19/09/2020
Police Reform: Mece ce dokar sauya fasalin aikin ƴan sandan Najeriya?
18 Satumba 2020
Wannan doka tana son ofishin shugaban ƴan sanda ya samu kariya ganin wurin ya tsaya tsawon wani lokaci k**ar shekara huɗu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sa hannu kan ƙudurin dokar sauye-sauye ga ayyukan ƴan sanda na 2020 wanda majalisar dokokin ƙasar ta amince da shi.
Yanzu ya zama doka wadda ta tanadi yadda za a inganta ayyukan ƴan sanda ta fuskar samar masu da kuɗaɗe da kayan aiki yadda yak**ata da kuma kare hakkin ɗan Adam don inganta tsaro.
Hon Yusuf Adamu Gagdi dan majalisar wakilai ne a Najeriya da tun farko ya gabatarwa majalisa wannan ƙuduri, ya shaida wa BBC cewa dalilai da dama ne s**a sa a ƙirƙiri wannan ƙuduri.
Ga bayanansa:
1. An ce an samar da yadda al'umma za ta sa hannu a cikin aikin ƴan sanda ta wurin ba da bayanan da zai kawo tsaro ga mutane. Da yadda al'umma za ta zama cikin duk wata harkar tsaro da ta same ta, kwanaki shugaban ƙasa ya amince da fitar da kudi biliyan 13 don aiwatar da wannan aiki.
2. Na biyu akwai abun da ya shafi al'umma ta yadda a wasu lokutan yan sanda kan k**a mutum har ya yi sa'a 48 ko fiye a hannunsu ba a kai shi kotu ba.
Ya k**ata ne daga lokacin aka k**a mutum to ya yi sa'a 24 kawai a hannun ƴan sanda a gurfanar da shi a kotu. Idan ƴan sanda ba su iya sakinsa a wannan lokaci ba to sai sun samu umarnin kotu don ci gaba da tsare mutum fiye da tsawon hakan.
3. Sauran abubuwa sun haɗa da yanayin aikin ɗan sanda da albashin ɗan sanda. Sau da yawa za ka ga ɗan sanda akan t**i amma albashinsa bai fi daga naira 30,000 zuwa naira 45,000 ba a wata.
Ana nufin mutum yana kan t**i yana aiki tsawon wata daya amma a biya shi wannan ɗan kuɗi? Bai je ya kula da iyalansa sosai ba, to yaya ma kuɗin za su ishe shi cin abinci, sa sutura da sayen man mota?
4. Wannan doka ta ɗauki ƙudurin gyara hakkin ƴan sanda don ganin an magance maganar karɓe-karɓen kuɗi a hanya.
5. Haka kuma daga ran da aka samar da hukumar ƴan sanda za ka ga shugabanninta wani ya yi