APC Youth Mobilization Bat LG

APC Youth Mobilization Bat LG Mobilizations and awareness

03/01/2025
Maigirma Dan Majalissar Dokoki ta Jahar Katsina mai Wakiktar Karamar Hukumar Batagarawa Hon Tukur Iliyasu Shagumba nayim...
03/01/2025

Maigirma Dan Majalissar Dokoki ta Jahar Katsina mai Wakiktar Karamar Hukumar Batagarawa Hon Tukur Iliyasu Shagumba nayima Al'ummar Karamar Hukumar Batagarawa da Jahar Katsina da Al'ummar Musulmi baki daya Barka da Safiyar Jumma'a.

Hon Tukur Iliyasu Shagumba na mika Sakon Taya Murna Shiguwar Sabuwar Shekarar 2025 zuwa ga Gwamnan Malam Dikko Umar Radd...
03/01/2025

Hon Tukur Iliyasu Shagumba na mika Sakon Taya Murna Shiguwar Sabuwar Shekarar 2025 zuwa ga Gwamnan Malam Dikko Umar Radda

Maigirma Dan Majalissar Dokoki ta Jahar Katsina mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa Hon Tukur Iliyasu Shagumba na mika Sakon taya Murna Shiguwar Sabuwar Shekarar 2025 zuwa ga Maigirma Gwamnan Jahar Katsina Malam Dikko Umar Radda

Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa ya yabama Gwamnan Jahar Katsina Malam Dikko Umar Radda bisa Ayyukan Alherin da yayima Al'ummar Karamar Hukumar Batagarawa da Jahar Katsina baki daya a Cikin wannan Shekarar data gabata a 2024

Hon Shagumba yayi fatan Allah yaba Maigirma Gwamnan Malam Dikko Umar Radda ikon cigaba da Ayyukan Alherin da yayi a cikin Shekara data gabata ta 2024 a cikin wannan Shekarar da muka shigo ta 2025 domin cigaban Al'ummar Karamar Hukumar Batagarawa da Jahar Katsina baki daya

Daga karshe Hon Tukur Iliyasu Shagumba yayi addu'ar Allah Ubangiji ya kara bamu lafiya da zaman lafiya a Karamar Hukumar Batagarawa da Jahar Katsina da Kasarmu Nigeria baki daya

DAGA
HON MUZAMBILU GIDE BATAGARAWA

S'S'A Media to Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa

Date 3/12/2025.

Jabun Kaya Ake Yiwa Fenti Don Janyo Hankalin Masu SayaNagartattun Kaya Basa Bukatar Karin Haske Wanda Yasan Su Zai Bisu ...
30/12/2024

Jabun Kaya Ake Yiwa Fenti Don Janyo Hankalin Masu Saya

Nagartattun Kaya Basa Bukatar Karin Haske Wanda Yasan Su Zai Bisu Har Inda Suke Domin Ya Saya.

Mafi Akasarin Al'ummar da S**a Sanka da Alkairai S**a Sanka,

Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissar Dokoki ta Jahar Katsina mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa Allah ya karama lafiya da nisan kwana Maigida abin alfarin l'ummar Karamar Hukumar Batagarawa

Ko gobe Al'ummar Batagarawa da kewaye na Al'fahari dakai dan Mutum Shagumba.

Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta Kashe Sama da Naira Biliyan 10 kan Ayyukan Ruwa a Fadin Kananan Hukumomi Bakwai a jihar Da...
28/12/2024

Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta Kashe Sama da Naira Biliyan 10 kan Ayyukan Ruwa a Fadin Kananan Hukumomi Bakwai a jihar

Daga Abbas Nasir PRO (STOWASSA)

Hukumar Samar da Ruwa da Tsaftar Muhalli a Matsakaitan Birane ta Jihar Katsina (STOWASSA), ƙarƙashin jagorancin Babban Daraktanta, Alhaji Ibrahim Lawal Dankaba, ta sanar da kafa kwamitoci masu sa'ido don kula da ayyukan samar da ruwa a ƙananan hukumomi bakwai. Wannan muhimmin shiri, wanda Gwamnatin Jihar Katsina ke daukar nauyi ƙarƙashin shirin nan na Samar da ingantaccen ruwan sha da tsaftar muhalli Mai dorewa Wato (NG-SURWASH) a takaice zai lakume sama da Naira Biliyan 10 don inganta ayyukan samar da ruwa a fadin jihar.

Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Ibrahim Lawal Dankaba, ya jaddada cewa za a fara aikin nan take bayan hutun karshen shekara, duba da cewa gwamnati ta biya kaso 40% na kudin fara aiki ga dukkan ‘yan kwangila. Ya kuma yi kira ga cikakken bin ka’idojin aiki don ganin cewa ayyukan sun yi nasara.

A cewar sanarwar, kwamitocin da za su kula da ayyukan sun hada da shugabannin kananan hukumomi, shugabannin jam’iyyar APC, shugabannin matasa, shugabannin mata, ma’aikatan hukumar STOWASSA, da sauran masu ruwa da tsaki daga al’ummomin da abin ya shafa.

Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D., ya himmatu wajen cika alkawarin samar da ruwa mai tsafta ga al’ummar Jihar Katsina.

“Wannan al'amari wani bangare ne na jajircewar gwamna wajen inganta rayuwar al’ummar Jihar Katsina. Mun zabo mutanen da s**a cancanta don kula da aikin tare da tabbatar da nasarar kammalarsa,” in ji Dankaba.

Ayyukan na samar da ruwan sha za su hada da gina sababbin bututun ruwa, sabunta na da, gyara tsofaffin bututun ruwa a kananan hukumomi k**ar haka: Kankara, Charanchi, Funtuwa, Kafur, Batagarawa, Daura, da Baure.

Ayyukan, wadanda gwamnatin jihar ke gudanarwa karkashin hukumar STOWASSA, suna samun goyon baya daga shirin Samar da ingantaccen ruwa da tsaftar muhalli Mai dorewa Wato (NG-SURWASH) a takaice na Bankin Duniya, wanda yake da nufin samar da ruwa da tsaftar muhalli mai a matsakaitan garuruwa.

Babban Kwamitin Mai Kula da dukkanin Yankunan Shiyyoyin Dan Majalisar Dattawa guda Uku ya kunshi:

1. Alhaji Rabiu Gambo Bakori (Shugaban Kwamitin)
2. Yusuf Abdulkadir Nasarawa (Sakataren Kwamitin)
3. Injiniya Salisu Dahiru Himma
4. Injiniya Muntaka Muhammad Na’iya
5. Arc. Usman Aliyu Hajji
6. Qs. Abdullahi Abdullaziz
7. Alhaji Abdulwahab Sani Stores
8. Hon. Suleman Ahmed Muduru
9. Alhaji Yusuf Shehu Shema
10. Alhaji Abdulrashid Tari Maidabino
11. Alhaji Abubakar Yusuf Bindawa
12. Hajiya Hadiza Manman Danmusa
13. Hajiya Fadila Bala Abdullahi
14.

SAURAN MAMBOBIN GUDA NA KWAMITIN A ƘANANAN HUMOMIN SUN HADA DA;

Kwamitin Kula da aikin na Shiyar Katsina (KATSINA ZONE):

KANANAN HUKUMOMIN BATAGARAWA DA CHARANCHI:

BATAGARAWA LG
1. Hon. Bala Batagarawa (Shugaban Karamar Hukuma)
2. Hadiza Mamman Danmusa (Sakatariya)
3. Shamsu Sahalu Banbami (Shugaban APC)
4. Babangida Sale (Shugaban Matasa)

5. Haire Musa Ibrahim (Shugabar Mata) da sauran mambobi goma sha hudu (14) a karamar hukumar.

*/CHARANCHI LG
1. Hon. Ibrahim Sani (Shugaban Karamar Hukuma)
2. Yusuf Abubakar Radda (Shugaban APC)
3. Abdullahi Dangoggo (Shugaban Matasa)
4. Hajiya Zainab Ahmad (Shugabar Mata) da sauran mambobi goma (10) a karamar hukumar

Kwamitin Kula da aikin na Shiyar Daura
(DAURA ZONE)

Kananan Hukumomin DAURA DA BAURE:

DAURA LG
1. Hon. Bala Musa Daura (Shugaban Karamar Hukuma)
2. Iliyasu Aminu (Sakataren Yanki)
3. Mamman S. Banki (Shugaban APC)
4. Salisu Sallau (Shugaban Matasa)
5. Hajiya Sa’adatu Nahabu (Shugabar Mata) da sauran mambobi goma sha bakwai (17) a karamar hukumar.

BAURE LG
1. Hon. Murtala Adamu (Shugaban Karamar Hukuma)
2. Sani Sule (Shugaban APC)
3. Lirwanu Mamman (Shugaban Matasa)
4. Maryam Sh*tu (Shugabar Mata) tare da sauran mambobi goma sha daya (11) na karamar hukumar.

Kwamitin Kula da aikin na Shiyar Funtua (FUNTUA ZONE)

Kananan Hukumomi FUNTUA, KAFUR, da KANKARA:

FUNTUA LG
1. Muntari Sani (Sakataren Yanki)
2. Hon. Lawal Sani (Shugaban Karamar Hukuma)
3. Muhammad Sani (Shugaban APC)
4. Habibu Muhammad (Shugaban Matasa)
5. Talatu Rabi’u (Shugabar Mata) da karin mambobi goma sha shidda (16).

KAFUR LG
1. Hon. Garba Kanya (Shugaban Karamar Hukuma)
2. Sadi Isiyaku (Shugaban APC)
3. Audu Kaura (Shugaban Matasa)
4. Gaje Usman (Shugabar Mata) da wasu karin mambobi goma sha daya (11).

KANKARA LG
1. Hon. Anas Isah (Shugaban Karamar Hukuma)
2. Mansir Ishaq (Shugaban APC)
3. Garba Gambo (Shugaban Matasa)
4. Shugabar Mata na Karamar Hukumar, da kuma sauran mambobi goma sha daya a karamar hukumar.(11).

Babban Daraktan na Hukumar STOWASSA, Alhaji Ibrahim Lawal Dankaba, ya yi kira ga kwamitoci da duk masu ruwa da tsaki su yi aiki tukuru don cimma nasarar wannan babban shirin karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda.

Hon Tukur Iliyasu Shagumba ya Hallaci Daurin Auren Dan Alhaji Lawal Dallatu Batagarawa inda ya samu Wakilcin Maigirma Ma...
28/12/2024

Hon Tukur Iliyasu Shagumba ya Hallaci Daurin Auren Dan Alhaji Lawal Dallatu Batagarawa inda ya samu Wakilcin Maigirma Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Batagarawa Hon Abdulrahman Ahmed Ajiwa

An Daura Auren Abubakar Lawal Dalhatu Batagarawa Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa ya samu Wakilcin Hon Abdulrahman Ahmed Ajiwa Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Batagarawa kuma Dan Takarar Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Batagarawa a zaben dake tafi na 2025

Al'ummar Karamar Hukumar Batagarawa sun Shaida Daurin Auren Hon Yahaya Lawal Kawo Dan Takarar Chairman din Karamar Hukumar Batagarawa yana daga cikin Manyan baki da Takwaransa Hon Muhammad Ali Rimi Dan Takarar Chairman din Karamar Hukumar Rimi

Maigirma Shugaban Jam'iyar Apc na Karamar Hukumar Batagarawa Alhaji Shamsu Sahalu Bambami shima yana daya daga cikin wadanda s**a shaida daurin Auren

Hon Abdulrahman Ahmed Ajiwa yayi addu'ar Fatan alheri ga Ango da Amarya da niyar Allah yabasu lafiya da zaman lafiya da zuri'a Dayyaba

DAGA
HON MUZAMBILU GIDE BATAGARAWA

S'S'A Media to Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa

Date 28/12/2024.

Hon Tukur Iliyasu Shagumba ya Hallaci Zana'idar Maragayi Alhaji Amadi KurfiAllah yayi Alhaji Amadi Kurfi Rasuwa bayan ya...
25/12/2024

Hon Tukur Iliyasu Shagumba ya Hallaci Zana'idar Maragayi Alhaji Amadi Kurfi

Allah yayi Alhaji Amadi Kurfi Rasuwa bayan yasha fama da jinya Maigirma Dan Majalissar Dokoki ta Jahar Katsina Mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa Hon Tukur Iliyasu Shagumba ya Hallaci Zana'idar

Hon Shagumba yayi addu'ar neman gafara ga Maragayi Alhaji Amadi Kurfi da niyar Allah yaji kansa da rahma Allah yasa aljanace makumarsa muma idan ajalinmu yazu Allah yasa mu cika dakyau da imani

DAGA
HON MUZAMBILU GIDE BATAGARAWA

S'S'A Media to Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa

Date 25/12/2024.

Ɗan Majalisar Tarayya ya bayar da kuɗaɗe, ya gwangwaje Ƙungiyoyi Ƙwallon Ƙafa na Ƙananan Hukumomin Rimi, Charanci, Batag...
25/12/2024

Ɗan Majalisar Tarayya ya bayar da kuɗaɗe, ya gwangwaje Ƙungiyoyi Ƙwallon Ƙafa na Ƙananan Hukumomin Rimi, Charanci, Batagarawa da ƙwallaye da kayan sanyawa
....an kurrama Ɗan Majalisar da Lambar yabo

Ɗan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Ƙananan Hukumomin Rimi da Batagarawa da Charanci Hon. Usman Murtala Banye ya rarraba ƙwallaye da kayan sanyawa na ƴan wasa ga Ƙungiyoyin Wasan Ƙwallon Ƙafa guda 48 a faɗin Ƙananan Hukumomin uku da yake wakilta.

Usman Murtala Banye ya ƙaddamar da bayar da kayayyakin ne a wani taro da ya wakana a farfajiyar gidan sa dake cikin GRA a cikin birnin Katsina.

An dai zaɓo Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa guda 16 daga kowacce ƙaramar hukumar da yake wakilta, inda ya baiwa ƴan wasan ƙwallaye da kayan sanyawa da kuɗaɗe ga ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Ƙananan Hukumomin.

A jawabin sa ya yin kaddamar da kayayyakin, Hon. Usman Murtala Banye ya bayyana cewa zai kuma zaɓo masu horas da ƴan wasa daga ƙananan hukumomin gami da basu kuɗaɗe da kayayyakin wasa domin cigaban wasanni a ƙananan hukumomin.

Ya bayyana cewa ya ƙudiri aniyar haka saboda taimakon matasa gami da sanya su k**a harkar wasan ƙwallon ƙafa a dalilin kwashe amfani da aka yi.

Hon. Usman Murtala Banye ya ce wannan somin taɓi ne ga irin abubuwan da yake da shi ya kuma tsara ga kungiyoyin wasanni na ƙananan hukumomin da yake wakilta.

Yace idan Gwamna Dikko Umaru Radda ya amince za su sanya gasar wasan ƙwallon ƙafa tsakanin matasan tare da baiwa kowace ƙungiyar da ta shiga wasan shatara ta arziƙi.

A wannan rabon ƙwallaye, Ɗan Majalisar ya bada kayan sanya wa da ƙwallaye da dubu 100,000 ga kungiyoyin wasannin gami da bayar da Naira dubu 200,000 ga kungiyoyin wasanni na ƙananan hukumomi.

Haka zalika, saboda irin gagarumar gudummawar da Dan Majalisar ke bayarwa ga ɓangaren wasanni, an karrama shi da Lambar yabo kan namijin ƙoƙarin sa.

Wannan dai bashi ne karon farko da Ɗan Majalisar ke gudanar da aikin cigaban al'umma ba, inda ya kasance a kowane wata, Ɗan Majalisar na yin ayyuka ƙanana da manya ga al'ummar sa, baya ga ciyarwa da taimakon Almajirai da marasa ƙarfi.

Hon Muzambilu Gide Batagarawa.

*Daya daga cikin Abokiyar Gwagwarmayar Hon Muzambilu Gide Batagarawa S'S'A Media to Hon Tukur Iliyasu Shagumba watou Zai...
21/12/2024

*Daya daga cikin Abokiyar Gwagwarmayar Hon Muzambilu Gide Batagarawa S'S'A Media to Hon Tukur Iliyasu Shagumba watou Zainab Halliru Batagarawa (Ministry) zata zama Amarya nan da sati daya mai zuwa*.

*A yau Asabar wanda yayi dai dai da 21/12/2024 Zainab Halliru Batagarawa ta amsa kiran Maigirma S'S'A Media Hon Muzambilu Gide Batagarawa a Office dinsa domin tayata murna akan Auren da zatayi nan da sati daya Mai zuwa inda ta samu rakiyar wasu daga cikin Abokanta*.

*Anyi mana nasihohi akan yadda zata rike Aurenta Malam Usman Muhammad Batagarawa yana daga cikin wanda yayi mata nasiha akan yadda zatayi hakuri a gidan mijinta Mutane da yawane s**a tofa albarkacin bakinsu da kuma yimata addu'ar fatan alheri*.

*Hon Muzambilu Gide Batagarawa ya godema Zainab akan irin gudumuwar da ta bada akan tafiyar shi ta Siyasa daga Karshe Hon Muzambilu Gide Batagarawa S'S'A Media to Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa ya bata Jari domin ta dogara da kanta a gidan mijinta*.

*Allah yasa mudace duniya da lahira dan alfarmar mazon Allah {s a w}*.

*Right: by chairman Batagarawa Media Hub Aliyu Sayyadi Ya'u Batagarawa*

Hon Arc. Usman Murtala  Banye (Usmaniyya Alheri ne) ya samar ma wasu Matasa aiki a Hukumar kashe gobara ta kasa watou Fi...
21/12/2024

Hon Arc. Usman Murtala Banye (Usmaniyya Alheri ne) ya samar ma wasu Matasa aiki a Hukumar kashe gobara ta kasa watou Fire Service)

Maigirm Dan Majalissar Tarayya mai Wakiltar Batagarawa Rimi Charanchi Arc. Usman Murtala Banye yadda kake kula da Al'ummar da kake Wakiltar kai ma Allah Ubangiji ya kula da kai

Tabbas Al'ummar Batagarawa Rimi Charanchi suna samun kyakyawan Shugabancin a Majalissar Tarayya Allah Ubangiji yayi maka Jagoranchi Hon Arc. Usman Murtala Banye

Allah Ubangiji ya baka ikon Cigaba da kawo abubuwan Alheri wanda zai amfani Al'ummar Batagarawa Rimi Charanchi k**ar yadda ka saba kawowa

Hon Muzambilu Gide Batagarawa.

*A yau 20/12/2024 Mai girma (SS'A) MEDIA na dan Majalissar Dokoki ta Jahar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Batagara...
20/12/2024

*A yau 20/12/2024 Mai girma (SS'A) MEDIA na dan Majalissar Dokoki ta Jahar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Batagarawa Hon. Muzambilu Gide Batagarawa*.

*Ya kai Ziyara ta musamman a sabon Office din yan Road safety da aka bude a chikin karamar hukumar Batagarawa a madadin mai gidan sa Hon. Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissar Dokoki ta Jahar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Batagarawa*.

*Yayin da ya samu tarbar shugaban office din baki daya wato Officer Abdullahi Danladi Ibrahim*.

*Shugaban jami'an Road safetyn ya nuna matukar farin chiki da jin dadi da Ziyarar da Wakilin dan Majalissar ya kawo masu in da yake chewa da za'a samu wakilan shuwagabanni irinku masu gaskiya da rikon amana da kuma san chigaban al ummar su da suke wakilta to da an samu chigaba sosai a duniya*.

*Ya kuma Kara da chewa basu bude wannan office din ba sabo da wani abu sai dan su kawo ma wannan karamar hukuma chigaba ta bangarori daban da ban musamman ta bangaran bada temakon gaggawa ga wadanda s**a samu hadani a kan hanya na Mota,kurkura,mashin da sauransu da kuma wayar da kan al'umma ta bagaran kula wajan bin hanya yayin yin tafiya sabo da chigaba da gari ya kara samu ta bangarori daban da ban*.

*Shima mai girma wakilin dan Majalissar wato (SS'A) MEDIA Hon.Muzambilu Gide Batagarawa ya matukar muna farin chikin sa da kuma goyan baya a kan wannan office musamman da yaji an ambani chigaban al ummar karamar hukumar Batagarawa*.

*Ya kuma yi Masu albishir da chewa mai girma da Majalissar yana tare da su dari bisa dari kuma zai tai maka masu da duk wani abin da suke buka ta dan su chigaba da yin aikin nasu chikin sauki da natsuwa da Kwanciyar hankali*.

*Yayin da wakilin dan Majalissar Dokoki ta Jahar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Batagarawa (SS'A) MEDIA nashi wato Hon. Muzambilu Gide Batagarawa a chikin bayanin sa na bankwana ya basu gudumuwar naira dubu ashirin (20'000) domin su kara su sha mai dan chigaba da bada tai makon gaggawa ga al'Ummar karamar humar tamu ta Batagarawa*.

*Daga karshe Shugaban office din yan Road safetyn Officer Abdullahi Danladi Ibrahim yayi godiya ta musamman ga dan Majalissar da wakilin dan Majalissar tare da yi masu fatan alkhairi a chikin al'amurran su na alkairi baki daya*

*Allah yasa Mudace Duniya Da Lahira Dan Alfarmar Mazon Allah {s a w}*

*Right: by Chairman Batagarawa Media Hub Aliyu Sayyadi Ya'u Batagarawa*

Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissar Dokoki ta Jahar Katsina mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa ka zamu Zakara...
19/12/2024

Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissar Dokoki ta Jahar Katsina mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa ka zamu Zakaran Gwaji a Karamar Hukumar Batagarawa

Tabbas Al'ummar Karamar Hukumar Batagarawa suna matukar Al'fahari da Hon Tukur Iliyasu Shagumba saboda Kyakyawan Shugabancin shi a koda wane lokaci zaka gashi cikin Al'ummar shi musamman Talakkawa yana sauraransu kuma yana biya masu butakarsu dai dai da abinda s**a zo mashi dashi

A kowa ce rana idan kaje gidan Hon Tukur Iliyasu Shagumba sai kace gobe ne ranar zabe amman duk da haka Hon Shagumba bai tafa gajiyawa ba da irin abubuwan alheri da yake ma Al'ummarsa ba

Samun irin Hon Tukur Iliyasu Shagumba a dai dai wannan lokacin abune mai matukar walahar gaske ya Allah muna rukonka Allah kacigaba da taikon Maigidanmu Hon Tukur Iliyasu Shagumba saboda wlh bashi da wani guri wanda ya wuce ya taimaki Al'ummarsa Allah kayi mashi maganin abinda yafi karfensa ya Allah ka kara yimai Jagoranchi a cikin duk Al'amurransa na yau da kullun

HON MUZAMBILU GIDE BATAGARAWA

S'S'A Media to Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa

Date 19/12/2024.

Gov. Dikko Umaru Radda has signed the 2025 Budget, titled (Building your Future) into lawKatsina State Governor HE. Mala...
18/12/2024

Gov. Dikko Umaru Radda has signed the 2025 Budget, titled (Building your Future) into law

Katsina State Governor HE. Malam Dikko Umaru Radda PhD, CON, signed the 2025 Budget into law. The budget, initially proposed at ₦682,244,449,523.87 Billion, after a careful Defense exercise by the State House of Assembly, an additional ₦10 Billion was discovered and added before approval, which metamorphose the amount to 692,244,449,513.87 Billion. This adjustment emphasizes the administration’s focus on development and aligning with the needs of the people

The Budget was submitted to the Governor for assent by the Speaker of the House, Rt. Honourable Nasir Yahaya Daura FISS, alongside with his Deputy, Rt. Honourable AbdulJalal Haruna R***a, House Leader, Honourable Shamsuddeen Abubakar Dabai, Chief Whip, Honourable Ibrahim Umar Dikko, Chairman House Committee on Appropriation, Hon. Lawal H. Yaro, and other Honorable members of the House

This collaborative approach highlights the legislature’s role in fine-tuning the budget and ensuring it aligns with the developmental priorities of the state before it was signed into law

This process underscores the strong partnership between the executive and legislative arms of government in Katsina State, aimed at implementing impactful Budget for the benefit of the citizens. May it be beneficial to Katsina and its citizens.

Report by Hon Muzambilu Gide Batagarawa S'S'A Media to Hon Tukur Iliyasu Shagumba

Date 18/12/2024.

Breaking: Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD CON ya rattaba hannu a dokar kasafin kuɗin shekarar 2025.Gov...
18/12/2024

Breaking: Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD CON ya rattaba hannu a dokar kasafin kuɗin shekarar 2025.

Governor Dr. Dikko Umaru Radda has assented the appropriation law for the 2025 which was approved by the Hon. House.

The Speaker Rt Hon Nasir Yahaya Daura led other Hon. Members to Government House for the historic ceremony

Allah ya sa ya amfani al'umma
Allah kara bamu lafiya da zaman lafiya a duk inda muke

DAGA
HON MUZAMBILU GIDE BATAGARAWA

S'S'A Media to Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa

Date 18/12/2024.

BREAKING NEWS: MAJALISAR DOKOKI TA ZARTAR DA DOKAR KASAFIN KUƊIN SHEKARAR 2025Majalisar Dokokin jihar Katsina ta amince ...
17/12/2024

BREAKING NEWS: MAJALISAR DOKOKI TA ZARTAR DA DOKAR KASAFIN KUƊIN SHEKARAR 2025

Majalisar Dokokin jihar Katsina ta amince da zunzurutun kuɗi Naira (₦692,244,449,513.87 ) Biliyan Dari Shida da casa'in da Biyu da Miliyan Dari biyu da Arba'in da Huɗu da Dubu Ɗari Huɗu da Arba'in da Tara da Ɗari Biyar da Sha Uku da kwabo Tamanin da Bakwai kasafin kudin shekarar 2025

Kenan an sami karin Naira Biliyan Goma bisa ga ƙiyasin kuɗi da Maigirma Gwamnan jihar Katsina ya gabatar wa majalisar

Katsina State House of Assembly has passed the 2025 Appropriation Bill in to law

Katsina State House of Assembly has approved the sum of
₦692,244,449,513.87 as the Recurrent and Capital Expenditure for the year 2025

DAGA
HON MUZAMBILU GIDE BATAGARAWA

S'S'A Media to Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa

Date 17/12/2025.

Fatan Alheri ga Al'ummar Karamar Hukumar Batagarawa da Jahar Katsina da Kasarmu Nigeria baki daya Allah Ubangiji ya kara...
15/12/2024

Fatan Alheri ga Al'ummar Karamar Hukumar Batagarawa da Jahar Katsina da Kasarmu Nigeria baki daya Allah Ubangiji ya kara mana lafiya da zaman lafiya.

Hon Tukur Iliyasu Shagumba ya Hallaci Daurin Auren Dandan Hon Aliyu Abubakar Albaba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar H...
14/12/2024

Hon Tukur Iliyasu Shagumba ya Hallaci Daurin Auren Dandan Hon Aliyu Abubakar Albaba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar Hukumar Katsaina

An Daura Auren Alhaji Abdulkadir Aliyu Abubakar Albaba da Amaryarsa Fatima Babangida Abubakar Albaba akan Sadaki Naira Dubu dari biyu (200,000) kuma anbiya Lakadan

Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissar Dokoki ta Jahar Katsina Mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa yana daya daga cikin wadanda s**a Shaida Daurin Auren

An Daura Auren a Masallacin Jumma'a na Alhaji Dahiru Bara'u Mangal, Maigirma GOC Alhaji Dahiru Bara'u Mangal shine Wakilin Amarya Watou Fatima Babangida Abubakar Albaba

Hon Shagumba yayi fatan Alheri ga Ango da Amarya da niyar Allah ya basu lafiya da zaman lafiya da zuri'a dayyaba

DAGA
HON MUZAMBILU GIDE BATAGARAWA

S'S'A Media to Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa

Date 14/12/2024.

Hon Tukur Iliyasu Shagumba ya Shaida Daurin Auren Maryam Sada Tukur da Angonta Abba Tukur Sha'itu a Unguwar Sodangi dake...
14/12/2024

Hon Tukur Iliyasu Shagumba ya Shaida Daurin Auren Maryam Sada Tukur da Angonta Abba Tukur Sha'itu a Unguwar Sodangi dake cikin garin Dabaibayawa a Karamar Hukumar Batagarawa

A jiya Jumma'a wanda yayi dai dai da 13/12/2024 Maigirma Dan Majalissar Dokoki ta Jahar Katsina Mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa Hon Tukur Iliyasu Shagumba ya Shaida Daurin Auren Kawar Hon Abubakar Sodangi Dabaibayawa Inda ya samu Wakilcin S'S'A Media nashi Watou Hon Muzambilu Gide Batagarawa

An Daura Auren a Unguwar Sodangi dake Dabaibayawa a Karamar Hukumar Batagarawa Hon Yahaya Lawal Kawo Dan Takarar Chairman din Karamar Hukumar Batagarawa yana daya daga manyan bakin da s**a Shaida Daurin Auren

Hon Tukur Iliyasu Shagumba yayi fatan Alheri ga Ango da Amarya da niyar Allah ya basu lafiya da zaman lafiya da kuma zuri'a dayyaba

DAGA
HON MUZAMBILU GIDE BATAGARAWA

S'S'A Media to Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa

Date 14/12/2024.

Address

No. 23 Batagarawa Local Government
Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when APC Youth Mobilization Bat LG posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to APC Youth Mobilization Bat LG:

Share