DKW HAUSA

DKW HAUSA wannan shafi an kirkireshine domin Samar da ingantatun labarai da Rahotonni daga sassa daban daban.

NA BAUTAWA KADUNA DA GASKIYA KUMA INA ALFAHARI DA HAKA--El-RufaiCopy BBCKwamitin da Majalisar dokokin jihar Kaduna ta ka...
06/06/2024

NA BAUTAWA KADUNA DA GASKIYA KUMA INA ALFAHARI DA HAKA--El-Rufai

Copy BBC

Kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa kan nazari game da kuɗaɗen da aka kashe a gwamnatin da ta gabata a jihar ya miƙa sak**akon bincikensa a yau.

Cikin shawarwarin da kwamitin ya bayar har da na buƙatar hukumomi su binciki tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i.

Lokacin da ya gabatar da rahoton a ranar Laraba, shugaban kwamitin, Henry Zacharia ya ce an gano cewa akasarin kuɗin bashin da jihar ta karɓa a zamanin mulkin El-Rufa'i, ko dai ba a yi amfani da su kan abin da aka ciyo bashin domin su ba ko kuma ba a bi ƙa'ida wajen cin bashin ba.

Da yake karɓar rahoton, shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman ya ce kuɗi naira biliyan 423 ne s**a zurare a lokacin gwamnatin El-Rufa'i tare da jefa jihar cikin ƙangin bashi.

Sai dai tsohon gwamnan ya ce binciken da majalisar jihar ta ba da shawarar a yi kan gwamnatinsa "bi-ta-da-ƙulli ne kawai na siyasa".

Cikin wata sanarwa da Muyiwa Adekeye ya fitar a madadinsa, El-Rufai ya ce ya bauta wa Kaduna "da gaskiya kuma yana alfahari da abubuwan da ya yi".

"[El-Rufai] ya bi duk wasu dokoki a ayyukansa lokacin da yake gwamna...ya k**ata a yi watsi da wannan binciken na ƙeta a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa."

Kwamitin ya buƙaci da a binciki tsohon gwamnan da wasu jami'an gwamnatinsa kan zargin rashawa da bayar da kwangila ba bisa ƙa'ida ba da kuma halasta kuɗin haram.

A watan Afrilu wannan shekara ne Majalisar Dokokin Kaduna ta kafa kwamiti domin binciken ayyukan da gwamnatin El-Rufa'i ta aiwatar tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.

Hakan ya zo ne bayan gwamnan jihar, Uba Sani, ya koka kan cewa jihar na fama da ƙangin bashin da ya kai na naira biliyan 85 da kuma wasu ayyukan da ke buƙatar kuɗi naira biliyan 115 domin kammalawa.

Uba Sani ya bayyana cewa a halin da ake ciki "jihar ba ta iya biyan albashi ba tare da ta ciyo bashi ba".

Lamarin ya haifar da muhawara, ganin cewar a baya ana yi wa gwamna Uba Sani da tsohon gwamna Nasiru El-Rufai kallon aminan juna.

A shekarar 2023 ne Nasir El-Rufa'i ya miƙa ragamar mulkin jihar ta Kaduna ga Sanata Uba Sani, bayan kammala wa'adin mulkinsa na shekara takwas.

Uba Sani ya zama gwamna ne bayan ya lashe zaɓen da aka gudanar a watan Maris na shekara ta 2023.

Kafin wannan lokacin, Uba Sani ya kasance ɗan majalisar dattijai mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta tsakiya, kuma ana ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen karɓar basuss**an da gwamnatin jihar Kaduna ta samu a lokacin mulkin Nasir El-Rufa'i.

Kaduna na daga cikin jihohin Najeriya waɗanda s**a fi yawan bashi a kansu.

Rigimar Sarautar Kano: Sanusi II Ya Samu Goyon Baya Daga Kungiyar Lauyoyin Najeriya  Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta...
05/06/2024

Rigimar Sarautar Kano: Sanusi II Ya Samu Goyon Baya Daga Kungiyar Lauyoyin Najeriya

Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta gayyaci Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II zuwa wani babban taro da ta gudanar a jihar A yayin da ake ci gaba da fafata rikicin sarautar Kano, NBA ta amince da Sanusi II a matsayin halaltaccen sarkin masarautar Sarkin Kano Sanusi II wanda ya yi jawabi a taron ya ce har sai akwai karfin shari'a a ƙasa ne al'uma ke iya yin rayuwa cikin salama

A yayin da ake ci gaba da fafata rikicin sarautar Kano, kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta amince da Muhammadu Sanusi II a matsayin halaltaccen sarkin masarautar.

Wannan na zuwa bayan da shugabannin kananan hukumo 44 na Kano da hakiman su, kwamishinoni da wasu manyan jihar s**a yi mubaya'a ga sabon sarkin.

Kungiyar NBA ta gayyaci Sanusi II taro

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kungiyar NBA ta amince da nadin Sarki Sanusi II ne bayan ta gayyace shi taronta na shekara da ke gudana yanzu a Kano.

La'akari da girman wannan taron, kungiyar lauyoyin ta gayyaci Sanusi Sarkin Kano na 16, domin ya gabatar da jawabin sanya albarka a matsayinsa na uban ƙasa.
An ce kungiyar ta NBA ba ta gayyaci Alhaji Aminu Ado Bayero ba, wanda dokar masarautar Kano ta 2024 ta kore shi daga karagar mulki a matsayin Sarkin Kano na 15.

Sarki Sanusi II ya yi magana kan shari'a

A ran Litinin ne babbar kotun tarayya da ke Kano ta shirya sauraron karar da aka shigar gabanta kan rigimar masarautar amma saboda yajin aikin NLC ba ta samu zama ba.

Sarki Sanusi II wanda ya yi jawabi a taron kungiyar NBA ta bakin wakilinsa, Mahe Bashir Wali (Walin Kano) ya yi wa baki maraba da nuna girman al'adun jihar Kano. Sarkin ya ce har sai akwai karfin shari'a a ƙasa ne al'uma ke iya yin rayuwa cikin salama, wanda kuma ya ce bunkasar al'uma na tattare da karfin shari'a, in ji rahoton Independent.

Gwamnan Kano ya ƙalubalanci lauyoyi

A bangaren gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf kuwa, ya yi amfani da damar wajen ƙalubalantar NBA kan makomar umarnin kotuna biyu game da rigimar masarautar jihar. Gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Bappa Bichi ya nemi lauyoyin da s**a rika wayar da kan abokan huldarsu kan hurumin kotuna a shari'a. Abba Yusuf ya ce akwai kotun da ba ta da hurumin sauraron shari'ar rigimar masarautar Kano kasancewar rigima ce ta cikin gida, wadda kotun jiha ke da hurumin saurare.

Sarki Sanusi II ne Sarkin Kano
-NBA Da yake zantawa da manema labarai kan rikicin masarautar Kano, Barista O.M Femi ya ce kungiyar NBA ba ta da masaniya kan abin da ke faruwa. Barista O.M Femi ya ce: “Duk da haka, ba ka bukatar a gaya maka ko ka sanya tabarau kafin ka san cewa Mai Martaba Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano na 16 a yanzu.

"Haka zalika, gayyatar Sarki Sanusi II zuwa wannan babban taron na NBA zai kara ba ka tabbaci na wanda muke kallo a matsayin Sarkin Kano na 16.

International Human Rights I Commission Ta Nemi Masu Ruwa Da Tsaki Su Sulhunta Rikicin Masarautar Kano. By Nura Bala Aji...
04/06/2024

International Human Rights I Commission Ta Nemi Masu Ruwa Da Tsaki Su Sulhunta Rikicin Masarautar Kano.

By Nura Bala Ajingi

Hukumar Kare Hakkin bil'adama ta Duniya ta nemi masu ruwa da tsaki su sulhunta rikicin Masarautar kano domin dorewar zaman lafiya.

Daraktan Hukumar a Nigeria Alh. Abdullahi Bakoji Adamu ya bayyana bukatar hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Mai Alfarma Sarkin Musulmi da Kungiyar Tuntubar Arewa da Gwamnonin Arewabda sarakunan gargajiya da duk wasu masu ruwa da tsaki, da su dauki matakan gaggawa da s**a dace don kawo karshen rikice-rikicen da ake yi a Masarautun Kano.

Alh. Abdullahi Bakoji ya jaddada Matsayar Hukumar na inganta zaman lafiya da tsaro ga dukkan 'yan Najeriya da kuma warware wadannan rikice-rikice bisa la'akari matukar muhimmancin hakan wajen zama lafiya.

Ya kara da cewa halin da ake ciki yanzu a Masarautun Kano akwai barazanar tsaro da samun cikas ga cigaban jahar da yankin arewa da kasa baki daya.

Hukumar ta bayyana Rikice-rikice masu tsawon irin wannan na iya haifar da karuwar tashin hankali, koma bayan tattalin arziki, da karin rarrabuwar Kawuna tsakanin al'umma.

Muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su shiga cikin tattaunawa mai amfani da warware rikice-rikice, bisa ka'idodin da aka shimfida a cikin Kundin Kare Hakkin Dan Adam na Duniya.

Ofishin Hukumar kare hakkin bil'adama ta Duniya a Nigeria ya bayyana muhimmancin girmama juna da fahimtar juna, da hadin kai, wajen dorewar zaman lafiya da cigaba.

Nawa kuke gani ya dace a biya ma'aikata a matsayin mafi karancin albashi? Ga jadawalin kasafin kudin da aka ware wa yan ...
04/06/2024

Nawa kuke gani ya dace a biya ma'aikata a matsayin mafi karancin albashi?

Ga jadawalin kasafin kudin da aka ware wa yan majalissu, da kuma mafi karancin albashi da ake biyan ma'aikata tun daga farkon fara demokradiyya a Najeriya.

Wata sabuwar Amarya mai suna Habiba Ibrahim, ta guntule al'aurar angonta Salisu Idris, mai shekaru 40, ya yin da yake ba...
04/06/2024

Wata sabuwar Amarya mai suna Habiba Ibrahim, ta guntule al'aurar angonta Salisu Idris, mai shekaru 40, ya yin da yake barci.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Kudan da ke jihar Kaduna tun a ranar 26 ga watan Mayu bayan ya dawo daga sallar asuba.

KANO TUMBIN GIWA Babbar kotun tarayya da ke Kano bata zauna kan batun rushe masarautu ba sanadiyyar yajin aiki.Yajin aik...
03/06/2024

KANO TUMBIN GIWA

Babbar kotun tarayya da ke Kano bata zauna kan batun rushe masarautu ba sanadiyyar yajin aiki.

Yajin aikin da kungiyar kwadago ta tsunduma ya haifar da Nakasu a bangarori da dama a fadin kasar nan

Yan sanda Jigawa sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da aikata laifin fashi da makami

Rashin yashe magudamam ruwa na kan gaba wajen haifar da ambaliyar ruwa a sassan unguwanin jihar Kano.

03/06/2024

Yaya yajin aikin Yan Kwadago ya shafe ku?

Mafi karancin albashin dubu 494 da NLC ke nema na iya haifar da illa ga tattalin arzikin kasa – AkpabioShugaban Majalisa...
03/06/2024

Mafi karancin albashin dubu 494 da NLC ke nema na iya haifar da illa ga tattalin arzikin kasa – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce mafi karancin albashi na Naira dubu ɗari huɗu da Casa'in da huɗu 494,000 da kungiyoyin kwadago s**a nema zai tilasta wa ma'aikatu masu zaman kansu da yawa korar ma’aikatansu idan har aka aiwatar da shi.

Mista Akpabio ya bayyana haka ne a ranar Lahadi yayin Jawabin bude taron gaggawa da ake yi da Shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya wato NLC da TUC a harabar Majalisar dokokin Tarayya a Abuja.

Shugabannin Majalisar dattawa da na wakilai ne s**a kira taron.

Taron na zuwa ne kwana ɗaya gabanin fara yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyoyin kwadagon biyu s**a kira kan mafi karancin albashi.

Shugaban Majalisar dattijai yayin da yake Jawabi ga shugabannin kwadago kafin soma taron, ya bukace su da su lura da barnar da ka iya faruwa idan har Gwamnatin Tarayya ta amince da mafi karancin albashi na Naira 494,000 k**ar yadda s**a bukata.

Ya ce yawancin kamfanoni da Ma'aikatu masu zaman kansu a kasar nan na iya kasa biyan mafi karancin albashin da kungiyoyin s**a bukata, kuma hakan na iya tilastawa kamfanonin sallamar ma’aikatansu.

Don haka ya bukaci shugabannin kungiyar da su kula da tasirin bukatar tasu ga tattalin arzikin ƙasa.

"Amma kuma dole ne mu lura da barnar da ka iya aukuwa. A kokarin da ake na cimma mafi karancin albashi, sai kuma mu gamu da matsaloli masu tsanani na rashin aikin yi, domin da zarar mun tabbatar da mafi karancin albashin, to mu sa ran cewa kamfanoni masu zaman kansu su ma za su bi sabon tsarin, idan kuwa ba za su iya ba, hakan ba ƙaramar matsala ba ce” inji shi.

Mista Akpabio ya ba da tabbacin cewa duk wata yarjejeniya da za a cimmawa tsakanin Gwamnati da Shugabannin kwadago to zai zama maslaha ne ga ‘yan Najeriya.

Wannan shine dalilin da ya sa muka ji ya k**ata mu hadu cikin gaggawa, Tabbas wannan babban mataki ne a ka ɗauka, kuma za muyi abin da ya dace.

Shugaban Majalisar dattawan ya ba da tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya da shugabannin Majalisun biyu za su duba bukatun.

Daga Ibrahim Ibrahim

GWAMNAN JIHAR KANO YA DAWO TASHIN TASKAR ALHAZAN KANO. A jiya, 1 ga watan Yuni, Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Alhaji Abb...
02/06/2024

GWAMNAN JIHAR KANO YA DAWO TASHIN TASKAR ALHAZAN KANO.

A jiya, 1 ga watan Yuni, Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da rakiyar Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Dan Baffa, sun yi musabaha da maniyyatan Kano. Mahajjatan sun shirya tashi ne a jirgin Max Air mai lamba VM3055.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana jin dadinsa bisa kokarin hukumar jin dadin alhazai wajen tabbatar da jin dadin alhazai. Ya kuma bayyana kudurinsa na tallafawa kowane mahajjaci da Riyal 10,000 idan ya isa kasar Saudiyya.

Idan dai ba a manta ba a baya Gwamnan ya bayar da tallafin kudi na Naira 500,000 ga kowane alhazan Kano a daidai lokacin da farashin dala ya tashi. Bugu da kari, ya amince da $5,000 a matsayin kudin aljihu ga kowane mahajjaci.

A wani ci gaban mak**ancin haka, Hon. Abdul Mumini Jibrin Kofa, Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, ya ziyarci filin jirgin domin duba maniyyatan karamar hukumar Bebeji. Ya kuma tallafa wa kowane mahajjata 500 da Naira 10,000 da karin Naira 20,000 ga kowane mahajjaci daga karamar hukumar Bebeji.

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Dan Baffa, ya gode wa Gwamna Abba kan ziyarar da Hon. Kofa saboda karamcin da ya nuna ga alhazai. Ya kuma bukaci maniyyatan da su kasance jakadu nagari na Kano da Najeriya baki daya.

Alhazan sun nuna jin dadinsu ga Gwamnan bisa wannan karamci da ya nuna masa tare da yi masa addu’a.

Rahoto:
Abdullahi Ghali Basaf
Tawagar Jahar Kano Hajj 2024
2 ga Yuni, 2024

Sanata Abdulaziz yari tsohon Gwamna Zamfara ya bayyana cewa, Nasarar da gwamnatin Tinubu ta samu ba'a taba samun wata gw...
02/06/2024

Sanata Abdulaziz yari tsohon Gwamna Zamfara ya bayyana cewa, Nasarar da gwamnatin Tinubu ta samu ba'a taba samun wata gwamnati a Najeriya da ta cimma wannan nasarar ba.

Yari ya bayyana haka ne yayin rabon motocin bas da gwamnan Sokoto yayi guda 56 ga ƙananan hukumomi da kungiyoyin addininai na fadin jihar Sokoto..

Tsadar rayuwa: Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce sai da s**a yi wa 'yan Nijeriya gargadi ka...
02/06/2024

Tsadar rayuwa: Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce sai da s**a yi wa 'yan Nijeriya gargadi kar su sake yin kuskuren zaben jam'iyyar APC a zaben 2023.

KANO KENAN KODAME KAZO ANFIKA       An k**a wani matashi a Najeriya ya yi sata, maimakon mutanen unguwar su ƙoná shí ko ...
02/06/2024

KANO KENAN KODAME KAZO ANFIKA
An k**a wani matashi a Najeriya ya yi sata, maimakon mutanen unguwar su ƙoná shí ko su raunata shí, sai s**a ba shi Maltina da abinci ya ci ya ƙoshi...

Sannan s**a saka shi a gaba s**a kai shi sai da ya kwashe dukkan kwatamin da ke unguwar ya fitar musu da hanyoyin ruwa saboda damina, sannan s**a sallame shi.

Shin wannan hukuncin ya yi daidai?

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke mawakin nan kuma Jarumin TikTok Al’amin G-Fresh.Bayanan da Freedom Radio ta samu s...
02/06/2024

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke mawakin nan kuma Jarumin TikTok Al’amin G-Fresh.

Bayanan da Freedom Radio ta samu sun nuna cewa Hisbah ta k**a G-Fresh saboda zargin yiwa Alkur’ani Mai Girma Izgili da kuma yin kalaman batsa.

Me za ku ce?

Ba bu Sasantawa Kan Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi – DoguwaShugaban kwamitin kula da harkokin man fetur na Majalisar Wa...
02/06/2024

Ba bu Sasantawa Kan Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi – Doguwa

Shugaban kwamitin kula da harkokin man fetur na Majalisar Wakilai, Alhaji Alhassan Ado Doguwa, ya ce batun samar da ‘yancin cin gashi kan kananan hukumomi a kasar nan shi ne babban fifiko.

Doguwa ya shaida wa manema labarai a Kano ranar Asabar cewa: “Rashin zaman lafiya, talauci, da rashin ci gaban da ake fama da shi a yau duk sak**akon rashin ayyukan yi ne na kananan hukumomin kasar nan.”

Doguwa, wanda ya bayyana a cikin Wata rigar basaraken gargajiya, ya ce: “Na kasance Sardauna Doguwa ne, domin a iya sanina, rigimar da ke tattare da rusa masarautun (Kano) har yanzu batu ne na shari’a. Ya bayyana cewa ita ma wannan majalisar ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin an amince da kudurin dokar man fetur ya zama doka, kuma a yau, dangane da wannan fanni, Nijeriya na tafiya da kafadarta a tsakanin kasashen duniya.”

Da yake tunawa a yau kasar ta fi kyau saboda wasu kudirori da dama da aka zartar da su a matsayin doka, ya ce:

“Saboda haka, ya k**ata mu wuce gona da iri domin ganin an samu ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi. Don haka ne nake son shugaban majalisar da kansa ya jagoranci kwamitin duba kundin tsarin mulkin kasar domin mu yi sihiri tare.

"Ina tabbatar muku da cewa idan kananan hukumomi s**a sami 'yancin cin gashin kansu, 'yan Najeriya za su sake kwana da idanunsu a rufe kuma su zaga ko'ina ba tare da fargabar an yi musu fyade ko a dauke su ba."

Daga: Abbas Yakubu Yaur

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf  ya gwangwaje iyalan guda daga cikin wakilan kwamitin jiha na masu kula da Ma...
01/06/2024

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gwangwaje iyalan guda daga cikin wakilan kwamitin jiha na masu kula da Makabartu, Alhaji Yusuf tukur Tarauni wanda Allah yayi wa rasuwa da kyautar kudi naira Miliyan biyu (2,000,000) domin magance wasu 'yan matsalolin yau da kullum.

Inda kuma nan take mai girma Gwamnan ya ba da umarnin a dauki babban dansa aikin gwamnati wanda yayi karatun injiniya

Sakataren Gwamnatin jihar Kano Dr Baffa Bichi, shi ne ya wakilci gwamnan wajen isar da wannan sakon Alkhairi.

📷 Hon Salisu Muhammad Kosawa

01/06/2024

DKW HAUSA Ke muku fatan kuntashi lafiya Daga nan Birnin Kano.

RABI'U MUSA WANKWASO Sheikh Ja’afar mahamud Adam yace: Babu wata kasa daga kasashen manyan kafuran duniya da basu zagi K...
31/08/2023

RABI'U MUSA WANKWASO

Sheikh Ja’afar mahamud Adam yace: Babu wata kasa daga kasashen manyan kafuran duniya da basu zagi Kwankwaso kan kafa shari’ar musulinci ba a jahar kano da jan kunnen sa na kar ya soma amma Kwankwaso sai da ya tsaya tsayin daka ya tabbatar da ita ba tare da kallon s**ar da akeyi masa da zagin sa ba. Amma kullum ba’a kallon wannan amatsayin aikin alkhairin da yakamta Ayaba masa

Shine gwamna na farko a jahar kano da ya kafa hukumar da zata ringa aiki da lttafin Allah da umarnin manxon Allah s a w (Hisba) amma duk da haka Kwankwaso bai kai Ayaba mai ba.

Sheikh Kabiru haruna Gwambe yace: Kwankwaso shine mutumin da ya dauki nauyin karatun ‘ya’yan talakawa ‘yan asalin jahar kano da wajen kano Sama da dubu goma a kasashen turai kyuata Amma wasu sunce yana 6ata tarbiyar matasa da basu mak**ai da kwayoyi.

Kwankwaso Shine wanda yazo yatarar da kano babu wata Universe sai guda daya, YAQARA university biyu a jahar tazama uku Amma wasu sunce bashi da buri wai sai son Lalata tarbiyar matasan jahar kano dashigar dasu cikin bangar siyasa.

Kwankwaso yakafa makarantar kiru dan magance matsalar samari masu shaye-shaye, in agama yima maganin kuma akoya ma sana’a abaka jarI, in kana da shaidar karatu ga hukuma nan yakafa ta karota da comepress security masu jan wando Farar riga,a dauke ka aiki ake runga baka albashi duk wata, Amma duk wannan ba alkhairin bane awajen wasu.

Mu kalli alkhairin Kwankwaso da sharrin sa in yaso sai miyi masa hukunci da abun da ya rinjaya na ayyikan sa, domin mu musulmai ne so Da ki duk dan Allah yakamta ace munayi.

Shi yasa mu kullum muke rokon Allah Akan ya nuna mana gaskiya gaskiya ce kuma ya bamu ikon bunta koda daga gun wanda ba layin mu daya ba.

Kuma muke rokon Allah da ya nuna mana karya karyace
ya bamu ikon guje Mata koda daga gun wanda yake layin mu daya ne dashi.

✍️ :Abasu mamaki 09035010830

Duk wanda ya keta doka, to tabbas doka za tayi aiki akansa kowanene - Anti KwarafshanHukumar yaƙi da rashawa da karɓar k...
21/07/2023

Duk wanda ya keta doka, to tabbas doka za tayi aiki akansa kowanene - Anti Kwarafshan

Hukumar yaƙi da rashawa da karɓar korafe-korafen al'umma ta jihar Kano, ta ce ayyukan ta na ba sani ba sabo ne, da yan jam'iyya mai mulki da na adawa, duk doka za tayi aiki akansu, idan an same su da laifi.

Jawabi hakan ya fito ne daga bakin shugaban hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, yayin wata ganawa da manema labarai, inda yace hukumar na yin ayyukan ta tsakani da Allah, babu batun nuna wariya akan kowa, matukar mutum ya aikata laifi, to ba shakka doka za tayi aiki a kansa.

Muhuyi ya ce ko a makon jiya sun gayyaci wani mai suna Murtala Alasan Zainawa, akan wasu batun wasu motocin hukumar kwashe shara ta jihar Kano (REMASAB), da ake zargin an cefanar dasu a gwamnatin da ta gabata, kuma shi Zainawa yana da alaƙa da batun, wanda kuma a halin yanzu jigo ne a jam'iyyar NNPP mai mulkin Kano.

Bugu da ƙari, Muhuyi ya gargadi tsohon kwamishinan ma'aikatar raya yankunan Karkara ta jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, akan wani zargi da yayi masa na cewa yasa jami'an tsaro sun ci zarafinsa, inda yace ba haka bane, ya karɓi Mota ne wacce Musa Iliyasu ya dauka kafin su bar gwamnati, wacce kuma ta hukuma ce.



21/7/2023

Address

No 18 Western Road Opposite Police Station
Kano
0019

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DKW HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to DKW HAUSA:

Share

Category


Other Newspapers in Kano

Show All