
20/04/2024
Ruwan Fanfo...
Dole muyi ma'aikatar wannan bawan Allan uzuri,
Domin nasan shi nasan jajircewar sa akan dukkanin abinda yasa gaba,
Nayi tafiya a yan kwanakin nan canma na tarar da babban birnin jihar yana fama da matsalar ruwa,
Sai na fuskanci matsalar ruwan nan kamar tana da alaka da rashin wadatuwar hasken wutar Lantarki da Kuma zafin rana,
A jihar Kano akwai matsalar Lalacewar manya manyan injina dake turo ruwan daga manyan dams zuwa cikin gari kuma na tabbata Maigirma kwamishinan ruwa yana iya kokarin sa akan Lamarin,
Domin akwai wuraren da sukai shekara da shekaru basu da ruwa amma a yanzu haka ruwa yaje musu,
Wannan kadai ya Isa mu fahimci kokarin da Maigirma Kwamishinan Ruwa Dr Ali Makoda yake akan wannan al'amarin,
Allah SWT ya cigaba da dafa masa domin shawo kan wannan matsalar..
Sageer Skeeper ✍️