05/10/2023
NRC Ta Dakatar Ma’aikacinta Kan Karbar Kudin Fasinja Ba Bisa Ka’ida Ba.
Biyo bayan zargin da ake yi wa wasu daga cikin ma’aikatan hukumar kula da sufurin jiragen kasa (NRC), da suke aiki a tashar jirgin kasa ta Obafemi Awolowo na kyale fasinjoji hawan jirgin kasa daga jihar Legas zuwa Ibadan ba tare da sun sayi tikiti ba, mahukuntar hukumar, sun dakatar da wani ma’aikaci da faifan bidiyo ya fallasa shi yana karbar kudin hawa jirgin daga hannun wasu fasijoji.
Faifan bidiyon wanda ya karade shafukan sada zumunta, ya bayyana ne, ranar 2 na watan Okutobar 2023, wanda ya nuna ma’aikacin na shawartar wasu fasinjojin cewa, ba sai sun sayi tikitin kafin su hau jirgin ba, amma ya daidaita da su yayin da s**a shiga cikin jirgin.Kazalika, sama da fasinjoji 60 ne aka yi zargin cewa, ko wannensu, ya biya kudi Naira 3,600 kafin su shiga jirgin daga tashar Obafemi Awolowo.
A cikin wata sanarwa da mataimakin mai hulda da jama’a na hukumar, Mista Yakub Mahmood, ya rattabawa hannu ta ce, an dakatar da ma’aikacin har sai kwamitin bincike, ya gabatar da rahotonsa a kan zargin.
Yakub, ya danganta laifin da ake zargin ma’aikacin a matsayin saba wa dokoki da ka’idar da hukumar ta gindaya.Bugu da kari, ya shawarci fasinjoji da ke son yin tafiya a cikin jirgin kasa, da su tabbatar sun sayi tikiti kafin su shiga cikin jirgin.
Ya ce, duk wani ma’aikacin hukumar da aka k**a ya na karya dokar hukumar, za a hukunta shi k**ar yadda doka ta tanada.
Abubakar Abba Leadership Hausa.