09/01/2025
Gwamnatin kasar Ethiopia ta amincewa kamfanin BIT na kasar China ya kafa cibiyar samar da wutar lantarki mai karfin Mega watts 51 domin mining Bitcoin.
~ Kamfanin hakon Bitcoin na kasar China wato "BIT Mining" yace zasu fara aikin wanda zai lashe Dala Miliyan 14 (kimanin Naira biliyan 23 a kudin Nigeria).
BIT mining yace idan aikin ya kammala zai iya daukar Na'urorin hakon Bitcoin guda dubu 18,000 tare da samar da aikin yi ga matasa a kasar fiye da mutum 2,000.
~ A nata bangaren kuma gwamnatin Ethiopia tace wannan zai karawa kasar ta kudin shiga daga cikin dimbin arzikin hydropower resources da kasar take dashi idan investors s**a cigaba da shiga kasar irin haka.