20/08/2026
Dan siyasar Najeriya kuma mai fafutukar kare dimokuraɗiyya, Omoyele Sowore, ya yi kira da a k**a tare da gurfanar da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, kan zarge-zargen laifuka da s**a shafi zamanin mulkinsa.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Sowore ya ce cikar Babangida shekaru 85 bai k**ata ya zama dalilin da zai ba shi kariya daga bincike ko yiwuwar fuskantar shari’a ba.
Sowore ya yi kwatankwacin lamarin da tsohon shugaban mulkin soja na Chile, Augusto Pinochet, wanda ya fuskanci k**awa da matakan shari’a lokacin da yake cikin shekaru tamanin. A cewarsa, shekaru ba su k**ata su zama cikakkiyar kariya daga ɗaukar alhaki ba.
Ya kuma yi zargin cewa akwai kisan gilla, cin zarafi, rashawa da wasu manyan take-take da ake dangantawa da mulkin Babangida, yana mai cewa ya k**ata a gudanar da bincike mai zurfi kan waɗannan zarge-zargen, sannan a gurfanar da duk wanda hujjoji s**a nuna yana da alhaki.
Wannan kalami na Sowore ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattauna gado da tasirin mulkin Babangida, wanda ya jagoranci Najeriya daga 1985 zuwa 1993, yayin da yake cika shekaru 85 da haihuwa.
📌 Source: Omoyele Sowore, X (Twitter)