Hausa Post

Hausa Post GASKIYA DA GASKIYA

14/05/2024

HUKUMAR HISBA A KATSINA TA K**A DANJARIDA A LOKACIN DA YAKE KAN AIKINSA.

Hisba ta k**a Dan jaridar Jamilu Mabai wanda shine wakilin gidan talabigin na trust tv a katsina bisa zarginsa da yin dogon rubutu na 6atanci ga hukumar a kafar sadarwa ta Facebook

DCL Hausa ta ruwaito cewa hukumar ta Hisbah ta nemi dan jaridar ruwa a jallo sak**akon wani rubutu da ya yi a kafar sadarwa ta Facebook, wanda yake da alaƙa da zargin cin mutuncin hukumar da shugabanta

Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta k**a ɗan jarida Jamilu Mabai, wakilin gidan talabijin na Trust Tv a jihar Katsina.

An k**a danjarida jamilu Mabai ne a wannan Talata bayan da ya je hukumar da niyyar haɗa rahoto na zargin da ake ma hukumar na harbe wani dattijo mai sana'ar faci da bindiga, wanda hakan ake zargin ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

20/04/2024

Dogaran tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello sun shiga hannu bisa zargin taimaka mishi ya tserewa jami'an hukumar EFCC da s**ayi yunkurin k**ashi.

Hukumar EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo bisa laifukan dake alaka da kudi da s**a zarta biliyan 80.

24/03/2024

Ɗaliban Makarantar Kuriga da 'yan bindiga da s**ayi garkuwa dasu sun sami isakar'yanci.


An sako dukkan Ɗaliban Makarantar na Kuriga guda 137 da masu garkuwa da mutane s**a sace a jahar Kaduna.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ne ya sanar da hakan a wata sanarwa,inda yake godewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Mai bashi shawara akan tsaron kasa Malam Nuhu Ribadu saboda kokarin da s**a yi wajen ganin an sako daliban.

11/02/2024
Fatima Sa'id da aka fi sani da BINTU a shirin Dadinkowa mai dogon zango na tashar Arewa24 ta rasuTa rasu da misalin karf...
11/02/2024

Fatima Sa'id da aka fi sani da BINTU a shirin Dadinkowa mai dogon zango na tashar Arewa24 ta rasu

Ta rasu da misalin karfe 2:00pm na Lahadin nan bayan fama da rashin lafiya.

23/12/2023
Ƴan Chadi na kaɗa kuri’a kan sabon kundin tsarin mulkiMasu kada kuri’a a kasar Chadi sun fita rumfunan zabe ranar Lahadi...
17/12/2023

Ƴan Chadi na kaɗa kuri’a kan sabon kundin tsarin mulki

Masu kada kuri’a a kasar Chadi sun fita rumfunan zabe ranar Lahadi domin kaɗa kuri’ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin kasar, a wani muhimmin mataki na zabuka da kuma dawo da ikon farar hula da aka yi wa ƴan ƙasar alkawari, amma gwamnatin mulkin soja mai mulki ta jinkirta cika shi.

Wani babban bangare na ƴan adawa da kungiyoyin fararen hula a kasar da ke tsakiyar Afirka na yin kira da a ƙauracewa zaɓen.

Suna masu cewa an tsara shi ne kawai domin share fagen zaɓen shugaban rikon ƙwarya na yanzu, Janar Mahamat Idriss Deby Itno, da kuma ci gaba da “daular” da mahaifinsa ya fara shekaru 33 da s**a gabata bayan juyin mulkin da ya jagoranta.

Ɓangaren masu cewa “E” da alama yana da tabbacin samun nasara bayan ƙayataccen yaƙin neman zaɓen da gwamnatin mulkin soji ta yi kan ƴan adawar ƙasar waɗanda kawunansu ke rarrabe, wadanda kuma s**a fuskanci kame da tsoratarwa da barazana yau fiye da shekara guda ke nan.

Ko ina ka duba cikin babban birnin ƙasar N’Djamena, fasta-fasta masu nuna ƙuri’ar “E” za ka gani waɗanda ke iƙirarin “samar da kundin tsarin mulki don ƙasa mai haɗin kai.”

Wannan tsarin mulkin bai sha bamban da kundin tsarin mulkin da sojoji s**a soke a shekarar 2021 ba, inda s**a kafa tsarin mulki wanda akasarin madafun iko ke tattare a hannun shugaban kasa mai cikakken iko.

Ƴan adawa da masu ra’ayin tarayya suna goyon bayan kuri’ar “A’a”.

Ɓangaren “E” kuwa na mayar da martani da cewa ƙasa mai dunkulewa ita ce kadai hanyar tabbatar da haɗin kai, yayin da suke a’awar tsarin tarayya zai karfafa “watsewa” da “hargitsi” ne.

An shirya fitar da sak**akon wucin gadi a karshen watan Disamba, inda kotun ƙolin ƙasar za ta tabbatar da sak**akon bayan kwanaki hudu.

An sako sauran matan da aka sace a jami'ar Dutsinma ta KatsinaHukumomin Jami'ar Tarayya ta Dutsimma da ke Jihar Katsina ...
16/12/2023

An sako sauran matan da aka sace a jami'ar Dutsinma ta Katsina

Hukumomin Jami'ar Tarayya ta Dutsimma da ke Jihar Katsina sun tabbatar da sako ragowar ɗaliban makarantar hudu da 'yan bindiga s**a sace a kwanakin baya.

Shugaban Jami'ar Farfesa Arma Ya'u Hamisu Bichi ne ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da ya yi da BBC, inda ya ce da taimakon gwamnatin Tarayyara aka sako yaran.

"A yammacin Juma'a aka yi mani waya ina Saudiyya aka ce an sako sauran yara huɗun da ake tsare da su, kuma an yi Abuja da su domin nuna wa gwamnati su.

"An yi aikin sako su ne tare da mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malan Nuhu Ribadu. Wanda tun lokacin da aka sako ta farko ya yi mana alƙawarin za a sako sauran hudun da ke hannu," in ji Bichi.

Ya ce ba a biya ko naira ɗaya ba aka karbo waɗannan yara. Kuma dukkansu suna cikin ƙoshin lafiya.

Nan da ranar Lahadi ko Litinin za a sada yaran da iyayensu, in ji shi.

Katsina dai na cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro da ta ƙi-ci-ta-ƙi cinyewa.

Gwamnan Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya halarci taron kungiyar gwamnonin arewacin Nijeriya a KadunaGwamnan jihar ...
15/12/2023

Gwamnan Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya halarci taron kungiyar gwamnonin arewacin Nijeriya a Kaduna

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD na daga cikin gwamnonin jihohin arewacin Nijeriya da s**a gudanar da taro a Kaduna don tattauna batutuwan da s**a jibinci yankin da kuma yunkurin tallafar al'ummar kauyen Tudun Biri da ibtila'in bam ya fada mawa a makon jiya.

Kungiyar Gwamnonin Arewa ta yi kudurin tallafa wa wadanda harin bam ya rutsa da su a kauyen Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi ta hanyar bayar da gudunmawar Naira Miliyan Dari da Tamanin (N180,000,000).

Haka zalika, Kungiyar ta yanke shawarar yin aiki tare don tabbatar da cewa an yi bincike sosai kan lamarin da nufin biyan diyya da kuma daukar matakan gyara domin hana afkuwar irin haka a nan gaba.

Kungiyar ta yabawa Gwamnatin Tarayya bisa nuna himma da ta yi wajen yaki da ta’addanci, garkuwa da mutane, fashi da makami da ya dade yana addabar yankin. Kungiyar ta kuduri aniyar tsayawa tsayin daka wajen tunkarar wadannan kalubale ta hanyar inganta hadin gwiwa da hukumomin tsaro, karfafa ayyukan tabbatar da doka a cikin gida, hada kan al’umma, daukar fasahar zamani da sauye-sauyen harkokin mulki, tare da magance matsalolin rashin tsaro k**ar talauci, rashin aikin yi.

Taron ya ƙudiri aniyar hanzarta haɗa haɗin gwiwar yanki baki ɗaya ta hanyar saka hannun jari a cikin ababen more rayuwa, haɓaka kasuwanci, noma, muhalli, tattalin arziƙi da sauran su.

Taron dai ya samu jagoranchin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahya Wanda ya gudana a gidan Gwamnatin Jihar Kaduna. Malam Dikko Umaru Radda, Gwamnan Jihar Katsina na cikin Gwamnonin da s**a halarci taron. Daga karshe, sun ziyarci asibiti domin duba mutanen da s**a jikata ta sanadiyar wannan harin bom da sojoji s**a kaima farar hula a Tudun-Biri.

Isah Miqdad
SSA Digital Media
15/12/2023

Yan Najeriya Na Da Ƴancin Ɗaukar Bidiyon Ƴan Sanda A Bakin AikiHukumar 'yan sandan Najeriya ta ce yan ƙasar na da damar ...
15/12/2023

Yan Najeriya Na Da Ƴancin Ɗaukar Bidiyon Ƴan Sanda A Bakin Aiki

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta ce yan ƙasar na da damar ɗaukar bidiyo da hotunan 'yan sanda a lokacin da suke bakin aiki.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ƙasar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X ranar Alhamis.

Adejobi na mayar da martani ne kan saƙon da wani mai amfani da shafin ya wallafa da ya ce 'yan sanda sun tatse shi naira 10,000 saboda bidiyon da ya ɗauke su a lokaci da suke binciken ababen hawa.

Kakakin rundunar ya ce ba laifi ba ne ɗaukar hoto da bidiyon 'yan sanda a lokacin da suke bakin aiki.

Ya ƙara da cewa rundunar ta sha gaya wa mutanen cewa babu laifi ɗaukar bidiyo da hotunan 'yan sandan da ke bakin aikin.

Mista Adejobi ya ce duk wanda 'yan sanda s**a ci zarafinsa saboda ɗaukarsu bidiyo ko hoto su kai rahoto ga hukumar 'yan sanda.

17/11/2023

Kotun 'Daukaka Kara ta Kori karar da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya shigar da yake kalubalantar Hukuncin Kotun Tribunal data baiwa APC Nasara.

Kotun ta kuma tabbatar da Nasara ga Dakta Nasiru Yusuf Gawuna k**ar yadda Kotun Farko tayi.

Gwamna Mai Ci na Jam'iyyar APC a Jahar Imo ya lashe Zaben Gwamnan Jihar  wanda aka gudanar a Jiya Asabar .Hukumar Zaben ...
12/11/2023

Gwamna Mai Ci na Jam'iyyar APC a Jahar Imo ya lashe Zaben Gwamnan Jihar wanda aka gudanar a Jiya Asabar .

Hukumar Zaben INEC ta Samar da cewa Gwamna Mai Ci Hope Uzodinma shiya lashe Zaben Gwamna da aka Gabatar a Jiya Asabar da kuri'u dubu 'dari 540,308 sai Kuma PDP da 'dan takarar ta Sam Anyanmu s**a samu Kuri'u 71,503. Yayin da Athan Achonu na Jam'iyyar Labour ya samu Kuri'u dubu 64,081.

25/10/2023

A cigaba da hana shigowa da kaya ta Bakin iyaka (border)shi yafi_ Danmajalisa tarayya maiwakiltar karamar hukumar da keda border a jahar Katsina.

Hon sada soli Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomi jibia da kaita, ya gabatar
da kudirinne a zauren majalissar inda
Yake kalubalantar gwamnatin tarayya na cewa za'a cigaba da shigowa da Kayayyaki ta iya kokin kasar Irin su shinkafa, da siminti da sauran abubuwa 43 da CBN ya aminta a shigo da su daga waje, zai durkusar da tattalin arzikin Nijeriya, tuni majalisar ta amince da kudurin da ya gabatar mata.

Kudurin ya ja Majalisar Wakilan tarayyar Nijeriya, ta bayyana gayyatar Dr Olayemi Cardoso da ya gurfana a gabanta, sak**akon ɗage haramcin shigowa da kayayyakin abinci 43 daga ƙasashen waje ciki har da shinkafa

Ayyana gayyatar shugaban babban Bankin Nigeria(CBN) na zuwa ne bayan kudurin Na Dan majalissar daga jahar Katsina ,sada soli jibia kan batun kiran gaggawa game da janye dokar da aka sanya tun a watan June 2015 ta takaita shigowa da wasu abubuwa daga waje don haɓɓaka tattalin arzikin Nijeriya.

A cikin kudirin da ya gabatar, Dan majalissar maiwakiltar kananan hukumomin jibia da kaita Hon sada soli jibia ya ce shigowa da wasu kayayyaki daga waje, zai taimaka wajen durkushe sana'o'in da ake yi a cikin gida Nijeriya, irinsu noman shinkafa da, kamfunan siminti, manja da sauransu, inda ya ce daga karshe hakan na iya jawo kulle wasu kamfanoni dake aiki a cikin Nijeriya.

Wannan shi ne ake cemawa ta leƙo ta koma: Shigowa da shinkafa, da siminti da sauran abubuwa 43 da CBN ya aminta a shigo da su daga waje, zai durkusar da tattalin arzikin Nijeriya, Sada Soli ya gabatar da kudiri a majalisar wakila

Majalisar Wakilan tarayyar Nijeriya, ta bayyana gayyatar Dr Olayemi Cardoso da ya gurfana a gaban ta.

Ɗangote Ya Kai Ziyarar Ta'aziyya Ga Attajirin Ɗan Kasuwa Alhaji Ɗahiru Bara'u Mangal Bisa Ga Rasuwar Uwargidansa Haj. Ai...
22/07/2023

Ɗangote Ya Kai Ziyarar Ta'aziyya Ga Attajirin Ɗan Kasuwa Alhaji Ɗahiru Bara'u Mangal Bisa Ga Rasuwar Uwargidansa Haj. Aisha Ɗahiru Mangal A Jihar Katsina

Attajirin Ɗan kasuwa mai kuɗin Afrika Alhaji Aliko Dangote, yakai wa hamshakin ɗan kasuwa shugaban kamfanin sufurin jiragen sama na Max-Air Alhaji Ɗahiru Bara'u Mangal CON, ta'aziyar Rasuwar Uwargidansa Hajiya A'isha da safiya yau Asabar 22/07/2023.

Ɗangote, ya yi addu'oi na musamman ga mamaciyar domin nema mata rahamar Allah tare da sauran musulmi baki ɗaya.

Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sunayen wadanda s**a yi nasarar zama manyan sakatarori (Permanent Secretaries) bayan...
14/07/2023

Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sunayen wadanda s**a yi nasarar zama manyan sakatarori (Permanent Secretaries) bayan da s**a zauna jarabawar cancanta

Gwamnatin Jihar Katsina ta fitar da jerin sunayen mutane 36 da s**a yi nasara a jarabawar cancanta da ta gudanar domin nadawa mukamin manyan Sakatarori.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Usman Isyaku, babban Sakatare a ofishin shugaban ma'aikata na jihar Katsina.

Sanarwar ta ce an sake nada tsoffi da sabbin manyan sakatarorin ne bisa cancanta da irin gogewarsu a aikin gwamnati.

Kazalika, sanarwar ta ce za a sanar da ranar da za a rantsar da su tare da tura su ma'aikatun da za su yi aiki nan gaba.

Sabon shugaban Kwamandan Hisba na jahar Kano Shiek Aminu Ibrahim Daurawa ya shiga ofishin  a yau laraba 12/07 /2023Daura...
12/07/2023

Sabon shugaban Kwamandan Hisba na jahar Kano Shiek Aminu Ibrahim Daurawa ya shiga ofishin a yau laraba 12/07 /2023

Daurawa ya jaddada cigaba da auran zawarawa wanda Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sahale yayi haka kuma ya karbi faretin ban girma daga dakarun hukumar Hisba.

📸 Ado Danladi Farin Gida

An mika sabbin motocin bas-bas masu mak**ashin lantarki da kasar china ta Kira.
08/07/2023

An mika sabbin motocin bas-bas masu mak**ashin lantarki da kasar china ta Kira.

Gwamnatin jihar Katsina ta fara  shiri na musamman don daukar matasa 2,400 domin magance matsalolin tsaro dake addabar w...
08/07/2023

Gwamnatin jihar Katsina ta fara shiri na musamman don daukar matasa 2,400 domin magance matsalolin tsaro dake addabar wasu sassan jihar.

Bayan dauka da ba matasan horo, za su hadu da jami'an tsaro domin kara samar da tsaro a kananan hukumomi 8 da s**a sha fama da matsalolin tsaro a jihar.

A ranar Juma'ar nan 7th Juli, 2023 ne dai mataimakin Gwamnan jihar Hon Faruq Lawal Jobe ya kaddamar da rarraba takardun cikewa na 'form' ga shugabannin kananan hukumomin da lamarin ya shafa. Daga nan, shugabannin kananan hukumomin za su zakulo tare da tantance matasan, su rarraba musu wadannan takardun cikewa domin zuwa mataki na gaba na kokarin kare rayuka da dukiyoyin al'ummominsu.

Gwamnatin jihar dai ta ce babban makasudin wannan yunkuri, shi ne don karin maganar nan ta Hausawa dake cewa "da dan gari, a kan ci gari". Wadannan matasa sun san lungu da sako na yankunansu, don haka za su tallafi jami'an tsaro wajen bi kokuwa-kokuwa don fatattakar masu aikata assha a cikin al'umma.

Idan dai zaku iya tunawa, lokacin yakin neman zabe, Malam Dikko Umaru Radda ya yi alkawarin cewa tsaro na a sahun gaba a cikin alkawurran da ya daukar wa al'ummar jihar, inda ya buga misali da zuwa har wuraren da ake ganin ba su shiguwa ta dalilin ayyukan 'yan bindiga a lokacin yakin neman zabe.

A lokacin rarraba wadannan takardun cikewa na 'form', mataimakin Gwamnan jihar Katsina Hon Faruq Lawal Jobe ya ce, "sanin kowane cewa Mai Girma Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya sha alwashin kawo karshen ayyukan ta'addanci musamman ma a kananan hukumomin da lamarin ya yi k**ari, da sauran sassan jihar".

Mataimakin Gwamnan ya ce an shirya daukar wadannan matasa, su hadu da jami'an tsaro su ba su horo na musamman domin su tallafi jami'an tsaron wajen samar da tsaro.

Hon Faruq Lawal Jobe ya ce za a dauki matasa 300 a kowanne kananan hukumomin 8 da lamarin ya fi k**ari. Sannan ya ce za a dauki matasan da ba su wuce shekaru 35 da haihuwa.

Gwamnatin jihar Katsina ta ba da umurnin gaggawa na ginawa tare da fadada magudanan ruwan da ake da su musamman cikin kw...
07/07/2023

Gwamnatin jihar Katsina ta ba da umurnin gaggawa na ginawa tare da fadada magudanan ruwan da ake da su musamman cikin kwaryar birnin Katsina.

Gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda ta hannun mataimakinsa Faruq Lawal Jobe ta ce hakan zai ba ruwa damar wucewa salin-alin a duk lokacin da aka samu mamakon ruwan sama.

A lokacin da yake ganawa da manema labarai a lokacin da ya ziyarci inda aka samu ambaliyar ruwan, Hon. Faruq Jobe, ya ce gwamnatin jihar karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda ta yi umurnin gaggawa na a sake buda magudanan ruwa a inda ba su wadata ba, da kuma gina sabbi a duk inda babu, domin ruwan ya samu damar wucewa ba tare da ya yi ambaliya ga gidaje da dukiyoyin al'umma ba.

Da wannan umurni na Gwamnatin Malam Dikko Radda, kamfanin da aka baaikin, zai kammala cikin kankanin lokaci ganin yadda damina ke kara inganta.

SSA Isah Miqdad,
Ofishin Daraktan Yada Labarai.
7/07/2023.

Yadda aka bude bikin baje kolin na’urori masu kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI a birnin Shanghai na kasar Sin.
07/07/2023

Yadda aka bude bikin baje kolin na’urori masu kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI a birnin Shanghai na kasar Sin.

Rundunar 'Yan Sandan Jahar Kano ta bayyana sunayen wasu Matasa da su gaggauta Kai kansu Shalkwatar Rundunar domin tattau...
06/07/2023

Rundunar 'Yan Sandan Jahar Kano ta bayyana sunayen wasu Matasa da su gaggauta Kai kansu Shalkwatar Rundunar domin tattaunawa, ko kuma ta sanya kafar wando daya da su.

Matasan sun hada da:

1. Burakita Dorayi
2. Messi Kantudu
3. Danbos Dala
4. Ado Runtu Bachirawa
5. Baffa Killer M/Tanko
6. Kamilu Duna Adakawa
7. Cile Maidoki T/Fulani
8. Huzaifa Yola
9. Hantar Daba K/Diso
10. Nasir Nasiru Zango
11. Nazifi Nanaso Zango
12. Sharu Ali Sharifai
13. Ma'aruf Goma
14. Bahago K/Bulukiya
15. Zubairu Mai dala
16. Sharu Gambo

Kwamishinnan Yan Sandan Jahar Kano CP Muhammad Usaini Gumel shi ne ya bayyana sunayen yayin da yake holon wadanda ake zargi da aikata laifuka daban - daban su 108.

Address

Birnin Katsina
Katsina
LABARUDADUMI-DUMINSU

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausa Post:

Videos

Share