24/02/2022
Abubuwa 10 Da Kwankwaso Yai Magana akai yayin taron TNM yau a Abuja
A yau ne tsohon Gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso tare da wasu jiga-jigan yan siyasa s**a ƙaddamar da wata sabuwar Tafiyar siyasa mai suna The National Movement TNM domin samar da mafita a ga Nigeria.
A jawabin da ya fitar a a shafinsa na Twitter dazu Kwankwaso ya faɗi Jawabai 10 da ya gabatar a taron, wanda sune maƙasudi da manufar taron kamar yadda Legit Hausa ta rawaito.
Jaridar Amintacciya ta jiyo cewa Kwankwaso ya fara ne kamar haka.
1. Yace zanyi muku maraba da zuwa wajen wannan taro na dabam mai tarihi da ya tattaro mutane daga kusa da nesa – yara da manya – maza da mata da nufin sake gyara kasarmu Ina godiya da ku ka samu lokaci, ku ka halarci wannan taro.
2. Mun zabi ranar yau ta musamman 2/22/2022 domin tattaro mutane daga wurare, jam’iyyu, addinai, da kabilu dabam-dabam domin kaddamar da wannan gagarumar tafiyar siyasa da za ta canza akalar kasarmu, ta kuma ceto mu daga ha’ula’i.
3. An fara wannan tafiya ne a kakar 2021 lokacin ana fama da annobar COVID-19. Mun fara zama a karkashin lemar ‘Abokan Kwankwaso’ domin a nemawa Najeriya mafita. Mu na yi wa kanmu kallon jagorori bayan zamanmu ‘yan siyasa. Mu na da jama'a daga ko ina
4. A haka aka haifo wannan tafiya ta fadin kasar nan kamar yadda ku ke ganin an samu mutane daga ko ina a Najeriya da ketare. Mun ajiye siyasa, mun gayyaci jama’a daga kowace jam’iyya Dole mu kaucewa layin jam’iyyun da ake da su.
5. Mu na da mabiya a kowace mazaba a karamar hukuma da ke Najeriya Manufar wannan tafiya ita ce samar da kasa mai ‘yanci, adalci da dama ga al’umma domin a cin ma burin rayuwa. Abin da muka sa gaba su ne amana, gaskiya, kishin kasa, dsr.
6. Ana cikin fagamniya a dalilin matsalolin garkuwa da mutane, IPOB, Boko Haram da sauran masu tada zaune-tsaye da shugabanni s**a gagara shawo kansu. A shirye muke, mu yi maganin wadannan kalubale ba da karfin bindiga kawai ba.
7. TNM ta san da zaman masu kiran a barka Najeriya, da masu neman a sauya fasalin kasa ko a canza tsari. Duk za mu saurari kowa da nufin inganta rayuwar al’umma. Akwai bukatar a yi gyara a yadda ake kason dukiyar kasa a tsarin mulki. A ba mutane muhimmanci.
8. Ba a samun cigaba a Duniyar yau sai da ilmi da gina ‘Dan Adam. Tafiyar TNM za ta maida hankali wajen raya al’umma tare da adalci da ba kowa dama. Domin samar da ayyukan yi, ya wajaba a samar da abubuwan more rayuwa, a gyara masana’antu.
9. Za mu yi taka-tsan-tsan da dukiyar kasa, mu yi abin da ya kamata a game da bashin da ake bin mu. Mu na kuma kira ga al’umma su taya mu kokari wajen tabbatar da zabe mai nagarta tare da ba bangaren shari’a da majalisa cin gashin kansu.
10. Ina kira ga dinbin jama’a; ‘yan kwadago, matasa, malamai, manoma da kwararru duk su tashi domin a gyara kasa da su. Mu na yin kira ga mutane su daina zama a gefe su na kokawa da halin da ake ciki, dole mu tashi tsaye domin mu ceci kasar mu
Taron dai ya sami halartar manyan yan siyasa kuma ya sami goyon bayan tsofaffin Gwamnoni da yan majalisun tarayya Sanatoci da sauran su.
Kuma ana sa ran Ƙungiyar zata zama wata mahaɗa ta masu son kawo sauyi a Nigeria.
© Amintacciya News