Saƙon jajantawa daga bakin Kande Gao Basiniya mai jin yaren Hausa. A kan kisan Ummita
Kalli yadda matashi Abdullahi Umar wato 'yar dubu, ya karɓi hukuncin bulala 40 a kotu.
A watan da ya gabata ne dai wani bidiyo ya karaɗe shafukan sa da zumunta inda shi Abdullahin ya bayyana a ciki ya raba ƙafafuwansa a kan kabarin wata da bayanai suka nuna mahaifiyar wata ce da suka yi rigima da ita.
👉 www.hausateller.com
Hoton Bidiyo: Adamu Aleru ke nan ɗan fashin daji a wani ɓangare na cikin hirarsa da BBC. A cikin wannan hirar ne ya bayyana cewa shi ba ya kidinapin, shi kashewa yake yi.
🎥:BBC Hausa
HALIN GALLAZAWAR DA MUTANEN DA AKA SACE A HADARIN JIRGIN ƘASAR ABUJA KE CIKI
Wani hoton bidiyo ya bayyana a kafafen sa da zumunta wanda ke ɗauke da mutanen da haɗarin jirgin ƙasa a ya rutsa da su a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja kimannin watanni uku da suka gabata.
A cikin hoton an nuna wasu matasa ɗauke da sanda suna ta jibgar mazaje daga cikin kamammun inda matan kuma aka nuna su suna ta kuka cikin hali mai matuƙar ban tausayi.
Daga bisani kuma wani ya tsaya gaban kamara in dai ya nuna karayarsu da ƙoƙarin gwamnati musamman kamar yadda ya ambata, da gwamnatin ta hana 'yan uwansu biyan kuɗi a sake su.
Mutumin ya kira ga shugabannin duniya da su taimaka mu su tunda "gwamnatin Najeriya ta kasa fitar da mu" a cewarsa.
Za a iya tunanwa bayan haɗarin ya gabata ne, masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da mutane da yawa daga cikinsu.
Amma daga bisani masu garkuwar sun saki bakwai daga ciki bayan karɓar kuɗin fansa tare da tattaunawa da Mawallafin Jaridar nan ta Desert Held wato Tukur Mamu.
Shagirigirbau ya fayyace ma'anar deliget🤭
Shin ka yarda da batunsa?
🎥: Musty Lala
Bidiyon yadda al'ummar Hausawa a kasuwar Alaba Rago suka tarbi jagoran Kwankwasiyya injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso
🎥: Kwankwasiyya Reporters
Ana ta ci gaba da bayyana al'ajabi game da lashe zaben fid da gwani na takarar gwamnan Adamawa da Senator A'ishatu Binani ta yi a jam'iyyar APC.
Mutane suna ta baje basirarsu wajen zuwa da gajerun bayanai ko hotuna ko bidiyo da za su gajarce kwatancen yadda abin ya faru.
Wani shahararren mai amfani da kafafen sa da zumunta wato Isah Babayo ya kawo nasa kwatancen a shafinsa na Facebook wanda kuma ya ja hankali sosai. Ga dai abinda ya ce:
"Kunga yanda ta kasance a zaben APC na fidda gwani na gomna a jihar Adamawa. Haka Sen. Binani ta ɗaga Bindow ta sauke. Ta kuma sake ɗaukan Nuhu Ribadu ta buga."
Wani hoton bidiyo ke nan dake nuna abinda ya biyo bayan tashin bom a wata makaranta dake Sabon Gari a Kano a safiyar Talatar nan ta 17 ga watan Mayu, 2020.
Wani mazaunin unguwar Sabon Garin ne ya ɗauka.
Ka ga bidiyon 'ɗan KAROTA' mai tamɓele?
To ba 'ɗan KAROTA ba ne. Ya faɗa da bakinsa cewa sato rigar ya yi.
HUKUMAR KAROTA TA NESANTA KANTA DA JAMI'IN NAN MAI TAMƁELE
Hukumar KAROTA a jihar Kano ta bakin kakakinta, Nabulusi Abubakar Ƙofar Na'isa, ta nisanta kanta da wani jami'i wanda bidiyonsa ya cikin kafafen sa da zumunta a jiya.
Bidiyon ya nuna wannan mutumi ɗauke da kwalbar giya yana tamɓele a wani kwararo da ake zaton cikin unguwar Sabon Gari ne. Abinda ya jawo hankalin mutane a kan wannan ɗan maye shi ne kasancewar yana sanye da rigar aiki ta 'yan KAROTA.
Da yake jawabi, kakakin ya ce sun samu nasarar cafke wannan ɗan maye sa'annan sun damka shi a hannun 'yan Hisba inda ake sa ran za a yi ma sa hukunci daidai da abinda ya yi.
A cikin sanarwar an bayyana jin dadin shugaban KAROTA ga al'ummar jihar Kano bisa haɗin kan da ake ba shi waje saka ɗa'a a zukatan masu amfani da ababen hawa tare da godiya bisa bayyana mu su wanna ɗan maye da aka yi a kan kari.
YAU TAKE SALLAH
Allah Ya maimaita mana
#eidulfitr2022