28/06/2024
Assalamu alaikum
UPDATE! UPDATE!! UPDATE!!!
Kamar yanda nake ta faɗa, a duka minings da muke yi a telegram, kaf babu wanda ya kai Hot use case da kuma potential, kuma tabbas za'a samu alkhairi akansa in sha Allahu ba kaɗan ba.
A yanzu haka Hot wallet sun samu nasarar ɗora blockchaina guda uku kenan akan wallet nasu.
Na farko dama sun fara ne akan Near Protocol Wanda blockchain mai ƙarfin gaske da usecase mai ƙarfi.
Sai blockchain na biyu shine Base, wanda blockchain mallakin mamallakan babbar exchanger a duniya ta Coinbase. Coinbase suna daga cikin jiga-jigai a duniyar crypto da blockchain, wanda reshensu na coinbase ventures suna daga cikin investors din da ake auna girman project indai aka ga sun saka masa kuɗi. Sannan ɗora blockchain nasu na nufin zaka iya da mu'amala da Ethereum ecosystem akan Hot wallet.
Sai blockchain na uku wato Solana, Wanda ba ɓoyayye bane a duniyar crypto. Yana daga cikin Blockchain da s**a fi kowane blockchains saurin gudanar da transactions da sauri (tps). Sannan suke da jahilan masu kuɗi da suke transactions akan blockchain din.
Ku sani ita fa Hot wallet, Sha ƙundum ce, dalilin faɗar haka kuwa shine; ita wallet ce akan kanta, sannan akwai ɓangaren exchange (DEX) akanta, da launchpad da launchpool, ga bridge, ga kuma tsarin Decentralized Autonomous Organization wato DAO, wanda wannan kowanne daga ciki usecase da zai saka project yayi muguwar daraja a samu alkhairi.
Misali, duk darajar Uniswap da pancake swap iya Dex ne kawai, duk darajar coin na Trust wallet iya coins ake ɗorawa a ajiye akanta, duk darajar da ake tunanin Orbiter finance coins dinsu zai yi, iya bridge kawai gare su. Akwai babban project na MakerDAO suna da tsari na supporting DAO ecosystems ne kawai. Amma ko kasan nawa ne coins na wannan projects din (UNI=$9.5, Cake = $2.1, TWT = $1 etc.)
Bana son over hyping na project, but ina da yaƙini da kyakkyawan zato akan Hot 🔥 duba da yanayin abubuwan da suke ginawa, da kuma tokenomics nashi wanda shi kaɗai ma abin burgewa ne koda ace Hot bashi da usecase.
Allah ya nuna mana lokacin da zamu ga launching na $HOT kuma ya sa muna cikin wanda zasu amfana dashi.
Ɗan uwa har yanzu baka makara ba wurin mining Hot 🔥 idan sun rage maka mining power dinka, kawai ka nemi wani layin ka buɗe sabon telegram ka fara haƙo, dama babu wani abu na kirki da za'a sameshi cikin sauƙi, mafi yawan lokaci sai an ɗan sha wahala rai ya ɓaci.
Ga wanda basu fara ba link 👇👇👇👇👇
New generation Telegram wallet. Updates: