10/12/2022
*ƊAURIN AUREN MUTU’A*
Domin mai karatu ya gamsu da cewa Mutu’a ƙofar zina ce kawai aka buɗewa mutane, bari mu duba yadda ake yin ɗaurin aure a tsarin Mutu’a. Auren Mutu’a ba ya buƙatar a samu wakilin “ango” ko waliyin “amarya”, ba ya buƙatar shaidu; ba’a ma buƙatar kowa ya sani, kuma bai buƙatar wani ɓata lokaci. Da zarar an haɗu sai kawai a yi a gama!
Malaman Shi’a sun ruwaito cewa wani almajirin Imam Ja’afar Sadiƙ ya tambaye shi: “Ya zan ce da ita idan na kaɗaita da ita? Sai ya ce: Ka ce: Ina auren ki auren Mutu’a a bisa Littafin Allah da Sunnar Annabinsa; ba kya gado, ba’a gadon ki; kwana kaza kaza, ko shekara kaza kaza, a kan dirhami kaza kaza, sai ka ambata mata ladan da kuka yi yarjejeniya a kai, kaɗan ne ko da yawa.” [ *Muhammad binu Ya’akub Alkulaini, Furu’ul Kafi, bugun Darul Murtali, Bairut, 1428 B.H., muj. na 5 sha. na 455].*
Ina son mai karatu ya lura da yadda mai tambayar ya yi tambayarsa: “Ya zan ce da ita idan na kaɗaita da ita?” A ina a duniya aka san aure a cikin kaɗaitaka, a keɓe? Babu wani addini a duniya, ko wata al’ada, inda ake aure a keɓe. Babu inda ake aure a sirri sai a addinin Shi’a.
Wannan kawai ya isa ya tabbatar wa da mai karatu nisan wannan launi na aure da addinin Musulunci. A Musulunci, ana so a ɗaiɗaita labarin aure, a kururuta shi, a yaɗa shi, a kwaza shi, a yi talla da shi har duniya ta sani. Hadisai masu yawa sun zo da haka. Albani ma kaɗai, a cikin littafinsa Adabuz Zifafi, hadisai shida ya kawo, duka suna nuna wannan ma’ana. Ga biyu daga cikinsu don misali:
1. “Ku yi shela da aure.” [ *Albani ya ce Ibnu Hibban da Dabarani da Diya’u Almaƙdisi duka sun ruwaito shi, kuma isnadinsa mai kyau ne. Duba Adabuz Zifafi na Albani, bugun Almaktabul Islami, 1409/1989 sha. na 111-112].*
2. “Bambancin tsakanin halal da haram (a aure) buga ganga.” [ *Albani ya ce Nasa’i da Tirmizi da Ibnu Majah sun ruwaito shi da isnadi kyakkyawa. Duba Adabuz Zifafi, sha. na 111].*
Dubi yadda Manzo(SAW) ya kwaɗaitar a buga ganga, duk da ƙyamar da Musulunci yake ga kiɗa, don a kwarmata aure!
*Sadaki ko Lada?*
Abin sha’awa ne yadda malaman Shi’a ba sa kiran sadakin auren Mutu’a da sunan sadaki, sai dai su ce ujura, watau lada. Duk littafan da na duba ba inda s**a kira shi da sunan sadaki. Wataƙila a cikin wannan akwai matashiya, amma fa ga masu hankali!
Bari mu kira shi yadda s**a kira abinsu: Mene ne ladan auren Mutu’a? S**a ce an tambayi Abu Ja’afar, Imamin Shi’a na biyar, ya ce, “Dirhami zuwa sama.” [ *A duba Furu’ul Kafi na Kulaini, muj. na 5 sha. na 457* ]. Ɗansa kuwa, Ja’afar Sadiƙ, ya ce, “Tafi ɗaya na gari ko tafi ɗaya na dabino.” [ *Furu’ul Kafi, muj. na 5 sha. na 457].*
Watau da Hausa muna iya cewa sadakin auren Mutu’a shi ne ƙwandala ko gwan-gwan ɗaya na garin kwaki! Akwai wani addini a duniya da ya wulaƙanta mata kamar addinin Shi’a? Allah ya tsare matan Musulmi da irin wannan ƙasƙanci!
*Da Wa Ake Mutu’a?*
Shin sai da Musulma kawai ake Mutu’a? A’a sam! A cikin daren ƴan Shi’a, ko kyankyaso ma nama ne! Don haka s**a rawaito daga Imaminsu na shida, Ja’afar Sadiƙ, (Allah ya isar masa ƙarerayin da aka laƙa masa), wai ya ce, “Babu laifi mutum ya yi Mutu’a da Bamajusiya.” [ *Abu Ja’afar Muhammad binul Hassan Aldusi, Tahzibul Ahkam, bugun Darul Adwa, Bairut, 1406 B.H., muj. na 7 sha. na 256]* . Kuma ana yi da Banasariya (Kirista) da Bayahudiya, kamar yadda s**a ruwaito daga Imaminsu na takwas, Abul Hassan Ali binu Musa Rida, [ *Tahzibul* *Ahkam, muj* . 3 shafi na 144]. Haka nan ana yi da karuwa domin, kamar yadda s**a ce, sai ya hana ta karuwanci! [ *Tahzibul Ahkam, muj. na 7 sha. na 253. Kuma a duba Tahrirul Wasila na Ayatullah Ruhullah Khumaini, bugun Darul Ilmi, Kum-Iran, ba tarihi, sha. na 295].*
*- JERIN LITTAFAN SHI’A NA 4: "Auren Mutu’a a wajen Ƴan Shi’a" - na Prof. Umar Labɗo*
*✍ AnnasihaTv*
- ```Ga masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuɓe mu kamar haka``` ;
*Call/WhatsApp*: 08142286718
*Twitter:*
Islamic, Salafiy Online Television founded to solve all the media and publicity global challenges in the most systematic way. Most organize so far. Founded 2016