19/05/2023
JUMA'A PROMO
FAHIMTAR SUFAYE AKAN RAHMAR ALLAH
Sufaye suna rayuwa ne bisa hadisin Annabi SAW da yake cewa "Ku sauƙaƙa, kar ku tsananta, kuyi bushara, kar ku tsoratar/kore", Shiyasa a cikin dukkan ilimomin su da tarbiyar su, ƙkokari suke su isar da bushara ga bayin Allah, cikin hanya mai sauqi ba mai tsanani ba.
Haqiqa Allah maɗaukakin sarki, rahmarsa ta fi azabar sa yawa. Saboda haka ne sufaye suke yi masa kyakkyawar zato cikin dukkan ayyukan su na saɓo ko ibadah, Domin Shi Allah, Gwargwadon yadda bawa ya ke tsammanin sa, haka zai same shi.
Idan Allah SWT yace ba zai karɓi ibadar wanda ya sha giya ba tsawon kwana arba'in, ko ibadar mazinaci, ko wanin su, toh wani irin kwanaki yake nufi?
A wurin Allah dai, kwanan sa ɗaya, itace shekara dubu daya a wannan duniyar tamu, k**ar yadda yazo cikin Qur'ani, sura 32, aya 5: Yanã shirya al'amari daga sama zuwa ga ƙasã, sa'an nan (Al'amarin) ya tafi zuwa gare Shi a cikin yini guda, wanda gwargwadonsa shẽkaru dubu ne akan abin da kuke lissafãwa (kwanakin ku).
Ashe wanda Allah ba zai karɓi ibadar sa na kwana arba'in ba, shekaru 40,000 kenan irin namu za a ɗauka ba a karɓar ibadar sa, haka ne?
A'a!
A wurin sufaye, duk hukuncin da Allah SWT ya ambata na fushi/azaba akan bayin sa, suna yiwa Allah kyakkyawar zato wurin yawaitar rahmarsa akan Al'ummar Annabi SAW da saurin afwarsa garesu. In akace kwana arba'in, a wurinsu, mafi ƙkarancin ƙirga shine second arba'in, dan haka second Arba'in za ayi ba a karɓi ibadar mashayin giya ba.
Kai! A Wurin manyan sufaye ma, basa ganin kyakkyawa ko mummunar aikin su, ballantana su ga lada ko zunubi. Suna tuba ne ga Allah bisa ganin kansu yayin aiwatar da aikin, suna godiya ga Allah ne in s**a gane Allah shine mai aikin.
Ina Gayyatar duk wani mai munin hali/aiki zuwa ga Ɗariqar Tijjaniya, inda zai samu gafarar laifinsa komi girmansa cikin second ɗaya, kuma Allah zai bashi kariya daga yin mummunar ƙarshe, yakuma tashi a Fadar Ma'aiki S.A.W
✍ Jakaden SaiyidaJakaden Saiyida Fadima Tv.Jakaden Saiyida Fadima Tv.Jakaden Saiyida Fadima Tv.