HMD TV

HMD TV Thank

28/07/2022

"Ga fa ɗaya daga cikin irin matsalolinmu: inda babu kwarafshan

Daga Farfesa Mansur Sakkwato

A ƙasar Jamus ne wani ɗan gudun hijira daga ƙasar Yaman yake ba da labari yana cewa:

"Lokacin da na shiga kasar Jamus a 2015 gwamnatin kasar ce ta biya min kudin hayar gida da na ruwa da wuta na shekara daya kamar yadda doka ta tanada. Bayan haka kuma in na samu aiki sai in ci gaba da biya da kaina.

Bayan da na soma biyan kudin wuta da kaina wata rana sai credit dina ya kare ana bi na kusan ¥200, kwatsam sai aka dauke wutar gidana. Ban dauki lamarin da wani muhimmanci ba tun da ni kam a kasarmu rashin wuta ba komai ba ne. Sai kawai na sayi kyandur muka kunna muka cigaba da sha'aninmu ni da iyalina.

Ba a fi sa'a daya ba sai makota s**a taru a kofar gidana, wai sun ga ba haske a gidan amma suna jin duriyar mutane. Sai na bayyana musu cewa wannan ba komai ba ne, mu a kasarmu wutar lantarki kamar cin tuffaha ne sai 'yan birni. A birnin ma akan dauke wuta na tsawon lokaci, don haka mun saba, babu matsala. Kuma ma dai - insha Allahu - zuwa sati mai zuwa in na samu albashi zan biya kudin wutar.

Sai na ga sun girmama abin matuka; wai har a yi sati daya a gidan dan'adam ba wutar lantarki. A daren nan s**a sayo min janareta sabo ful s**a girke min a kofar gidana.

Wayewar gari sai kira nake ta samu daga tashoshin talabijin daban-daban wai sun samu labarin halin da nake ciki, suna son su yi hira da ni. Kafin wasu 'yan sa'o'in sai ga ma'aikatan kamfanin wuta sun zo don hada wutar gidana tare da takarda rubutacciya ta ba ni hakuri da kuma kyautar katin ¥1500 wai don ta da komadar dare daya da na share ba wuta, watakila ma ajiyar da na yi a firij ta dan samu matsala. Wai su nan suna neman in rufa masu asiri kada 'yan kasar Jamus su zarge su da rashin imani.

Shi ne na ce, oh! Wata miya sai a makota. Mu a kasarmu asibiti ma zai wuni ya kwana ba wuta b***e gidan talaka!

Allah ya shirye mu da shugabanninmu ya ba mu ikon gyarawa.

Copied from Sharif Mu'az Nababa

Address

Kofar Kaura
Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HMD TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to HMD TV:

Share

Category


Other TV Channels in Katsina

Show All

You may also like