da nufin kawar da wasu kura-kurai da kuma samar da tsarin biyan haraji mai sauki ga talakawa.

Sule ya kuma kawar da ra’ayin da ke nuna cewa an samu baraka tsakanin gwamnonin Arewa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

“Yawancin mutanen arewa an sayar musu da ra’ayin cewa za a kara haraji. A yau, ta wannan yarjejeniya, babu ƙarin haraji," in ji shi.

Likita mai ɗan karen basira da ƙoƙarin tsiya, Dr Murtala Ɗandashere da yan bindiga s**a harbar wa ƙafa a asibitin Genera...
17/01/2025

Likita mai ɗan karen basira da ƙoƙarin tsiya, Dr Murtala Ɗandashere da yan bindiga s**a harbar wa ƙafa a asibitin General ta Kankara da yake aiki a can, yana samun sauƙi

Yan bindiga sun shiga asibitin a daran Talata inda s**ai harbe-harbe, tare da garkuwa da wasu, sai dai a harin babu wanda s**a kashe

A shekarar da Ɗandashere ya kammala ABU a 2019, inda ya karanci Medicine, shi ne zakara gaba ɗaya Jami'ar a waɗannan kwasa-kwasan

1. Physiology
2. Histopathology
3. Biochemistry
4. Surgery
5. Chemical Pathology
6. Haematology
7. Pharmacology
8. Community Medicine Project
9. Pathology
10. Community Medicine
11. Anatomy
12. Medical Microbiology
13. Surgery

Ya sami kyaututtuka na lambar yabo saboda kwazonsa kusan 20, tare da samun tallafin karatu zuwa kasar waje

Allah Ya ba shi lafiya Ya yi mana tsari da miyagun mutane a duk inda suke

Matasanmu ku fito ku nema kar a bar mu a bayaTinubu ya ya aminta da a ɗauki sabbin ma'aikatan gyaran hali har su dubu bi...
17/01/2025

Matasanmu ku fito ku nema kar a bar mu a baya

Tinubu ya ya aminta da a ɗauki sabbin ma'aikatan gyaran hali har su dubu biyar a duk fadin ƙasar nan

Mukaddashin shugaban hukumar gidajen gyaran hali na Nijeriya Nwakuche Ndidi, shi ne ya bayyana wa majalisar wakilai haka

Ya ce shugaban kasar ya aminta da ɗauka sabbin ma'aikata 5,000 tun a watan Augustan 2024, amma saboda rashin isassun kuɗi ga hukumar ta jingine batun ɗauka

Ya bayyana cewa a kasafin kuɗin 2025 din nan da zarar an saki kudin hukumar CDCFIB z ta gudanar da ɗaukar sabbin ma'aikatan gidajen gyaran halin

Ku yi murna al'ummar jihar Katsina ci gaba da sauƙi ya zo maku har cikin gidaAn ƙaddamar da fara amfani da sabbin ƴar ƙu...
17/01/2025

Ku yi murna al'ummar jihar Katsina ci gaba da sauƙi ya zo maku har cikin gida

An ƙaddamar da fara amfani da sabbin ƴar ƙurƙura masu amfani da hasken rana Sola ba ruwanka da man fetur ko gas

Gwamna Dikko Radda ne ya ƙaddamar da motocin na ƙurƙura guda biyar, don fara jigilar al'ummar jihar Katsina cikin farashi mai rahusa

Sheikh Abdur Rahman As Sudais ne zai ja sallar Juma'a ta gobe, 17 ga watan Janairu, 2025 a Masallacin Harami na Makkah.S...
16/01/2025

Sheikh Abdur Rahman As Sudais ne zai ja sallar Juma'a ta gobe, 17 ga watan Janairu, 2025 a Masallacin Harami na Makkah.

Shafin X na Inside the Haramain ne ya rawaito.

Mai martaba sarkin Katsina Alh. Dr.  Abdulmuminu Kabir Usman zai dawo Masarautar shi a Ranar Lahadi  Mai zuwa  19/1/2025...
16/01/2025

Mai martaba sarkin Katsina Alh. Dr. Abdulmuminu Kabir Usman zai dawo Masarautar shi a Ranar Lahadi Mai zuwa 19/1/2025

Za a je tarbo dawowar Sarkin a filin jirgin sama na Kano a ranar ta Lahadi 19 January 2025. Indai zaizo yacigaba da tafiyar da masarautarahi kamar yadda yasaba.

Rikicin Siyasa : Kotu Ta Tsige Shugaban PDP Da Ke Biyayya Ga Wike A Jihar Rivers Wata Babbar Kotun Jihar Rivers da ke za...
16/01/2025

Rikicin Siyasa : Kotu Ta Tsige Shugaban PDP Da Ke Biyayya Ga Wike A Jihar Rivers



Wata Babbar Kotun Jihar Rivers da ke zamanta a Fatakwal ta tsige shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Hon. Chukwuemeka Aaron.



Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Stephen Jumbo, ita ce ta soke zabukan mazabu kananan hukumomi da jam’iyyar PDP ta gudanar a jihar a watan Yuli 2024.



Wannan matakin ya zo kasa da wata daya bayan wata Babbar Kotun ta soke zabukan mazabu, kananan hukumomi da na jiha da jam’iyyar adawa ta APC ta gudanar a jihar, wanda ya samar da Cif Tony Okocha a matsayin shugaban jam’iyyar na jiha.



Hukuncin kotun ya biyo bayan takaddama kan sahihancin zabukan PDP da wani bangare na jam’iyyar da ke biyayya ga Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, s**a gudanar.

'Dan Majalisar Tarayya Hon Abdulmumin Jibrin Kofa (Jarman Bebeji), ɗan Majalisar Wakilai na mazaɓar Kiru/Bebeji, Dake Ji...
16/01/2025

'Dan Majalisar Tarayya Hon Abdulmumin Jibrin Kofa (Jarman Bebeji), ɗan Majalisar Wakilai na mazaɓar Kiru/Bebeji, Dake Jihar Kano ya kai ziyarar girmamawa ga tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan a gidansa da ke Maitama, Abuja.

📷Sani Ibrahim P**i
Hadimin ɗan majalisar kan yaɗa labarai:

FIRE OUTBREAK AT GOVERNMENT SCIENCE SECONDARY SCHOOL , BINDAWAWe regret to inform the general public that a devastating ...
15/01/2025

FIRE OUTBREAK AT GOVERNMENT SCIENCE SECONDARY SCHOOL , BINDAWA

We regret to inform the general public that a devastating fire outbreak (inferno) occurred at Government Science Secondary School, Bindawa, on Monday 13/01/2025 around 8:45am.

Fortunately, we are relieved to report that there was no loss of life in the incident. However, the fire resulted in significant damage to the school's hostel (Dan Yusufa House), with mattresses and other cosmetic items being completely destroyed.

The school administration responded promptly to the incident, and an investigation is currently underway to determine the cause of the fire.

Bala Duwa
Senior Master Academic
For Principal

Almajirai da ƴan jari-bola sun maka Ministan Abuja, Wike a kotuAlmajirai da ƴan jari-bola mazauna babban birnin tarayya ...
15/01/2025

Almajirai da ƴan jari-bola sun maka Ministan Abuja, Wike a kotu

Almajirai da ƴan jari-bola mazauna babban birnin tarayya Abuja da s**a hada har da kananan ƴan kasuwa, da sauransu, sun shigar da kara akan ministan Abuja, Nyesom Wike, inda su ka bukaci ya biya su diyyar Naira miliyan 500 bisa zargin sa da tauye ƴancin su na yan ƙasa.

Wani lauya mai suna Abba Hikima ne ya shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1749/3024 a gaban mai shari’a James Omotosho na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a madadin rukunin mutanen.

Hikima, wanda aka ambata a matsayin mai shigar da ƙara a cikin takardar ƙarar da aka fitar a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2024, amma aka shigar a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2024, ya ce ya kai kara ne domin al'umma domin kare ƴan kasa masu rauni a Najeriya.

Masu ƙarar, kamar yadda Daily Trust ta rawaito, na ya haɗa da Wike, Sufeto-Janar (IG) na 'yan sanda; Darakta-Janar, Sashen Sabis na Jiha (DSS) da Hukumar Tsaron farar hula (NSCDC) a matsayin waɗanda ake kara na 1 zuwa 4.

Lauyan ya kuma hada da Babban Lauyan Tarayya (AGF) da Gwamnatin Tarayyar Najeriya a matsayin waɗanda ake kara na 5 zuwa 6.

Ya kuma nemi a biya Naira miliyan 500 a matsayin diyya saboda take hakkin ƴan kasa da abin ya shafa.

Ya yi roko ga kotun da ta bayyana cewa “kame ba bisa ka’ida ba, tsarewa ba tare da tuhuma ba, cin zarafi da karbar kuɗaɗe a wajen wadanda ba su da matsuguni, ‘yan banga, kananan ‘yan kasuwa, mabarata da sauran ‘yan Najeriya marasa galihu mazauna babban birnin tarayya Abuja, ya zama cin zarafi da take ƴancin su na yan kasa.

Don kauce ma haɗari; Sojoji sun haramta amfa da jirgi marar matuki a yankin Arewa maso gabacin Nijeriya
15/01/2025

Don kauce ma haɗari; Sojoji sun haramta amfa da jirgi marar matuki a yankin Arewa maso gabacin Nijeriya

Dambarwar masarautar Kano: A Kotun Ƙoli ma Sarki Sanusi ne zai yi nasara, in ji FalanaFitaccen lauyan nan mai rajin kare...
15/01/2025

Dambarwar masarautar Kano: A Kotun Ƙoli ma Sarki Sanusi ne zai yi nasara, in ji Falana

Fitaccen lauyan nan mai rajin kare ƴancin bil'adama , Femi Falana, SAN, ya tabbatar da cewa ko da an je Kotun Ƙoli, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ne zai yi nasara a shari'ar dambarwar masarautar Kano.

Femi Falana ya yi bayanin hakan ne a taron tunawa da Chief Gani Fewehini karo na 21 da aka gudanar a yau Laraba a Legas.

Taron dai ya samu halartar lauyoyi da dama da masu ruwa da tsaki a fannin shari'a.

Da ya ke gabatar da maƙala a taron, Falana ya ce "Ina so na taya Mai Martaba murna bisa nasarar da ya samu a Kotun Ɗaukaka Ƙara , naji wanda ke Shari'a da shi na cewa zai tafi kotun koli, to ko an je can din ma Sanusi ne zai nasara, kai ko ina ma za a je kai ne da nasara.

"Mai Martaba zama daram, kowa yasan kotun tarayya bata da hurumi kan sha'anin masarauta.

"Yakamata kungiyar lauyoyi ta kasa ta dau mataki kan yadda wasu lauyoyi ke yaudarar wadanda su ke karewa a kotu, ya kamata mu ceto mutuncin wannan tsarin", inji Falana.

15/01/2025

Shirin kaitsaye : Tambayoyi da ansoshi

Jamb zasu fara saida form 15 ga watan January 2025 . Shin Kunsan dalilin da yasa mutane ke cin maki da yawa domin samun ...
15/01/2025

Jamb zasu fara saida form 15 ga watan January 2025 . Shin Kunsan dalilin da yasa mutane ke cin maki da yawa domin samun wanannn shawarwari da kuma koyarwa a online ku tuntubi secrete achivers . Wanda wasu jajurtattun Daliban lafiya da kuma daliban kimiya s**a shirya domin taimakon yara sun cinmma burukansu na karatun da suke so suyi a rayuwa .
Domin Neman Karin bayani ku tuntubi
08034347129 , 09112114311
Ga masu bukata ga link dn group dn akasa👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/FmiUffx3ppwE50DoWSYB8Q

Yan Bindiga sun Harbi Likitan da ya aje tarihi a jami'ar Ahmadu Bello University dake Zaria, wanda ya kasance Dan Asalin...
15/01/2025

Yan Bindiga sun Harbi Likitan da ya aje tarihi a jami'ar Ahmadu Bello University dake Zaria, wanda ya kasance Dan Asalin Jihar Katsina a karamar Hukumar Kankara

A jiya dadare Yan Bindiga s**a kai hari a asibitin Kankara wanda S**a harbi Dr Dandanshiri, wanda yanzu yake karkashin kulawa a Asibitin cikin garin Katsina

Allah yabashi lafiya yayi mana maganin matsalar Tsaro

"Ko a lahira za mu shedi Dikko Radda a gaban Allah cewa mutumin kirki ne ya riƙe zumunci" Sarkin Daura ya yi wa Dikko Ra...
15/01/2025

"Ko a lahira za mu shedi Dikko Radda a gaban Allah cewa mutumin kirki ne ya riƙe zumunci" Sarkin Daura ya yi wa Dikko Radda fatan shiga gidan Aljanna bisa kyawawan manufofinsa ga al'umma

Mi za ku ce game da wannan kyakkyawan zaton da mai martaba sarkin Daura ya yi wa Dikko Radda?

Wato duk Adawar mutum yasan Gwamanan Jihar Katsina mai Tausayi da san yima kowa Adalci, inba a katsina ba ina ka tabajin...
15/01/2025

Wato duk Adawar mutum yasan Gwamanan Jihar Katsina mai Tausayi da san yima kowa Adalci, inba a katsina ba ina ka tabajin andako yan jam'iyyar adawa ta PDP ansaka su cikin kwamitoci, idan a son Bala Abu Musawa ne ba za'ayi haka ba soboda shi makiyin ka ko a ruwa kake sai yace katada kura, tabbas malan Dikko Yafida duk wani Dan Jam'iyyar APC kunya a jihar Katsina

Address

Rong Rod
Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zamani Media Crew posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zamani Media Crew:

Videos

Share