Sokeza Post

Sokeza Post Sokeza Hausa Sabuwar kafar watsa Labarai ta Nigeria. Muna watsa Labarai Siyasa, kasuwanci, wasani, nishadi, da sauransu

Kotu ta ba Nnamdi Kanu izinin kallon wasan kwallon Atletico da Madrid a La Liga, Sannan Premier League, gasar zakarun Tu...
18/05/2022

Kotu ta ba Nnamdi Kanu izinin kallon wasan kwallon Atletico da Madrid a La Liga, Sannan Premier League, gasar zakarun Turai Final da sauran wasannin da ya zabi kallo.

Mai shari’a Nyako ta umarci hukumar DSS da ta tabbatar da lamarin.

YANZU-YANZU: Gwamnan Jihar Sokoto Yana Zaman Gaggawa Da Malaman Addinin Musulunci Kan Kisan Dalibar Da Tayi Batanci Akan...
13/05/2022

YANZU-YANZU: Gwamnan Jihar Sokoto Yana Zaman Gaggawa Da Malaman Addinin Musulunci Kan Kisan Dalibar Da Tayi Batanci Akan Annabi Muhammad S.A.W

Kungiyoyin siyasa dana Matasa Maza da Mata aKalla 135 a jihar Zamfara sun mika cakin kudi na 50m ga Maidaraja Gwamna Mat...
06/05/2022

Kungiyoyin siyasa dana Matasa Maza da Mata aKalla 135 a jihar Zamfara sun mika cakin kudi na 50m ga Maidaraja Gwamna Matawalle Domin siya mashi form.
Wanda mukaddashin Gwamnan jihar Malam Hassan Nasiha ya karba.

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe 'dan kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Zamfara mai ...
03/04/2022

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe 'dan kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Zamfara mai suna Abba a daren yau Lahadi.

Wata majiya ta tabbatar da cewa, ‘yan bindigar sun far wa yaron ne a kofar gidan kwamishinan inda s**a bude wa yaron wuta, bayan nan sun yi amfani da wuka s**a yanke masa hannu.

Majiyar ta ce, daga bisani sun koma wani mazaunin Shugaban Hukumar Kula da Ma’aikatan kananan hukumomi ta Jihar Zamfara inda s**a kashe daya daga cikin 'dansa mai suna Saifullahi da kuma abokinsa.

Majiyar kara da cewa, da misalin karfe 10:00 na dare gaba daya garin Tsafe ya kasance babu kowa a cikinsa don haka mutane sun kasance a cikin gida saboda tsoron halin da suke ciki.

Ya ce, jami’an tsaro na musamman sun samu nasarar fatattakar ‘yan bindigar tare da karbe harkokin tsaron garin baki daya.

LABARI DA DUMI DUMINSA: Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta yi nasarar cafke wasu masu bayarda bayanan sirri ga ‘yan f...
03/04/2022

LABARI DA DUMI DUMINSA: Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta yi nasarar cafke wasu masu bayarda bayanan sirri ga ‘yan fashin daji su ukku, Nasiru Sadi, Bala Alhassan da Aminu Abdulra’uf da ke kauyen Kabalawa a karamar hukumar Sabuwa.

Tun bayan da aka ƙirƙiri Nigeria a alif 1914, ba’a samu nagartacce kuma adalin shugaba kamar Buhari ba, Cewar Gwamna Mas...
03/04/2022

Tun bayan da aka ƙirƙiri Nigeria a alif 1914, ba’a samu nagartacce kuma adalin shugaba kamar Buhari ba, Cewar Gwamna Masari

Masari ya bayyana haka ne a jiya Asabar, yayin da ya halarci wani taro wanda waɗanda s**a anfana da shirin NSIP na gwamnatin tarayya s**a gudanar a Jihar Katsina.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya fara azumin watan Ramadan a mahaifarsa, Mafa, ya raba tsabar kudi Naira miliyan 76, da ka...
02/04/2022

Gwamna Babagana Umara Zulum ya fara azumin watan Ramadan a mahaifarsa, Mafa, ya raba tsabar kudi Naira miliyan 76, da kayan abinci ga mutane 15,327 sannan ya ziyarci asibitin garin.

Gwamnan ya jagoranci rabon kudade da kayan abinci ga mutane 15,327 da s**a hada da ‘yan gudun hijira da sauran mutane masu rauni.

Wadanda s**a ci gajiyar tallafin sun hada da mata 9,313 da maza 6,014, kowanensu an bashi N5,000 jimlar kudin N76,635,000:00.

Baya ga kudin, kowane mutum ya samu buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 da yadi biyar na Shadda, yayin da kowace mace ta samu atamfa da s**ari kilo 10.

Daga bisani ya ziyarci babbar asibitin Mafa.

Yayin da yake garin Mafa, Zulum ya duba kayayyakin aiki a babban asibitin inda ya tattauna da ma'aikatan lafiya. Gwamnan ya kasance a dakin gwaje-gwaje na asibitin, dakin tiyata da kuma ofisoshin ma’aikata.

Zulum a karshen tantancewar tasa, ya umurci babban jami’in kula da lafiya na asibitin da ya gaggauta mika bayanan bukatunsu na ci gaba da samun lafiya.

Likitan hukumar Fifa mai suna Joseph Kabungo, ya rasa ran sa bayan fusatattun magoya bayan 'yan wasan super eagles sun a...
30/03/2022

Likitan hukumar Fifa mai suna Joseph Kabungo, ya rasa ran sa bayan fusatattun magoya bayan 'yan wasan super eagles sun afka cikin filin wasa,
Bayan super eagles din sun kasa samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

Rundunar sojojin Nageria tace sun kashe mutum 12 daga yan ta'addan da s**a kai hari a Tashar Jirgin Sama na kasa da kasa...
30/03/2022

Rundunar sojojin Nageria tace sun kashe mutum 12 daga yan ta'addan da s**a kai hari a Tashar Jirgin Sama na kasa da kasa dake Kaduna a ranar asabar. Sunyi nasarar kashe su ne ta hanyar kai musu hari ta sama.

Uriah Opuene wanda shine brigadier-general kuma kwamanda na Rundunar Kaduna Division 1, shine ya bayyana hakan a ranar litinin yayin da yake zantawa da manema labarai akan al'amarin.

Jami'an Custom Na Ƙasa,Sun K**a Na'urar Leƙen Asiri Mai Tashi Sama Drones, Kayan Soja Tare Da Sauran Na'urorin Da Kuɗins...
30/03/2022

Jami'an Custom Na Ƙasa,
Sun K**a Na'urar Leƙen Asiri Mai Tashi Sama Drones, Kayan Soja Tare Da Sauran Na'urorin Da Kuɗinsu Yakai N 300M a Jihar Lagos. Waɗanda Wasu Ƴan Ta'addah S**a Shigo Dasu.

Daga jihar Lagos.
21/03/2022

Daga jihar Lagos.

Yadda wata kabila akasar Indonesia suke tono gawarwakin yan uwansu domin bikin al'ada dasuke kira Mâ'nënëè.Allah Mungode...
02/03/2022

Yadda wata kabila akasar Indonesia suke tono gawarwakin yan uwansu domin bikin al'ada dasuke kira Mâ'nënëè.

Allah Mungode Maka da Ni'imar Muslunci.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bude wani babban taro kan matsalar tsaro da aka fara a Abuja a yau Talata.
01/03/2022

Shugaba Muhammadu Buhari ya bude wani babban taro kan matsalar tsaro da aka fara a Abuja a yau Talata.

Daga Jihar Neja:A cewar Abdulbaqi Ebbo ma'aikaci a fadar Gwamnatin Neja, ’yan bindiga sun yi watsi da baburan su a kauyu...
01/03/2022

Daga Jihar Neja:

A cewar Abdulbaqi Ebbo ma'aikaci a fadar Gwamnatin Neja, ’yan bindiga sun yi watsi da baburan su a kauyukan da ke yankin Kwakuti bayan da jami’an tsaro na hadin gwiwa s**a kai farmaki kan ‘yan ta’addan.

Jami'an tsaro a jihar na ci gaba da kaddamar da hare-hare kan 'yan ta'addan dake addabar yankin a cikin dare.

DA DUMI-DUMIN SU!ALLURA NA SHIRIN TONO GARMA: Cikin fushi da bacin rai, Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya nemi kung...
01/03/2022

DA DUMI-DUMIN SU!

ALLURA NA SHIRIN TONO GARMA: Cikin fushi da bacin rai, Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya nemi kungiyar kasashen Turai ta NATO da su fada masa dalilin kisan shugaban kasar Libya Muhammadu Ghaddafi

A cikin wani faifan Bidiyo na shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa kungiyar NATO kungiya ce ta kasashen Amurka, Ingila, da Faransa da kawayen su wadanda su ke yaki ta hanyar zalunci da danne kasashen da ba su kai karfin su ba.

"Miye dalilin ku na kashe shugaban kasar Libya Muhammadu Al-Ghaddafi?"

"Na sani cewa kun kashe shi ne saboda ya ki bin ku ne, saboda ya ki mara muku baya wajen ganin kun shigo kasar sa kun cutawa al'ummar sa".

"Kun kashe shi, kun lalata kasar sa, kun kwashe dukiyar kasar sa saboda zalunci".

"Wannan shine irin zaluncin da kungiyar NATO kuke aikatawa kasashen duniya musamman na Afriaca".

"Ghaddafi shugaba ne mai son kasar sa da cigaban ta, amman kun kashe shi akan zalunci kun kwashe dukiyar kasar

Inji Putin

Da Dumi Dumi: Rasha da Ukraine sun shirya tattaunawa a yau Litinin. Ukraine ta ce a ranar Lahadin da ta gabata ta amince...
28/02/2022

Da Dumi Dumi: Rasha da Ukraine sun shirya tattaunawa a yau Litinin.

Ukraine ta ce a ranar Lahadin da ta gabata ta amince da aikewa da tawaga domin ganawa da wakilan Rasha a kan iyakar kasar da Belarus, wanda zai zama tuntubar juna ta farko da abokan gaba tun bayan barkewar yaki.

Ina kan tattaunawa da sauran masu sana’ar sarrafa siminti don rage farashin a Najeriya, domin ‘yan kasuwa suna samun aka...
28/02/2022

Ina kan tattaunawa da sauran masu sana’ar sarrafa siminti don rage farashin a Najeriya, domin ‘yan kasuwa suna samun akalla ribar Naira 800 zuwa Naira 1000 kan kowane buhu ~ Inji BUA

kamfanin simintin BUA ya ta’allaka ci gaba da hauhawar farashin siminti a kasar ga ‘yan kasuwa da ke cin kazamar riba fiye da kima a harkar siminti a kasar.

Kamfanin ya zargi ‘yan kasuwa da taka rawar gani wajen ganin farashin siminti bai sauko ba a Najeriya, lamarin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa a kai.

Shugaban kamfanin, Abdul Samad Rabiu ne ya bayyana haka a lokacin da ya gana da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Ya ce kamfanin na kan tattaunawa da sauran masu sana’ar sarrafa siminti don rage farashin siminti a Najeriya.

Arsenal New Signing....Arsenal have signed Camron Ismail for their U15 squad.
10/02/2022

Arsenal New Signing....

Arsenal have signed Camron Ismail for their U15 squad.

Address


Telephone

+2347066637955

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sokeza Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share