09/12/2024
SANARWA TA MUSAMMAN!
Hukumar kula da manyan asibitoci ta jihar kano karkashin jagorancin Babban sakatare na hukumar Dr Mansur Nagoda na sanar da alumma cewa, an samu matsalar wutar lantarki a bangaren haihuwa a asibitin Murtala sak**akon hadewar layin wuta da pipe din ruwa da yayi ta karkashin kasa. A Tun jiya injiniyoyin mu ke ta haka domin shawo kan matsalar.
A dan haka ne hukumar ke sanar da masu bukatar aiki na gaggawa musamman aikin tiyata da su garzaya asibitin Nuhu Bammalli dake kofar Nasarawa domin samun kulawa.
Muna bada hakuri ga jamaa akan wannan tsaikon da aka samu.
SANARWA DAGA
Samira Suleiman
Jamiar Hulda da Jamaa ta Hukumar kula da manyan asibitoci ta jihar kano(HMB)
09/12/2024