
24/10/2024
Hakki ne ga duk wani Ɗan Uwa da ya ga rubutun nan ya yaɗa shi, domin ya shiga ko'ina, yan uwa su falka.
NAJERIYA INA MUKA DOSA? 4
Babu tashin hankali kamar ace ga al'umma, iya al'umma, amma bata san makomarta ba. Bata san matserarta da mayankanta ba. Bata san macecinta da macucinta ba. Bata san Gabas ɗinta da yammanta ba.
Abunda ya fi wannan tashin hankali shi ne, wani daga cikinsu ya gano bakin zaren, alhali saura na cikin Ɗimuwa. To haka zai zauna a cikinsu tamkar fursuna. Ga halaka yana ganin tana kewayesu, za ta gama da su, amma babu mai saurarenshi, b***e ya ankare. Ganin alummarka tana halakewa a gaban idanunka, alhali Kanada da hanyar kuɓutar da su a hannunka, da ace sun saurareka, ba ƙaramar Azaba bace.
Shi ya sa a kullum dole mu Yan Harka Islamiyyah mu Tausayawa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Da a ce wani zai daina bacci, ya dinga kukan jini, saboda tausayin wannan bawa na Allah, dangane da yadda al'ummar nan take bijirewa faɗakarwarsa da jan hankalinsa, dangane da yanayin da su ke ciki, da wanda Addininsu ya ke ciki, to da bai zamo abun zargi ba. Sai dai ma a yaba masa.
Billahi alaikum, ya ku wannan al'umma, minene Malam Ibraheem Al-zakzaky bai faɗa maku ba, game da sharrin Maƙiya a kanku, tun fiye da shekaru 40+?
Billahi alaikum, akwai wata kutungwuila, ko wani Sharri, ko makirci, tun daga rikicin mai tatsine, sauya tsarin mulki, cin hanci da rashawa, shari'ar bogi, rikicin Addini da ƙabikanci, rikicin mazhabobi da firkoki, rikicin boko haram, bandits, kidnapping, rikicin Hausawa da Fulani, satar ma'adanai, anshe gonaki, lalata tituna, tsadar man fetur, hauhawar farashi, rugujewar Tarbiyyah, shigowa da sabbin policies, hanƙoron Tinƙahon duniya, sharrin Yahudawa a kanmu, da dai sauran matsaloli, Shin akwai wadda bai gargademu a kan zuwanta tun kafin ta zo ba?
To kuma akwai wadda ya faɗa, aka ki saurarensa sai bata zo ba?
Shin wannan bai ishemu hankali ba?
Manta da Aƙidar malam, wadda wasu suke yiwa Mummunar fahimta, Shin ashe wanda ya ce da kai hattara ga rijiyan nan a gabanka, bai kamata ka saurari maganar sa a nan ba? Hatta kuwa koda ka ɗauka shi mara hankali ne, domin zai yiwu a nan yanada gaskiya.
Yanzu ga shi kusan duk sun gama lalata komai, saura su raba iyaye da Ɗiyansu, wanda shima yana daf da faruwa, musamman Ɗiya mata, daga nan sai a raba mutane da Addini, dama family ne ke rike da Addini, to idan an watse family addini zai ɓace.
Shin sai yaushe kunnuwanmu za su saurari wannan bawan Allah? Sai sun gama halaka mu?
Ko kuwa sai sun karkare kawarda da shi?
Kamar yadda suke yita hanƙoron haka, tun bayan fitowarsa daga gidan yari.
Musamman a kwanakinan, sun matsa sai sun kashe Sayyid Ibraheem Al-zakzaky, da Almajiransa a inda yake a Abuja.
Musamman bayan Ɗufanul Aqsa, inda aka jiyo Na yan hoo yana rantsuwa sai ya Murkushe masu kishin Addinin musulunci a Yammacin Afrika. Wanda kai tsaye da Sayyid Ibraheem Al-zakzaky yake, domin shine Almajirin Sayyid Ali Khamene'i mai kira irin nasa.
Babban abun mamakin shi ne, idan mutanen gari basu damu da wannan Haɗarin da yake tunkarar mu ba, bai kamata a ce yan uwa musulmi, musamman yan Harka Islamiyyah sun gafala daga wannan sharrin ba. Shin so suke sai sun ji labarin wani abu mara daɗi ya faru sannan su yi fargar jaji?
Isra'ila ta rantse sai ta kashe malam, to mu kuma ashe bai kamata mu bashi kariya da dukkan abunda za mu iya ba.?
Wasu ma ɗauka ɗauka suke, komai ya wuce, malam na can zaune ne cikin aminci, ya Allah.
Wasu kuwa tunda suna da matsala da wasu to ba za su yi abunda ya dace ba, saboda wadannan. Wannan wane irin reverse ne?
Wasu kuwa sun rantse sai sun huce fushinsu ga wasu. Sai kace dama ba aikin addini suke ba.
Wasu kuma neman abinci da son hutu ya shagaltar dasu.
Maƙiya sun bi mabiya sun rabawa kowa aiki, ya ɗauka yanata yi.
An bar Malam kusan shi Kaɗai a filin daga kuraye suna daka masa harara, tamkar Imam Husaini a filin Karbala. 😭
Yaushe za mu falka yan uwa. Mu cika Abuja da kewayen Abuja, mu ba wannan bawan Allah kariya. Kowa ya ajiye son ran sa ya yi abunda ya dace. Tun kafin lokaci ya kure mana. Ba wanda suke tsoro a Ƙasar nan idan ba malam ba. Ba wanda s**a dage sai sun kawar kamarsa. To mu hana faruwar haka.
_Dr. Shamsudeen Hassan