Sahelian Times Hausa

Sahelian Times Hausa Ku biyo mu domin samun sahihan labarai tare da labarai da Dumi-Duminsu daga Nigeria da kasashen Afri

Kamfanin BUA ya karya farashin siminti a kasuwa.A wata sanarwa da kamfanin ya fitar, za’a na saida siminti a naira 3,500...
01/10/2023

Kamfanin BUA ya karya farashin siminti a kasuwa.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar, za’a na saida siminti a naira 3,500 kacal, a maimakon naira 5,000 zuwa 5,500 da yake a da.

Sabon farashin zai fara aiki a gobe Litinin, 2 ga watan Oktoba, 2023.

Kwanakin baya dai shugaban kamfanin na BUA, Abdussamad Rabiu yasha alwashin rage farashin siminti da zarar sun kammala gina sabon kamfaninsu na siminti a farkon shekara ta 2024.

Sai dai kamfanin yace yayi hanzarin cika alkawari ne saboda bawa jama’a daman more farashi mai rahusa tun kafun shekara ta 2024.

Shin ko sauran kamfanonin siminti irin su Dangote Cement zasu bi sahun BUA?

Ga takaitaccen abubuwan da Tinubu ya zayyana a jawabinsa na bikin ranar samun 'yancin kan Najeriya.- Biyan naira 25,000 ...
01/10/2023

Ga takaitaccen abubuwan da Tinubu ya zayyana a jawabinsa na bikin ranar samun 'yancin kan Najeriya.

- Biyan naira 25,000 ga ma-aikata mafi karancin albashi har na tsawon watanni shida.

- Kafa asusun gina kasa don yin ayyukan raya kasa wadanda zasu farfado da tattalin arziki.

- Bada tallafin gaggawa wa jihohi don rage radadin cire tallafin man fetur.

- Samar da motocin sufuri masu amfani da iskar gas don rage tsadar kudin sufuri.

- Yin garambawul ga harkar haraji, ta hanya rage wasu harajin domin samawa masu kananan sana'a sauqi, tare da kuma toshe hanyoyin da ake asarar kudin haraji.

- Fadada asusun tallafawa marasa karfi har mutum miliyon 15.

- Yin garambawul a harkar gwamnati da harkar tattalin arziki.

Yaya kuke ganin wadannan kudurorin zasu kasance a aikace?

Najeriya kasarmu ta gado: mene ne fatanku ga Najeriya akan cika shekaru 63 da samun 'yancin kai?
01/10/2023

Najeriya kasarmu ta gado: mene ne fatanku ga Najeriya akan cika shekaru 63 da samun 'yancin kai?

Victor Osimhen yayi barazanar kai kulob dinsa ta Napoli kotu saboda wani bidiyon da s**a dora a manhajar TikTok dake nun...
27/09/2023

Victor Osimhen yayi barazanar kai kulob dinsa ta Napoli kotu saboda wani bidiyon da s**a dora a manhajar TikTok dake nuna batanci ga dan wasan.

Mai wakiltan dan wasan ne ya shaida haka. Tuni dai Napoli ta goge bidiyon, wanda wallafashi ya janyo kace-nace a dandalin sada zumunta na soshiyal midiya.

Muna taya dimbin mabiyanmu murnar zagayowar Bikin Maulidi.
27/09/2023

Muna taya dimbin mabiyanmu murnar zagayowar Bikin Maulidi.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu don bikin ranar maulidin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad...
26/09/2023

Gwamnatin Tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu don bikin ranar maulidin fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW).

Macron yace ya sanar da Mohammed Bazoum, wanda sojoji ke tsare dashi. Faransa dai har yanzu tana kallon Bazoum a matsayi...
25/09/2023

Macron yace ya sanar da Mohammed Bazoum, wanda sojoji ke tsare dashi. Faransa dai har yanzu tana kallon Bazoum a matsayin halastaccen shugaban Kasar Nijar, tare da tuhumar sojin Nijar da yin garkuwa dashi.

Hukumomin sojin Nijar sunyi maraba da kudurin, inda s**a bayyana shi a matsayin wani babban nasara da mutanen Nijar s**a cimma ta hanyar gangamin nuna kin amincewa da cigaba da zaman sojin Nijar a kasar.

Hulda tsakanin Nijar da Faransa dai ta tabarbare ne bayan sojin Nijar sun hambarar da gwamnatin Bazoum, lamarin da ya haifar da barazanar yin amfani da karfin soja daga kungiyar ECOWAS.

Lamarin dai ya faru ne a safiyar yau Litinin. Tuni yan kwana-kwana suna kokarin shawo kan gobarar. Har yanzu ba'a tantan...
25/09/2023

Lamarin dai ya faru ne a safiyar yau Litinin. Tuni yan kwana-kwana suna kokarin shawo kan gobarar. Har yanzu ba'a tantance asaran da gobarar ta janyo ba.

Wadannan sune sabbin nade-nade da Tinubu yayi na masu bashi shawara da kuma mataimaka na mussaman a ofishinsa da kuma na...
18/09/2023

Wadannan sune sabbin nade-nade da Tinubu yayi na masu bashi shawara da kuma mataimaka na mussaman a ofishinsa da kuma na mataimakinsa.

Kotun sauraron koke-koken zabe na Jihar Zamfara ta tabbatar da nasarar da Dauda Lawal ya samu a matsayin zababben gwamna...
18/09/2023

Kotun sauraron koke-koken zabe na Jihar Zamfara ta tabbatar da nasarar da Dauda Lawal ya samu a matsayin zababben gwamnan jihar Zamfara.

Gwamnatin Jihar Legas to bada umarnin yin sanarwa da harshen yarbanci a tashoshin jiragen kasa dake birnin Legas.
14/09/2023

Gwamnatin Jihar Legas to bada umarnin yin sanarwa da harshen yarbanci a tashoshin jiragen kasa dake birnin Legas.

A na fuskantar matsalar rashin wuta a sassan Najeriya da dama, bayan faduwan manyan layukan wutan lantarki na kasa.
14/09/2023

A na fuskantar matsalar rashin wuta a sassan Najeriya da dama, bayan faduwan manyan layukan wutan lantarki na kasa.

"Talakawa na tururuwa zuwa garin Daura don ganin Buhari, suna kewar mulkinsa," - cewar Garba Shehu.Tsohon mai magana da ...
14/09/2023

"Talakawa na tururuwa zuwa garin Daura don ganin Buhari, suna kewar mulkinsa," - cewar Garba Shehu.

Tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari yace dandazon jama'a ne ke tattaki zuwa garin Daura don ganin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, tare da nuna kewar mulkinsa.

A cewar sa, Shugaba Buhari dai ya yanke shawarar komawa Daura ne bayan kammala wa'adin mulkinsa, saboda ya bawa sabon shugaban kasa Bola Tinubu sukunin gudanar da mulki ba tare da wata tsangoma ba.

A wata makala da ya fitar a shafinsa ta X (Tuwita), Garba Shehu ya kara da cewa, Buhari na zuwa gona sau hudu a sati, inda alfahari da irin kulawar da amfanin gona da dabbobinsa suke samu. Amma duk da haka, mutane nayin tururuwa don zuwa gaisuwan ban gajiya da kuma godiya da irin rawar da ya taka a lokacin mulkinsa.

Tsohon kakakin ya kuma kara da cewa, Buhari bai son mutane suna kashe kudin mota har Daura domin da sunan gaisuwa. Inda a kwanaki yake maraba da cire tallafin man fetur da Tinubu yayi, ganin hakan zai iya sa mutane su hakura da zuwa gidan nasa na Daura. Amma sai dai kash, mutane basu hakura ba, inda suke hada kudin mota suyi lodi na musamman domin zuwa Daura gaisuwa.

"Peter Obi bai ci zaben 2023 ba, na uku ya zo, amma yana kokarin yamutsa hazo da karairayin cewa shine yaci zaben" - cew...
14/09/2023

"Peter Obi bai ci zaben 2023 ba, na uku ya zo, amma yana kokarin yamutsa hazo da karairayin cewa shine yaci zaben" - cewar Wole Soyinka.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sahelian Times Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sahelian Times Hausa:

Share