01/08/2023
KASAR NIJER TA DAUKO HANYAR SAMUN 'YANCI DAGA MULKIN MALLAKA
Ina daga cikin wadanda s**a zargi Sojan da ya jagoranci kifar da Gwamnatin Demokaradiyya a Nijer General Abdourahmane Tchiani a matsayin karen farautar Faransa, to amma bayan da naga abubuwa sun fara bayyana a zahiri da kuma tattaunawar da nayi da wasu daga Nijer, na fahimci wannan Sojan ba karen farautar Faransa bane
Don haka na fita daga cikin masu ganin Sojan a matsayin karen Farautar Faransa, asalima yana so ne ya jaddada kudurin Muhammad Bazoum na yanke alaka gaba daya tsakanin Nijer da Faransa don Nijer ta samu 'yanci, sannan har ya fara aiwatar da hakan ta hanyar rufe dukkan kamfanonin Kasar Faransa masu hakar sinadarin Uranium wanda ake hada makamashin Nukiliya da shi
Kuma sai gashi hatta su fararen hula dake Nijer din sun fara nuna cikakken goyon bayansu akan Sojojin da s**a kwace mulki, saboda suma sun gaji da mulkin mallakar da Faransa take musu
A yanzu haka, sanarwa ya fito daga Shugaban Kasar Algeria cewa zasu bawa Sojojin Nijer agaji idan ECOWAS da Faransa s**ace zasu kaddamar da hari, Algeria itace Kasa na biyu ko uku a karfin Soji a wannan nahiya tamu ta Afirka
Shi wannan tsarin Mulkin Demokaradiyya tun asali bai dace da Kasashen Afirka ba, adon turawa ne, mulkin Soja ba abin aibi bane idan Sojojin sun kasance masu kishi gaskiya da rikon amana
A mulkin Soja babu jan lokaci wajen aiwatar da abubuwa, sannan akwai tsaro, idan talaka ya samu tsaro ya je gona ya noma abincin da zaici ya rayu to bai da wata matsala
Kasar Mali tana daga cikin Kasashen da Sojoji s**ayi juyin mulki kuma s**a yanke alaka tsakaninsu da Faransa, yanzu haka al'amura sun fara daidaita a Mali
Yanzu abinda ya bayyana a garemu shine ECOWAS ne karyan farautar Faransa da take so ta tura yaran mutane Yaki a zubar da jini, don haka mu saka Nijer a addu'ah, Insha Allahu ba za'ayi Yaki ba, kuma Insha Allahu Nijer zata samu 'yanci daga mulkin mallakar Faransa
Muna rokon Allah Ya rusa mugun shirin Faransa a nahiyar Afirka