Sen Barau Jibrin Online

Sen Barau Jibrin Online Duk abinda aka ji ko aka gani ko aka karanta ba umarnin Sen Barau Jibrin bane, illah soyayyar da ke tsakaninmu ta sa muka watsa akan wannan tasha.

Mawallafin tashar – Ibrahim Ali Ahmad

14/02/2025

Siyasa Rigar Ƴanci

25/03/2022
G7 adon APC, in ba ku ba APC - idan kun hadu APC ta gyaru!
01/03/2022

G7 adon APC, in ba ku ba APC - idan kun hadu APC ta gyaru!

Mai MAD'I tafi ka siyar tun mai ZUMA bai zo ba!
20/02/2022

Mai MAD'I tafi ka siyar tun mai ZUMA bai zo ba!

Al'ummar jihar Kano ta yi Allah wadai da uwar jam'iyyar APC ta KasaKotun daukaka kara karkashin masu shari'a 3 ta zauna ...
18/02/2022

Al'ummar jihar Kano ta yi Allah wadai da uwar jam'iyyar APC ta Kasa

Kotun daukaka kara karkashin masu shari'a 3 ta zauna a Abuja Alhamis 17/2/2022 domin yanke hukuncin shari'ar da tsagin gwamnatin Kano ta daukaka akan zaben shugabannin jam'iyyar a matakin mazabu da kananan hukumomi da kuma neman sanin ko babbar kotun da ta fara yin shari'ar tana da hurumin yin shari'ar ko bata dashi

A lokacin da suke yanke hukuncin, sun bayyana cewa, su kansu basu da hurumin sauraron wannan shari'ar ballantana babbar kotun da ta fara yin shari'ar, sakamakon haka, ta umarci a koma wajen uwar jam'iyyar ta kasa a sasanta da masu korafin tunda rigimace ta cikin gidan jam'iyya.

Babu inda kotun daukaka karar ta ambata wanda zai zama shugaban jam'iyya a kowane tsagi, haka kuma babu inda ta ambata wanda yayi sahihancin zabe a kowane tsagi ko akasin haka, bisa dalilin ta na rashin hurumin sauraron shari'ar kamar yadda ta fada tun da farko.

Babban abin mamaki da takaici, maimakon uwar jam'iyyar ta APC ta sake neman kowane tsagi domin a sake komawa teburin sulhu, duba da jadawalin da ta fara bujiro da shi tun farkon sulhun, yaci karo da adalcin yin sulhu a tsakankanin masu jayayya, abinda ya jawo bangaren G7 su ka yi fatali da shi kenan.

Sai kawai uwar jam'iyyar ta APC ta dauke kai daga umarnin da kotun daukaka kara ya bayar na a koma wajen ta domin sasantawa, kai tsaye ta dankawa tsagin gwamnati takardar shaidar zama shugaban jamiyya na jihar Kano, duba da yadda tsagin gwamnatin Ganduje su ka bayyana a kafafen sada zumunta na zamani suna cin mutunci da keta alfarmar tsagin G7, jim kadan bayan yanke hukuncin.

Idan ba'a manta ba, uwar jam'iyyar ta janye bada takardar shaidar cin zabe wato satifiket ga kowane tsagi a jihar Kano, duk da tasan wata babbar kotu tayi hukuncin bai wa tsagin G7 nasara, amma uwar jam'iyyar ta gaza mutunta wannan hukunci, kamar yadda ta mutunta sabon hukunci wata kotun a halin yanzu, kai tsaye ya nuna dama akwai wata kullalliya daga ita uwar jam'iyyar domin wofantar da tsagin G7

Idan ba kullalliya ba, me yahana tun farkon hukuncin da babbar kotu ta yi, ba su dauki satifiket sun ba Danzago ba, sai gashi nan take bayan hukuncin kotun daukaka kara, sun dauka sun ba tsagin gwamnati?

Idan kuma sunyi la'akari ne da cewar tsagin gwamnatin Ganduje sun daukaka kara, shine ya hana su ba kowa satifiket din a wancan lokaci, to yanzu ma kowa yasan cewa tsagin G7 su ma zasu iya daukaka kara zuwa kotun Allah ya isa.

Wannan ne dalilin da yasa muke zargin wata kullalliya daga uwar jam'iyyar ta APC

Uwar jam'iyyar tana sane, cewa maganar tana kotu amma ta bujiro da maganar sulhu tun da farko, sai gashi ta gaza daukan wani kwakkwaran matakin sulhu duk da korafin da bangaren G7 s**a gabatar a gaban ta na rashin yin adalci da daidaito a jadawalin da uwar jam'iyyar ta bujiro dashi na yin sulhun, wannan ya nuna ba dagaske sulhun ne a gaban su ba, wata aniya ce ta wofantar da tsagin G7

Duk ta inda uwar jam'iyyar ta bullo jama'a na kallon ta, wannan ne dalilin da yasa al'ummar jihar Kano, basu nuna farin ciki bisa wannan hukunci ba, duk majalasin da ka zauna zakaji ana yin Allah wadai, al'ummar Kano wayayyu ne a siyasance, matukar an zalinci wani bangare, a shirye suke da yin tofin Allah tsine hade da tausayawa wanda aka zalinta, tun daga kan 'yan jam'iyya har wadanda basa yin siyasa, aje a duba tarihi.

Ko shakka babu wannan zai ba jam'iyyar APC matsala babba a kakar zabe ta 2023 inda zai yi wahala ta kai banten ta.

12/02/2022

APC: sai an bamu shugabancin jam'iyya sannan zamu hakura ~ martanin tsagin G7

Tsagin G7 a jam'iyyar APCn jihar Kano, karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, sun fitar da wata sanarwa mai dauke da sa hannun dukkan jagororin tafiyar tasu, akan batun sulhu tsakanin tsaginsu dana gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, tare da gindaya wasu sharuda guda uku da s**a ce dole a cika musu kafin yin wannan sulhu.

Jaridar Kano Online News ta rawaito cewa, cikin sharudan na yan bakwai, sunce suna nan akan matsayarsu ta cewar za a basu kaso 55% cikin 100% sannan a basu shugaban jam'iyya, su kuma bangaren Ganduje su dauki kaso 45%.

Sharadi na biyu sunce, Gwamna ba zai sake jagorantar duk wani kwamitin sulhu ba saboda yana daga cikin wadanda ake rigima dasu, sai kuma sharadi na uku cewa bangaren Gwamnati su janye karar da s**a shigar a kotun daukaka kara, yin hakan zai tabbatar cewa an shirya yin sulhu bisa adalci, inji sanarwar ta yan bakwai.

Wannan sune sharudan da yan bakwai s**a aikewa da shugaban jam'iyyar APC ta kasa, kuma Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, biyo bayan fatali da yan bakwai din s**ayi da wani kwamitin sulhu da ya kafa, wanda ya nada gwamna Ganduje a matsayin shugaban wannan kwamiti.

Daga: Kano Online News
12/2/2022

HADAKAR TSAGIN MASU RUWA DA TSAKI NA JAM’IYYAR (APC) JIHAR KANO (G7)Mu da muka sa hannu a kasa, muna sanar daku cewa, mu...
08/02/2022

HADAKAR TSAGIN MASU RUWA DA TSAKI NA JAM’IYYAR (APC) JIHAR KANO (G7)

Mu da muka sa hannu a kasa, muna sanar daku cewa, mun karbi takardar wasikar ku ta ranar 7/2/2022 wacce ta kunshi yadda dunkulewar shugabancin jamiyyar APC a jihar kano zai kasance a kowane mataki. Wacce aka mikawa shugaban wannan tsagi Sanata Ibrahim Shekarau (Sardaunan kano.)
Kamar kullun, muna yabawa da kokari da rashin gajiyawa wajen ganin an tsaftace da kuma dawo da hadin kai da aminci a tsakankanin iyalin jamiyyar APC a jihar kano.
Idan zaka iya tinawa, tun lokacin da aka fara yin wannan zama na sulhu, an zauna sau da dama a karkashin ka, inda kuma kowane tsagi ya rubuta bukatun sa na yadda dunkulewar shugabancin jamiyyar APC a jihar kano zai kasance a kowane mataki.
Mun yi tinanin za’a fito da sakamako wanda ya shafi irin bukatun da kowane bangare ya bujuro da su zuwa gareka. Rashin jin dadi bisa wannan yunkuri, takardar da ka turo mana bata shafi dukkanin kudure-kuduren kowane tsagi ba, haka kuma ba ta ma yi koda tsokaci akan su ba.
Dadin-dadawa, gabadaya abin damuwa da rashin cika yarjejeniyar, kafin ma tsagin mu ya sami takardar wasikar taka, sai gashi tana yawo a kafofin sada zumunta na zamani ta hannun mutanen gwamnatin jihar kano, a matsayin shaidar su na karerayin jamiyyar ma dungurungum za’a sadaukarwa da ‘’tsagin maigirma gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje.’’
Sakamakon wannan dalili ne, ya tirsasa mu daukar matakin sanar da kai, ya maigirma, dukkanin kunshin takardar wasikar ka, ba karbabbiya bace daga garemu.
Kamar kullun, muna kara jaddada mika wuya wajen tabbatar da mutuncin jamiyyar da kuma shugabancin ta.
Muna fata Allah ya yi maka jagora, ya kare ka wajen tafiyar da jagorancin babbar jamiyyar mu ta (APC)
Mun gode
• Dist. Senator Ibrahim Shekarau. (Kano Central)
• Dist. Senator Barau I. Jibrin. (Kano North)
• Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe. (D/Tofa/Rimin Gado/Tofa Fed. Constituency)
• Hon. Nasiru Abduwa Gabasawa. (Gezawa/Gabasawa Fed. Constituency)
• Hon. Barr. Haruna I. Dederi. (Karaye/Rogo Fed. Constituency)
• Hon. Sha’aban Sharada. (Kano Municipal Fed. Constituency)
• Alh. Shehu Dalhatu. (Chairman, Buhari Support Group.)

Bayan shafe awanni shidai (6) cur suna fafatawa domin samo bakin zaren, dukkanin bangarorin da s**a shata layi a jam'iyy...
04/02/2022

Bayan shafe awanni shidai (6) cur suna fafatawa domin samo bakin zaren, dukkanin bangarorin da s**a shata layi a jam'iyyar APC a Kano, inda Sanata Ibrahim Shekarau ya, jagoranci bangaren G7 a daya gefen kuma Gwamna Ganduje ya jagoranci daya bangaren.

Daga karshe an kawo karshen zaman a bisa wata yarjejeniya da s**a cimma, yanzu haka sun fito daga wannan taro sun mikawa uwar jam'iyyar APC ta Kasa wannan kuduri nasu.

Daga bangaren shugabannin jam'iyyar ta Kasa sunce zasu duba kudirin nasu domin daukar matakin da ya dace nan bada dadewa ba.

Wadannan shine zaman da ya faru a jiya Talata 1/2/2022 domin yin sulhu tsakanin tsagin G7 da tsagin Ganduje a Abuja, kar...
02/02/2022

Wadannan shine zaman da ya faru a jiya Talata 1/2/2022 domin yin sulhu tsakanin tsagin G7 da tsagin Ganduje a Abuja, karkashin shugaban jam'iyyar APC na Kasa kuma Gwamna Yobe Maimala Buni - zaman ya tashi ba tare da bangaren Ganduje ya sa hannun bisa yarjejeniyar da aka cimma ba.

Kodai yarjejeniya sulhun ta yiwa bangaren Ganduje tsauri ko kuma dai wani dalili na daban, abinda ya rage yanzu shine, mu zura Ido mu ga abinda zai faru a zama na gaba.

Address

No 78 Hayin Fulani Zage Panshekara
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sen Barau Jibrin Online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sen Barau Jibrin Online:

Share