26/03/2023
BAYAN FADUWARSU ZABE,
IDAN WADANNAN ZARGE-ZARGEN SU KA TABBATA, WATAKILA GANDUJE DA IYALANSA SU SHA DAURI KAMAR GORO.
KU KARANTA KU JI
KASHI NA DAYA.
Wani binciken kwakwaf da na soma gudanarwa, jim kadan bayan bada sanarwar rangada Dakta Nasir Yusuf Gawuna da kasa, da kuma nasarar Abba Kabir Yusuf matsayin Gwamnan Jihar Kano, ya soma nuna alamar cewa da wahala Gwamnatin mai shigowa ba ta binciki Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje da iyalansa ba. Wannan bincike dai, mai Mujalladi goma, shafuka fiye da dari daya, zan cigaba da sakinsa da yardar Allah, sannu a hankali.
DA MA CAN CIKIN GIDAN DAKTA GANDUJE BA SU SO TAKARAR GAWUNA BA.
Majiyoyin boye da kuma wadanda su ka bayyana sun nuni da cewa dama iyalan Dakta Abdullahi Umar Ganduje, musamman Farfesa Hafsat ba su so Dakta Nasir ya zama dan takara ba. Idan za a iya tunawa da Farfesa Hafsat ta taba yin wani furuci da ke nuni da bukatar ta na ganin Hon Murtala Sule Garo ya zama dan takara karkashin Jam’iyyar APC. Sai kuma wata majiya ta tabbatar min da cewa, mutane sun gaya wa Dakta Ganduje idan aka dora Murtala, mutanen jihar Kano ba za su yi shi ba, domin Dakta Nasir Yusuf Gawuna ya fi shi gogewa, ilimi da kwarjini. A don haka a dole aka dora Gawunan.
GANDUJE DA IYALANSA BA SU TAIMAKI GAWUNA BA YADDA YA KAMATA A LOKACIN ZABE.
Wani jigo a cikin Jam’iyyar APC na jihar Kano, ya guntsa min cewa har zuwa ranar Juma’a 17/3/2023. wato jajibarin zabe, Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje bai saki kudaden da za a yi kai da komowan zabe ba ga ‘yan jam’iyyar ta APC ba.
Wani na kusa da Babban Darakta Kamfen na jiha, na Jam’iyyar APC Rabiu Sulaiman Bichi, da karfe takwas na dare na jajibarin zaben, ya shaidawa wannan bincike da na aiwatar cewa a wannan rana ta Juma’a 17/3/2023, Babban Daraktan ya shaida masa cewa ‘har zuwa lokacin ba a a saki kayan aiki ba (Kudi), a domin haka su cigaba da hakurin jira.
Wani kusa kuma a cikin Jam’iyyar ta APC a jihar Kano ya tabbatar min cewa ire irensa da yawa a ranar zabe, sun je rumfunan zaben ne matsayin ‘yan kallo ba domin su taimaki takarar Nasir Gawuna ba.
Ya ce ‘Ba mutum da aka ba wa naira ko daya, in ji shi. Wasu kuma an ba su kudaden domin ba wa ‘yan Jam’iyya, amma sun kwanta a kai sun ki su bada.
Ya ce, da karfe biyu na daren jajibarin zabe, aka yi masa sakon text a wayarsa ana gayyatarsa zuwa wani filin wata Makaranta, amma ya yi biris da sakon, sai da safe a ranar zabe ya je. ‘A lokacin da na je, aka ce za a ba ni wasu ‘yan kudade kalilan don rabawa ga ‘yan Jam’iyya. Ni kuma na ce, ba zan karbi komai ba, don gudun ka da a hada ni rigima da jama’a, ko mutunci na ya zube’, in ji shi. Ya ce haka ya yi tafiyarsa ya koma gida ba tare da ya taimaki Nasir Gawuna ba. Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin ta Ganduje ba ta yin komai da su.
TABARGAZAR DA AKE ZARGIN GWAMNA GANDUJE DA IYALANSA SUN TAFKA
Wani binciken da na aiwatar, mai tarin yawa ya bayyana yiwuwar watakila Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje da iyalansa da wasu mukarrabansa kalilan su fuskanci fushin sabuwar Gwamnatin NNPP jim kadan bayan an rantsar da Abba Kabir Yusuf.
Wani binciken gani har hanji da na aiwatar, ya yi nuni da zargin da ake yiwa Gwamna Ganduje da sayar da kadarorin Gwamnati daban daban, a cewar wadanda su ka yi fallasar domin azurta kan sa da iyalansa.
Wani babban Jami’i a cikin Gwamnatin ya shaida min cewa Gwamna na da iko akan filaye da ke fadin jihar da ya ke mulki, amma doka ce sayar da ginin Gwamnati. Amma a cewarsa Gwamna Ganduje ya sayar da gine ginen Gwamnati da su ka hada da Ma’aikatar Gona. Ya ce Gwamnan ya bada fulotai a harabar.
Ya cigaba da cewa, Gwamna Ganduje ya bada gefen Ganuwar Kano (BADALA), ga mutanen da su ka rika mayar da wuraren gidajen Mai.
Ya ce shi ma ginin Daula Hotel, wanda kaya ne na al’umma, Gwamnan ya bada shi ga wani fitaccen dan kasuwar Kantin Kwari. Ya ce a doka ba Gwamna ba shi da ikon sayar da ginin Gwamnati, sai dai a mayar da shi wajen amfanin al’umma.
Ya ce, a lokacin mulkin Gwamna Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya mayar da ginin na Daula Makaranta. Ya cigaba da cewa, Kwankwason ya mayar da ginin Hasana Sufi da ke hade da ginin Ma’aikatar ruwa ta jiha Makarantar ‘Yam mata. Ya ce, amma shi Gwamna Ganduje hatta gidan Rediyon Tukuntawa ya tashe shi daga aiki, ya raba Fulotai ga jama’a.
Jami’in Gwamnatin ya cigaba da nuna takaicinsa yadda Gwamna Dakta Andullahi Umar Ganduje ya kwashe watanni goma sha tara ba tare da ya bawa Ma’aikatun Gwamnati Overhead ba, wato kudaden tasarrufi na wata-wata. Har ya bada misali da wata Ma’aikata wadda akwai ofisoshin da rufinsu ya lalace, amma gwamnan ya yi kemadagas ya hana kudaden da za a gyara.
Ya ce, shi ma Mayankan nan mai tarihi da ke kan hanyar zuwa Panshekara wanda tsohon Gwamnan jihar Kano Alhaji Abubakar Rimi ya gina, shi ma sai da Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya wargaza shi. Mai fallasar ya yi zargin cewa Ganduje ya bada wannan wuri ga surukinsa dan uwan matarsa.
Ya ce sai da aka yi wata uku ana kwasar karafuna da injina ana fitar da su daga wurin. Ya tabbatar da cewa a kiyasi za a iya samar da fuloti sama da dari biyu a wurin.
Bari na tsaya anan, gobe zan cigaba da yardar Allah. Kafin nan, watakila Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano Malam Muhammad Garba, zai amsa kiraye-kiraye ko sakon kar-ta-kwana da na yi ta masa domin jin ta bakinsu.
Bala M Makosa
(Baban Haidar)