21/10/2024
KASHEWA MACE KUƊI ALAMA CE TA RASHIN SANIN DARAJAR KAI DAKUMA LALACEWA.
Mazaje ku saurareni da kyau. Idan kana tunanin kashewa mace kuɗi shine zai saka ta girmama ka, to ka sake tunani. Ƙarya ake yi maka, zuƙi ta malle ake yayyafa mana cewa mata suna durƙusar da kansu a ƙasan wanda yake kashe musu kuɗi wajen siyan abu mafi tsada, ɗaukar su zuwa gidan abinci mai tsada, dakuma yi musu yayyafi da kuɗi.
WALƘIYA. baza su taɓa girmama ka ba saboda haka. Hasali ma saidai su kalle ka a matsayin shashasha sakarai. Sannan kai ɗin ba kowa bane ba face ATM ma tafiya a idanun ta.
Bari in yi maka gwari-gwari: ba zaka taɓa burge mace ba saboda adadin kuɗin da kake kashe mata ba, eh zasu iya yin murna da murmushi, suyi maka fari da ido, suyi maka godiya cikin tausasan kalamai masu daɗi, amma a can ƙarƙashin zuciyar su sunsan menene abinda yake faruwa.
Kana siyan kulawar su, lokacin su, kulawar su dakuma alaƙar su. To kasani cewa Mata suna girmama wanda yake umarni da girmamawa ne ta hanyar amfani da halaye tsayayyu da ƙarfi tare da manufa. Bawai wanda yake buɗe bakin aljihun shi ba.
Yayin da ka jefeta da kuɗi, to anan take kana tura wani saƙo ne wanda yake nuna gazawar ka a sarari tare da ƙoƙarin siyan yarjewa daga gare su. Amma kuma kasan me?? Babu wanda yake girmama namijin da yake ƙoƙarin siyan yarjewa. Zaka iya shinshino bijerewa daga wajen mace tun tana da tazara mai nisa.
Sannan adadin kuɗin da ka kashe mata?? Adadin rashin girmamawar da zaka gani daga gare ta. Zata karɓe kyaututtukan, zata morewa abincin, sannan ta ɗauki hoto tana murmushi harma ta turo maka. Amma a can ƙasa dariya take yi maka. Kai din ba kowa bane ba face wani lusari cikin jerin lusaran da suke kashe mata kuɗi.
Ka tsaya kayi tunani da kyau. Yaushe ne lokaci na ƙarshe da ka girmama wanda ya jefeka da kuɗin da yasha wahalar nema batare da wani dalili ba? Babu ko? To k**ar haka ne. Suma mata haka ne ta bangaren su. Zasu kwashi abinda zasu kwasa, amma GIRMAMAWA? wannan kana iya samun ta ne ta hanyar aikin ka, burin ka dakuma adadin yadda kake girmama kanka.
Namiji mai daraja wanda yasan ƙimarshi baya bukatar sai ya kashe kuɗi kafin mace ta kula shi. Yasan shi ɗin wanene sannan baya bukatar tabbatar da martabar shi da kuɗi. Ya himmatu wajen fafutukar shi ne. Yana gina goben shi ne sannan baya ɓarnatar da dukiyarsa domin burge mace, wadda Babu abin da zai samu a madadin kuɗin. Mazaje masu daraja suna kashe kuɗin su ne akansu, akan goben su dakuma abubuwan da zasu bayar da sak**ako. Ba wai akan murmushin da zai busar da aljihu ba.
A tunanin ka kana burge ta ne saboda sabuwar jakar daka siyo mata? Kokuma kuɗin anko ɗin daka bata? A'a sam sam, hasali ma tana tunanin yadda zata ƙara zage dantse ne wajen tatsarka dakyau. So take taga adadin malejin ka. Burinta shine nawa zata samu daga gare ka kafin ka farga ka waye. Sannan da zarar ka ankara SHIKENAN zata k**a gabanta. Ta tafi wajen wani sakaren na gaba wannan zai cigaba da biyan farashin. KADA KA SAKE KA ZAMA WANNAN SAKAREN.
Ka daina kasancewa dolon da yake kashe kuɗin shi akan mace da tunanin ai yana cin nasara ne akanta. Bata girmama hakan. Tana amfani da kai ne, tana yi maka dariya a bayan idonka, sannan da zarar ta gama dakai zata matsa izuwa wajen wani dolon wanda bai ankara ba.
Ka girmama kanka dakyau. Ka san kai wanene ta yadda zaka iya cewa A'A. Kuɗin ka naka ne, na kasuwancin ka ne, na ƙara bunƙasa kanka ne. Idan taƙi tsayawa saboda burin ka da manufar ka , to bata cancanci cin kuɗinka ba.
Saboda haka duk lokacin da mace ta ƙara yunƙurin gwada ka, tambayar ka kuɗin anko kokuma siya mata sabuwar waya, ka kalli cikin idanuwan ta kace mata KAI BA IRIN WANNAN SAURAYIN BANE. ka nuna mata cewa ƙimar ka bata da ma'aunin ta ɓangaren adadin kuɗin da zaka iya kashe mata. Sai dan kasancewar ka NAMIJI. idan ta cancanta to zata tsaya, idan kuma bata tsaya ba to ƙyale ta, sannan kayi murna ka kaucewa HARSASHI.
akwai abubuwa da yawa a gaban ka.
Ka rayu cikin aminci.
Ibrahim reco kano