Bollywood fans kofar kabuga

Bollywood fans kofar kabuga Home of Bollywood Latest News, Blockbusters, Superhit, Hit, plot and Average. Stay With us for the following update daily �

Wannan haka yake
29/01/2024

Wannan haka yake

BOLLYWOOD A RANAR BIKI KIRISIMETI.Bayan Film Din Babban Jarumi Shah Rukh Khan  Me taken Dunki ya Kawo 23cr a Ranar Bikin...
26/12/2023

BOLLYWOOD A RANAR BIKI KIRISIMETI.

Bayan Film Din Babban Jarumi Shah Rukh Khan Me taken Dunki ya Kawo 23cr a Ranar Bikin christmas, Inda Shima Babban Jarumi na tollywood Me taken Salaar ya kawo 13.50cr. Gaba daya Sun kawo 36.50cr a ranar hutun christmas Har Yanzu Film din Babban Jarumi Aamir Khan Me Taken Dangal wanda ya fita a 2016 Shine Yake Rike Da Mafi Karbar Kudi Ranar Bikin christmas Inda yake da 42cr. Shi Kuma Film din ranveer sigh me taken "83" ya zama mafi kaskanci wajen taka rawa (most dissapointed) ranar bikin christmas ya kawo 16cr a 2021.

A yau Alhamis Kayataccen Shirin da Aka Jima Ana Jira Me Taken Dunki ya Fita Wanda Babban Jarumi Shah Rukh Khan Ya Jagora...
21/12/2023

A yau Alhamis Kayataccen Shirin da Aka Jima Ana Jira Me Taken Dunki ya Fita Wanda Babban Jarumi Shah Rukh Khan Ya Jagorance shi tare Da Matashiyar Jaruma Tapse Pannu da Kuma Matashin Jarumi Vicky Khaushal Sannan Kuma Babban Director Rajkumar Hirani Wanda Yan Kallon s**ayi Imanin Baya Film din Banza Ma'ana Indai yayi film se ya samu karbuwa wajen yan kallo da masana domin yana girgiza box office tare da samun tsagaron yabo.
To yanzu ma haka ne ya fara da Dunki wanda ya fita yau Alhamis yana ta samun yabo daga masu sharhin film sedai be samu tikitin tanadin kallo ba kamar yanda sauran ragowar fina-finai Srk Guda Biyu S**a samu ba wato pathaan da jawan saboda ba irin na Doke-doke bane kamar yanda wasu suke bukata ba sedai kuma daman su fina-finan director rajkumar hirani haka yawanci suke idan mukayi da la'akari da na baya da yawa basa mugun kawo kudi ranar farko amma kuma suna rike yan kallo sosai ta yanda ake jimawa ana kalla dalilin tsarin kyawun labari Sannan Kuma Lokaci ne da za a shiga hutun kirsimeti duk da Akwai Film din Babban Jarumi na Tollywood Prabhas Raju Uppalapati da Babban Director Prashanth Neel wanda yayi KGF yanzu ma zai fitar da Film Me Taken Salaar Gobe Juma'a wanda har bangaren Hindi Za a sakeshi Bayan Can Kudancin sedai Bazai Hana Dunki Girgiza Box office ba bangaren hindi watau Bollywood.
Wani Rahoto dai ya tabbatar da tanadin tiikitin kallon Salaar ranar farko a india gaba daya yakai kusan 18cr amma iya na hindi 2cr ne inda shi kuma Dunki yake da 13cr gaba daya na india, l.

Yau Lahadi Gagarumin Film din Babban Jarumi Salman Khan Me Taken Tiger 3 Ya Fita Inda Masana da Yawa Suke Yabawa Wannan ...
12/11/2023

Yau Lahadi Gagarumin Film din Babban Jarumi Salman Khan Me Taken Tiger 3 Ya Fita Inda Masana da Yawa Suke Yabawa Wannan Film da Sunan Film din Doke-doke da Aka Shirya su S**a Shiryu Sedai Kuma An Masa Kasafi Me Yawa Kuma Acikin Dakon tikiti na Jiran Sabon film da Akeyi Bai Samu Damar Kafa Sabon Record ba Sedai Kuma Tunda Alamu Sun Nuna yayi kyau Indai Har Yan Kallo S**a Zuzuta Shi to Zai Muguwar Dagawa da Zata Saka ya fara Kafa Record.
Cikin Wannan Film Akwai Babbar Jaruma Katrina Kaif Wadda itama Ana Yabawa Yanda tayi Doke-doke Aciki Se Kuma Mugun Ciki Watau Emran Hashmi Shima An Yaba masa Daman Can Kuma Shi Salman Khan Indai a Wannan Fanni ne Na Doke-doke An Saba Yaba Masa .

08/11/2023

Ana ta Tsokace-tsokace Akan Gagarumin Shirin Jarumi Salman Khan Da Katrina Kaif Watau Tiger3 Wanda Aka Jima Ana Tsumayen sa Kuma Yau Saura Kwanaki 4 Kacal ya fita.
Ana Tunanin Bayan Fitowa ta Musamman da Jarumi Shah Rukh Khan da Hrithik Roshan Zasu yi a matsayin Pathaan da Kabir An Kara Mintina Biyu Akan Yanda Aka Sani Kuma Ana Tunanin Jarumi na Tollywood watau NTR shima zai fito Aciki Wanda Idan Hakan Ya tabbata to Zai Zama Film dinsa na Farko a Bollywood Kafin Wanda Akayi Tsammani Zai fito na Farko tare da Hrithik Roshan Watau War2. Yanzu dai Ana Nan Ana Gangami na Siyan tikiti na Tiger3 din Wanda Kuma Za a Shiga Lokacin Bikin Diwali.

Gaskiya film yana kasuwa
18/09/2023

Gaskiya film yana kasuwa

16/09/2023
GUGUWAR SABON FILM ƊIN SRK JAWAN. Bayan yau An Saki Shirin da Aka Jima Ana Tsumaye na Babban Jarumi Shah Rukh Khan Wanda...
07/09/2023

GUGUWAR SABON FILM ƊIN SRK JAWAN.
Bayan yau An Saki Shirin da Aka Jima Ana Tsumaye na Babban Jarumi Shah Rukh Khan Wanda Yanzu Duk Sinimu S**a Cika Domin Ganewa Idanuwansu, kuma da yawan manyan masana Film da kasuwanci sun yaba da wannan Film kuma kowa yana ganin Film ɗin zai kawo nasara sosai domin har an fara bashi yiwuwar kawo 600cr a karon farko na Film din Bollywood Abinda ba a taɓa ba, Sannan da yawa suna hasashen zai kawo kudin da ba a taɓa kawowa ba a ranar farko na Fina-finan Bollywood Wanda Daman tun lokacin booking na Tikiti Aka fara wannan tunanin na cewa zai iya kawo 70cr a ranar farko bugu da ƙari yau ranar bikin murnar haihuwar Abin bauta a Addinin Hindu watau Krishna ( Ana Kiran ta Janmashtami) tuni yau kasar India Ana Shan Wannan Biki.

01/09/2023
Zanso Nayi Film da Matashiyar Jaruma Alia Bhatt Amma ba Kamar yanda Ake tunani ba, wai cewa muyi soyayya na jarumi da ja...
31/08/2023

Zanso Nayi Film da Matashiyar Jaruma Alia Bhatt Amma ba Kamar yanda Ake tunani ba, wai cewa muyi soyayya na jarumi da jaruma ba, Kawai dai Kamar Matsayin Uba da 'ya Inji Babban Jarumi Sunny Deol Yayin da Aka Tambaye shi da Wace Jaruma Yanzu Yakeso yayi Film tare.
Jarumi Sunny Deol Yanzu haka Yana Cikin Farin ciki na Nasarar Film ɗinsa Gadar2 Wanda a Jiya Ranar ta 20 da Fita ya Kawo 8cr, inda ya zama Jimilla 474cr Wannan Film ana Saka Ran Cikin Karshen Makon nan Zai Haura 500cr Sannan Kafin Gama Kasuwancin sa Zai Iya Zama Film ɗin da Yafi Kowa ne Kawo Kuɗi a ɓangaren kasuwanci na Fina-finan hindu.

MUNA ƘARA MAIMAITAWA BOLLYWOOD TA DAWO:  Dream Girl 2 Shima Ya Fara Kasuwa da Nasara.A ɗan Lokutan Baya Bollywood  Tana ...
26/08/2023

MUNA ƘARA MAIMAITAWA BOLLYWOOD TA DAWO:
Dream Girl 2 Shima Ya Fara Kasuwa da Nasara.

A ɗan Lokutan Baya Bollywood Tana Shan S**a Akan Rashin Nasara da ta rinƙa yi har hakan ya zama kamar Abin tsokana ko kuma Rani Daga Masoya ɓangaren Fina-finai na Kudanci ( South Cinema) Duk da An Manta Ko Iya Haka Bollywood ta tsaya se an ɗau Tsawon Lokaci ba a Kamota ba.
Wannan Shekarar tazo da Abin mamaki wajen Samun Nasarori Sosai Tun Daga Kan Film ɗin Shah Rukh Khan Pathaan tun a January duk da Bayan Shi An Samu Manyan Jarumai Sun Fitar basu Nasara ba, Irin Su Akshay Kumar da Film ɗin Selfie, Sannan Ajay da Film Bholaa, Haka Salman Khan da Film ɗin Kisi ka Bhai Kisi ka Jaan, da Sauran su. Amma Kuma Yanzu Tun Daga Watan May da Aka Saki Film The Kerala story Aka Samu Nasara Sosai, Yanzu Haka An jera Fina-finai Masu Nasarar Gaske irin su Zara Hadke Zara Bachke, Satyaprem ki Katha, Rocky Aur Rani prem ki kahani, Gadar2 da OMG2 Sannan Jiya ma Da Aka Saki Dream Girl2 ya fara da Nasara ya kawo 10cr Wannan Film Zai Iya Haura Kasafin kudin da Aka Kashe masa tun a kwanaki 3-4 na Farkon sa.

Sannan Akwai Manya-manyan Fina finai da Ake Tunanin Zasu Samu Gagarumar Nasara Nan Gaba Musamman Jawan na Shah Rukh Khan da Tiger3 na Salman Khan.

Film ɗin Babban Jarumi Gadar2 Ya Samu Nasarar Shiga 300cr Club Bayan Jiya Juma'a Ranar sa ta 8 da Fita ya Kawo 20cr Wand...
19/08/2023

Film ɗin Babban Jarumi Gadar2 Ya Samu Nasarar Shiga 300cr Club Bayan Jiya Juma'a Ranar sa ta 8 da Fita ya Kawo 20cr Wanda ya Zama Jimilla 305cr, Yayin Da Shima Film ɗin Babban Jarumi Akshay Kumar Jiya ya Kawo 6cr Shima Jimilla 91cr.
Duk Fina-finai Biyun Zasu Ƙara Ɗagawa a Kasuwancin su na yau Asabar da Gobe Lahadi Kasancewar Ranakun Weekend Ana Hutu.

Jaruman Bollywood a 300cr da Adadin da Kowa Yake Dashi:-

Salman Khan-3
Aamir Khan-2
Ranbir Kapoor-1
Shah Rukh Khan-1
Sunny Deol-1
Hrithik Roshan-1
Tiger shroff-1
Ranveer Singh-1

AKSHAY KUMAR BAI KARBI KO KWANDALA BA A MATSAYIN KUDIN AIKINSA NA FILM DIN OMG 2OMG 2 fim ne da Amit Rai ya bada umarni,...
18/08/2023

AKSHAY KUMAR BAI KARBI KO KWANDALA BA A MATSAYIN KUDIN AIKINSA NA FILM DIN OMG 2

OMG 2 fim ne da Amit Rai ya bada umarni, sannan jarumai irinsu Akshay Kumar, Yami Gautam, da Pankaj Tripathi s**a jagoranta. Fim din ya bada mamaki wajen kawo kudi da yayi, a inda ya kawo 85.05cr a satinsa na farko duk da guguwar Gadar 2 data mamaye India. Ana sa ran fim din zai shiga rukunin finafinai da s**a kawo 100cr a gobe asabar a inda zai zama fim din jarumi Akshay Kumar na 17 da ya kawo 100cr. Yayin da OMG 2 ya riga ya zama CLEAN HIT akwai jita-jita da ke yawo a cikin kafofin watsa labarai game da kasafin kudin sa. Akwai wani sashe a shafukan sada zumunta dake cewa an yi fim din ne akan kasafin kudi har 150cr.

Jaridar Pinkvilla ta tabbatar da cewa alkaluman da ke yawo a kan budget din fim din ba gaskiya bane. Furodusan fim din kuma shugaban kamfanin VIACOM 18 COO wato Ajit Andhare shine ya tabbatar da hakan. Ba tare da yin cikakken bayani ba, ya ce, “Rahotanni na kasafin kudin OMG 2 sun wuce gona da iri. Akasin haka, Akshay bai yi cajin sisin kwabo ba a matsayin kudin aikinsa kuma a zahiri, ya bamu gudunmuwa sosai tun daga kan gudunmuwa ta kudi har zuwa ta sauran abubuwa da s**a danganci film din". Ya cigaba da cewa, "Muna da dogon tarihi da fahimta tare da Akshay Kumar tun lokacin finafinai irinsu OMG 1, Special 26, da Toilet: Ek Prem Katha. Ba tare da shi ba, wannan film ba zai yiwu a shirya shi ba".

Wata majiya dake da alaka da cigaban shirin ta sanar da Pinkvilla cewa kasafin kudin OMG 2 bai wuce 50 crore ba. "An dauki shirin OMG 2 a cikin yanayi wanda ba sai an kashe masa kudi dayawa ba, kamar yawancin finafinai na zamantakewa da ake yi a masana'antar finafinai ta Hindi. Budget din kadan ne kasa da 50 crore. Ga wadanda ba su sani ba, ko da OMG 1 an yi shi ne akan kudi 25 crore kawai” majiyar ta gaya wa Pinkvilla.

SALEEM

LABARI ZAI IYA SHAN BAN-BAN KO KUMA ZAI MAIMAITA KANSA?A Zamanin Baya Wajen 90s Lokacin Ana Bukatar Fina-finai na Doke-D...
09/08/2023

LABARI ZAI IYA SHAN BAN-BAN KO KUMA ZAI MAIMAITA KANSA?

A Zamanin Baya Wajen 90s Lokacin Ana Bukatar Fina-finai na Doke-Doke A 1996 Jarumi Sunny Deol Ya Saki 'Ghatak ' Suma Sunil Shetty da Akshay Kumar Sun Saki 'Sapoot' Inda Sunny Ya Samu Nasara Ghatak ya Kawo 15cr ya Zama Super hit, Yayin da Sapoot na Akshay Kumar da Sunil Shetty ya Kawo 6cr ya Zama Flop.
Yanzu Munzo daf da Kwanan Wata 11, ga August Za Asaki Film ɗin Sunny Gadar2 da Film ɗin Akshay OMG2, duk a Rana Ɗaya.

Waye Kuke Ganin Zai Tafi da Wannan Nasarar?

Yayin da Babbar Jaruma Kajol take Cika Shekaru 49 a Duniya yau, An Bada Wani Labari Lokacin da Ta Fara Jin Kanta ta Zama...
05/08/2023

Yayin da Babbar Jaruma Kajol take Cika Shekaru 49 a Duniya yau, An Bada Wani Labari Lokacin da Ta Fara Jin Kanta ta Zama Wata a Bollywood Shi Kuma Babban Me Bada Umarni Sanjay Leela Bhansanli Shi Ba Kowa bane Lokacin Zai Fara Bada Umarni da Wani Film Me Taken Khamoshi Ya Fara Nuna Ra'ayinsa Akan Jaruma Kajol Itace Farkon Zaɓinsa Hakan Yasa Ya Neme ta Kuma ya Nemi Tsowuwar Jaruma Mahaifiyar Jarumar Watau Tanuja itama ta yarda Duk A Wajen 1996 ne, Bayan Sunyi Magana da Kajol tace Masa Zasuyi Wannan Tattaunawar a Wani Hotal Hakan Yasa Sanjay Leela Bhansanli ya Hau Jirgi ya tafi Wannan Wajen da S**ace Zasu Haɗu su tattauna.
Bayan yaje Mintina Shiru, Ɗan Lokaci Shiru, Awanni Shiru, Har Awanni 8 Shiru, Kawai Se ya Kirata a Waya Se Take Ce Masa Ita Kwata-kwata ta Manta Da Batun Haɗuwarsu.
Daga Karshe dai Ya Maye Gurbin ta da Manisha Koirala.
Har Yanzu Idan a Bollywood Ana Maganar Manyan Masu Bada Umarni Waɗanda Kowa Yakeso Suzo da Film To Se An Saka Sanjay Leela Bhansanli.

Jaruma Deepika Padukone tace Mijinta Ranveer Singh Shi Kaɗai ne Zai Iya Irin Wannan taka Rawar da Akayi Cikin Sabon Film...
30/07/2023

Jaruma Deepika Padukone tace Mijinta Ranveer Singh Shi Kaɗai ne Zai Iya Irin Wannan taka Rawar da Akayi Cikin Sabon Film ɗin sa tare Alia Bhatt Me Taken Rocky Aur Rani ki Prem Kahani Watau "Labarin Soyayyar Rocky da Rani" Wanda ya fita.
Yayin da ya Ɗora Wani Ɗan video da Suke Yin Wata Fitattaciyar Waqa ta Film ɗin, Waqar me taken (What Jhumka) Shi da Ita Bayan sun Gama Kallon Film ɗin. A karshen video ɗin take cewa Kai ne Kaɗai Zaka Iya, Shi kuma Yayi Rubutu yana Murna Cewa Matarsa taso Wannan Film da kuma Aikinsa ( Hakan Shine Alfaharinsa) a Yanda yake Nunawa.

ƳAN SIYASA NE SUKE RURA WUTAR ƘIYAYYA TSAKANIN ƘASASHE BIYU INDIA DA PAKISTAN A CEWAR SUNNY DEOL:Bayan An Saki Tallar Ga...
27/07/2023

ƳAN SIYASA NE SUKE RURA WUTAR ƘIYAYYA TSAKANIN ƘASASHE BIYU INDIA DA PAKISTAN A CEWAR SUNNY DEOL:

Bayan An Saki Tallar Gagarumin Shirin da Aka jima Ana Tsumaye na Babban Jarumi Sunny Deol Watau Gadar:2, Jarumin ya Bayyana cewa Lallai Mutanan ƙasashe Biyu na India da Pakistan su tuhuma Ƴan Siyasa Akan Amfani dasu Wajen Saka Ƙiyayya a Tsakanin su, su suke wasa da Hankalinsu domin duk kasashen suna bukatar zaman lafiya kuma duk ɗaya suke hakan kuma ya nuna acikin wannan Film.
Jarumi Sunny Deol dai Shima ɗan Siyasa ne Kuma ɗan Majlisa ne.

  is 400 NOT OUT… Remains an UNSTOPPABLE FORCE, packs a MASSIVE ₹ 63.50 cr in Weekend 2 [ ]… EXCELLENT jump on [second] ...
06/02/2023

is 400 NOT OUT… Remains an UNSTOPPABLE FORCE, packs a MASSIVE ₹ 63.50 cr in Weekend 2 [ ]… EXCELLENT jump on [second] Sat and Sun adds power to the BIG TOTAL… [Week 2] Fri 13.50 cr, Sat 22.50 cr, Sun 27.50 cr. Total: ₹ 414.50 cr. . biz.

+ [Week 2]: Fri 50 lacs, Sat 75 lacs, Sun 1 cr. Total: ₹ 15.40 cr.

⭐️ NOTE: + + *combined* biz: ₹ 429.90 cr. biz. Nett BOC.

Pathaan (in four days)India Nett :219 crOverseas: 164Worldwide Gross: 429 cr India Nett :257.44 crOverseas:112.32WW:418....
29/01/2023

Pathaan (in four days)
India Nett :219 cr
Overseas: 164
Worldwide Gross: 429 cr


India Nett :257.44 cr
Overseas:112.32
WW:418.80 cr

Domestic:Nett 240.54 cr
Overseas:57.06 cr
WW:343.42 cr

Domestic Nett:252.9 cr
Overseas:43.39 cr
WW:340.92 cr

26/01/2023

Hindustan Zindabaad Hai….Zindabaad Tha...aur Zindabaad Rahega!
This Independence Day, we bring to you the biggest sequel in Indian cinema after two decades.
releasing on 11th August 2023🔥



Sunny Deol Utkarsh Sharma Anil Sharma Productions LLP Mithoon Sayeed Quadri Simrat Kaur Manish Wadhwa Zee Music Company ZEE5 ZEE Cinema

26/01/2023
TEAM SRK FANS NIGERIA CELEBRATED PATHAAN'S SUCCESS.Wani Hoto Yayin Taya Gagarumin Shirin Film ɗin Shah Rukh Khan Murna W...
25/01/2023

TEAM SRK FANS NIGERIA CELEBRATED PATHAAN'S SUCCESS.

Wani Hoto Yayin Taya Gagarumin Shirin Film ɗin Shah Rukh Khan Murna Watau Pathaan Wanda Ya Fita Yau ɗin nan Kuma Aka Samu Abinda Akeso.

LABARI ME DAƊI GA MASOYA SRK DA MA BOLLYWOOD GABA ƊAYA:Bayan Nasarar Irin Yanda Sabon Film ɗin Babban Tauraro Shah Rukh ...
25/01/2023

LABARI ME DAƊI GA MASOYA SRK DA MA BOLLYWOOD GABA ƊAYA:

Bayan Nasarar Irin Yanda Sabon Film ɗin Babban Tauraro Shah Rukh Khan Me Taken PATHAN Yake Samu Tun Daga Yanda Ake Booking na Tikiti Domin Ya Karya Kusan Duk Wannan Rekod ɗin To Yanzu Haka Ya Fara Samun Yabo Musamman Daga Bakin Wannan Shahararren Masani Kasuwanci da Abinda Film Ya ƙunsa Watau Taran Ya Bashi Star 4.5/5 Yace Wannan Film Kome Nasa Yayi Sannan Har ma Abin da Ba Ayi Zato ba Na Kyawun Film Akwai Shi Lallai Srk Ya Dawo Da Ƙafar Dama Kuma Wannan Nasara ce ga Bollywood Matuqa Domin Ana Ganin Sun Kwanta Dama Bayan Nasarar Drishyam2 to Pathan Zai Ƙara Wata Domin Shi Ana Ganin Zai Kawo 50+ cr To Tunda ma Ya Fara Samun Wannan Yabon Zai Iya Kawo 60+ cr a India Sannan Duk Duniya Zai iya Kawo 100+cr.

25/01/2023

...
: BLOCKBUSTER.
Rating: ⭐️⭐️⭐️⭐️½
has it all: Star power, style, scale, songs, soul, substance and surprises… And, most importantly, , who’s back with a vengeance… Will be the first of 2023.

Chief minister Himanta Biswa Sarma Yace Ya Samu Kiran Waya Na Cikin Dare Misalin ƙarfe 2am Daga Jarumi Shah Rukh Khan Ga...
23/01/2023

Chief minister Himanta Biswa Sarma Yace Ya Samu Kiran Waya Na Cikin Dare Misalin ƙarfe 2am Daga Jarumi Shah Rukh Khan Game da Zuwa Inda Ake Gwajin Kallon Film ɗinsa Pathan da Zai Fita Ana Ƙona Fastocin da Barazana a Wajen Yace Jarumin Ya Nuna Damuwarsa Kan Haka Inda Shi Kuma ministan Ya Tabbatar Masa da Cewa Wannan Birnin na Guwahati ɗin da Yake Ƙarƙashin Gwamnatin sa Zai Tabbatar Yayi Amfani da Doka da Oda Kan Kowa Ba Tare Da Ancutar da Kowa ba da Kuma Film ɗinsa.

Pathan dai Yau Saura Kwana 2 Ya Fita Kuma Tuni Mutane Suna Ta Rububin yin booking na Tickets Domin Alamu Sun Nuna Cewa Zai Kawo Kuɗi a Ranar Farko Kusan Irin na Film ɗin WAR da KGF2.

KARTIK AARYAN YA TSORATA DA MARIN DA YAYIWA PARESH RAWAL CIKIN SHEHZADA.Bayan An Saki Tallar Film ɗin Matashin Jarumi Ka...
12/01/2023

KARTIK AARYAN YA TSORATA DA MARIN DA YAYIWA PARESH RAWAL CIKIN SHEHZADA.

Bayan An Saki Tallar Film ɗin Matashin Jarumi Kartik Aaryan Me Taken SHEHZADA Aciki Akwai Inda Matashin Ya Mari Tsohon Jarumi Paresh Rawal.

Kartik Aaryan Yace Wannan Wajen Ya Tsora tashi Amma Yana Godewa Tsohon Jarumin Kan Shi Ya Ƙara Masa Karfin Gwiwa Akan Ya Aiwatar Domin Shi Yace Masa “Tu Tension mat lena. Kheench ke maarna. Film ke mood mein
jaana.. Ma'ana Karka damu Kawai Ka Dakeni Ai Duk Yana Cikin Yanayin Tsarin Film.

Wannan Film Ya Hada Da Wasu Jaruman Kamar Kriti Sinon, Monisha Koirala da Ronit Roy.

Matashiyar Jaruma Alaya F. Ta Samu Damar Fitowa Cikin Qayataccen Film da Ake Shiryawa Babban Jarumi Akshay Kumar da Mata...
09/01/2023

Matashiyar Jaruma Alaya F. Ta Samu Damar Fitowa Cikin Qayataccen Film da Ake Shiryawa Babban Jarumi Akshay Kumar da Matashin Jarumi Tiger Shroff Me Taken Bade Miyan Chote Miyan Wanda Babban Director Ali Abbas Zafar Zai Bada umarni.

Alaya F Ƴar Gidan Jaruma Pooja Bedi ce Wadda Tafito Cikin Jo Jeeta Wohi Sikandar na Jarumi Aamir Khan ce, Kuma Wannan Yarinya Ta Fara Fitowa Tare Da Jarumi Saif Ali Khan Cikin Fim Jawani Janiman Shekara 2020.

Yanzu Haka Wannan Yarinya Fina-finai ɗin ta Kusan Guda Huɗu ne Zasu Fita Har Wannan Sunkai Guda Biyar.

Wannan Film Bade Miyan Chote Miyan Yana Ɗauke da Gwarazan Jarumai Kamar Haka :-Akshay Kumar, Tiger Shroff, Prithviraj Sukumaran, Sonakshi Sinha , Manushi Chhillar da ita Alaya F.

Acikin Wannan Watan Ake Tunanin Fara Aikin sa Kuma Film ne da Za Ayi Hatsabibanci da Tashin Hankali da Doke-Doke.

SAM SAM BAZAMU YARDA AAMIR KHAN YA TAFI HUTU BA: WASU MANYAN MASU SHIRYA FILMS.Babban Jarumi Aamir Khan Yana Bawa Film L...
04/01/2023

SAM SAM BAZAMU YARDA AAMIR KHAN YA TAFI HUTU BA: WASU MANYAN MASU SHIRYA FILMS.

Babban Jarumi Aamir Khan Yana Bawa Film Lokaci Maqura Wajen Tsara Shi Da Zuwan Ƴan Kallo Ta Inda Sukeso Hakan Ne Yasa Yake Yawan Karya Rekod Amma Duk da Haka Yayi Rashin Nasara Gagaruma Bayan Ya Saki LAL SINGH CHADDHA Karkashin Kamfanin sa Aamir Khan Productions Bayan Ƴan Kallon India Sunƙi Su Kalla a Sinimu, Kwanaki Yace Zai Zauna Da Iyali Ya Huta.

Amma Kuma Wasu Labarai da Suke Zuwa Shine Manyan Masu Shirya Fina-finai na Kudancin India Suna so Suyi Masa Film.

Na Farko Wanda Yayi Film ɗin KGF na 1 da na 2, Yace Yanaso Ya Haɗa Aamir Khan da NTR a Wani Gagarumin Shiri Wanda Akayi Masa Kasafi Me Girma Kuma Tuni Sun Sanar da Wannan Film Amma Dai Shi Aamir Khan Be Tabbatar Zaiyi ba Zuwa Yanzu.

Sannan na Biyu Shine Sanannen Mashiryin Film Wanda Yayi Ghajini watau Madhu Mantena Yace Yana da Burin Yin Ghajini na 2 Kuma Aamir Khan Yakeso Ya Fito.

Akwai Wani Fitaccen Mashiryin Film da ba a Bayyana Sunan sa Amma Shima Yana Nan Yana Ƙoƙarin Yiwa Aamir Khan Film Indai Kuwa Hakan Ya Tabbata Koda Guda Ɗaya ne Ko Biyu To Babu Batun Hutu ga Wannan Jarumi.

ABIN YA TADA HAZO:An yi Caraf An Lalubo Wani Video da Babban Director Na Masana'antar Tollywood Watau SS RAJAMOULI Bayan...
03/01/2023

ABIN YA TADA HAZO:

An yi Caraf An Lalubo Wani Video da Babban Director Na Masana'antar Tollywood Watau SS RAJAMOULI Bayan Shekaru Kaɗan da fitar Dhoom2 na Jarumi Hrithik Roshan Yake Furta Cewa Yana Mamakin Kuranta Bollywood da Ake Cewa Tafi Tollywood Sannan Hrithik Ba Kome Bane a Gaban Jarumi Prabhas ba.
Domin Ya Kalli Fastocin Film ɗin Billa Wanda Lokacin 2009 ne Yace Ya Ƙara Yarda Da Prabhas Ba Za a haɗashi da Hrithik ba Saboda Prabhas Yana Kyawun Fuska Shima Sannan Ya iya Film ɗin Rigima ( Action) Haka Duka Wannan Director Ya Faɗa.

Sedai Mutane da Yawa Sunce Hakan Ya Bayyana Daman Wannan Director Yana Da Wani ƙulli Ko Hassada Ga Masana'antar Bollywood Sedai Kuma Shi Kansa Wannan Film na Billa da yake Zugawa Remake ne na Film din SRK Watau DON sannan Shi Kansa Jarumi Hrithik Roshan da Aka Haɗashi da Prabhas Ba A Ɓangaren Action Hrithik Ya Tsaya ba Domin Ana Yaba Masa da a Kowanne Fanni Idan An Ɗora shi Saɓanin Prabhas ɗin.

Wannan Video Yana ta yawo a Kafar Sadarwa Kuma Mutane Suna Raddi Tare da Mamakin Mutum Kamar Ss Rajamouli Yana Irin Wannan Zance Duk da Yanzu Abin Ya Bayyana.

RANBIR KAPOOR: 'ANIMAL' FIRST LOOK IS HERE...   in  , directed by   [ ,  ]… 11 Aug 2023 release [  weekend]… In  ,  ,  ,...
31/12/2022

RANBIR KAPOOR: 'ANIMAL' FIRST LOOK IS HERE... in , directed by [ , ]… 11 Aug 2023 release [ weekend]… In , , , and .

also stars , , and … Produced by , , and .

Address

Kofar Kabuga
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bollywood fans kofar kabuga posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Bollywood fans kofar kabuga:

Videos

Share


Other Kano media companies

Show All