Dan Bello Fans.

Dan Bello

Fans. Arewa Spotlight

Barkada Sallah from Dan Bello and Sahura.
27/05/2026

Barkada Sallah from Dan Bello and Sahura.

LABARIN ABOKAN JUNA BIYU : Abin da ke faruwa yanzu a ƙasar Senegal tsakanin Bassirou Diomaye Faye da Ousmane Sonko abin ...
26/05/2026

LABARIN ABOKAN JUNA BIYU : Abin da ke faruwa yanzu a ƙasar Senegal tsakanin Bassirou Diomaye Faye da Ousmane Sonko abin mamaki ne — kuma ana iya cewa irin sa ba kasafai aka gani ba a siyasar Afirka ta zamani.

Ousmane Sonko ne ya gina wata ƙaƙƙarfar tafiyar siyasa, kuma lokacin da matsalolin shari’a s**a hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasa, sai ya miƙa tikitin takarar ga mutumin da ya yarda da shi gaba ɗaya: Bassirou Diomaye Faye. Tare s**a lashe zaɓen shugaban ƙasa. Amma bayan sun hau mulki, rahotanni sun nuna cewa rashin jituwa kan manyan batutuwa ya fara bayyana, har hakan ya kai ga Faye cire Sonko daga mukamin Firayim Minista.

Sai kuma abin mamakin da ya biyo baya.
Cikin ƙasa da awa 24, Kakakin Majalisar Dokoki ya yi murabus, abin da ya buɗe wa Sonko hanya ta komawa siyasa — wani abu da kusan ba zai yiwu ba a yawancin tsarin siyasar Afirka.
Nan take aka mayar da Sonko ɗan majalisa, kuma a ranar guda aka zaɓe shi a matsayin Kakakin Majalisar Dokoki. Lallai abubuwa masu ban mamaki suna faruwa a Senegal.
Kuma labarin bai ƙare ba.

Yanzu duk wani motsi da ake yi yana nuna alamun shirin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2029. Mutane biyu da aka taɓa gani a matsayin amintattun abokan siyasa yanzu suna bayyana a matsayin manyan hamayyar
juna.

Ko mene ne zai biyo baya, Senegal na ci gaba da nuna wa Afirka wata irin siyasa ta daban. Girmamawa ga Senegal.
A ƙarshe, jama’a su ne s**a fi sanin shugabansu.

Amma Dai Hon. Malam Pantami Ya Janye Wannan Addu'ah ko?
26/05/2026

Amma Dai Hon. Malam Pantami Ya Janye Wannan Addu'ah ko?

An Kwarfe Malam Pantami Yaqi Kwarfuwa!!!
26/05/2026

An Kwarfe Malam Pantami Yaqi Kwarfuwa!!!

DOLE SAI KUN KULA DA YARAN KU FA: An k**a wata kirista sanye da hijabi ta sato yarinya ƙarama a gidan maƙotansu, ta nufi...
25/05/2026

DOLE SAI KUN KULA DA YARAN KU FA: An k**a wata kirista sanye da hijabi ta sato yarinya ƙarama a gidan maƙotansu, ta nufi tashar mota....

GOMNATIN JIHAR KATSINA TA DAGE SAI TAYI KARYA!!!.. : A kokarin Su na barranta kansu da Tsohon SA din Gomna Dikko Radda W...
25/05/2026

GOMNATIN JIHAR KATSINA TA DAGE SAI TAYI KARYA!!!.. : A kokarin Su na barranta kansu da Tsohon SA din Gomna Dikko Radda Wanda Aka k**a dumu-dumu da hannu ko jagorantar sace Wani karamin Yaro Dan shekara 8, s**ayi garkuwa dashi har saida s**a karbi kudin fansa.

To Abunda ya bayyana dai na Gaskiya shine shi Wannan Nura ya ajiye muqamin sa ne domin yayi Takarar majalisar jiha, wadda aka kwarfe mugun a Kwarfensus da s**ayi nasu na APC. To Amma wai sun fitar da Sanarwa dazu Wai Daman an Sallame shi tuntuni saboda ya taba karkatar da kayayyakin tallafin da za'a raba wa jama'a, kuma hakan ya s**a dakatar dashi - Inji Gwamnatin Katsina.

Saidai inda gizo ke sakar ba'a taba ganin sanarwar korar tashi ba a baya, saidai takardar ajiye aikin Sa daya rubuta da kanshi ya niqawa Gomnatin a Watan march domin yayi takara k**ar yadda doka ta tanadar ga dukkan mai riqe da muqamin Gomnati da ke son yayi takara.

Idan Gomna da Gomnatin sa na gudun jami'an ta su bata mata suna to tasan Wanda Zata dinga ba muqamai ta hanyar yin taka tsantsan wajen sanin waye Su da halayyar su. Amma banda shiririta ta Gomnatin Dikko Radda ka rasa wanda Zaba ba muqami Sai Wanda keda tarihin yin tattakin maula Daga Katsina zuwa Kano domin Taya Ganduje Murnar Zaluncin da yayi na Inconclusive kuma kayi tsammanin Kayi Abunda Ya dace?..

INNA NILLAHI WA INNAH ILAIHIN RAJI'UN.Muna cikiyar 'yan uwan wannan mutumin Wanda Mota ta bigeshi a bayan garin Zangonbu...
25/05/2026

INNA NILLAHI WA INNAH ILAIHIN RAJI'UN.

Muna cikiyar 'yan uwan wannan mutumin Wanda Mota ta bigeshi a bayan garin Zangonbuji akan titin Maiduguri zuwa Kano, Kuma Allah ya karbi rayuwarsa. Babu Wata alama Ko Wata shaida a tare dashi da zata nuna daga garin da ya fito.

Da safiyar wannan rana ta litinin akai jana'idarsa aka binne shi a makabartar zangonbuji k**ar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Allah ya jikansa da rahama, ya kyauta makwanci.

Dan Allah ayi share dinsa Ko Allah zai sa 'yan uwansa Ko wadanda s**a sanshi su gani, su San halin da yake ciki.

Sanarwa Daga.
Tanimu Inuwa Zangonbuji
Dutse L.G.A.
Jigawa state

Shi Wannan S.A din nan da aka k**a Yana jagorantar masu Garkuwa da mutane a Katsina fa makwabcin du Yaron ne. Kuma Wai h...
24/05/2026

Shi Wannan S.A din nan da aka k**a Yana jagorantar masu Garkuwa da mutane a Katsina fa makwabcin du Yaron ne. Kuma Wai hadda shi ake jaje a cikin group dinsu na Mazauna Estate dinsu. Gashi Nan hadda shi ake ta jajen batar Yaron, Bayan Su s**a sace shi!.

Amma Daman Ance irin Matasan nan ne yan yaki Halak Yaki Haram. domin kuwa ko a shekarar 2019 ance yayi tattaki Irin na Yan maula Dinnan a kasa Wai zuwa jihar kano ya Taya Ganduje Murnar cin zabe da akayi murdiya na Inconclusive, s**a Sallame shi ya koma gida Katsina.

Irin su ne fa suke rising s**ai matakin Shugabanci a Kasar Nan. Yanzu misali da ace yaci zaben da ya tsaya na Majalisar karamar hukumar su na Batsari da Fa Dan garkuwa da mutane ne zai zama Wakilin Al'ummah, yaje aje doka dashi..saboda Allah!!!

'Yan Sandan jihar Katsina Chafke Masu Garkuwa Da Mutane Domin Neman Kudin Fansa, A Ciki Hadda Wani Nura Aliyu Garwa Wand...
24/05/2026

'Yan Sandan jihar Katsina Chafke Masu Garkuwa Da Mutane Domin Neman Kudin Fansa, A Ciki Hadda Wani Nura Aliyu Garwa Wanda SSA on Community Development na Goman jihar Katsina Dikko, Wanda Ya Ajiye Muqamin shi bada dadewa ba domin yayi takara Kamar yadda Dokar zabe ta tanadar da duk Wanda keda Muqamin Siyasa Idan zaiyi takara to zai ajiye Muqamin sa.

Wannan Nura Ance shine Jagoran kungiyar Tasu, kuma maƙwabcine ga yaron da aka sace din mai shekara 8 a cikin birnin Katsina wanda akayi ta bada cigiyar shi. Masu garkuwar sun nemi kuɗin fansa har Naira miliyan 50, amma an biya Naira miliyan 17 kafin a sako yaron.

Allah Ya Cigaba da tona Muku Asiri!!!..

Work In Progress
24/05/2026

Work In Progress

Sarki Charles na Uku yayi magana kan gudummawar da Musulunci ya bayar wajen bunƙasa wayewar Yammacin duniya, inda ya ce:...
24/05/2026

Sarki Charles na Uku yayi magana kan gudummawar da Musulunci ya bayar wajen bunƙasa wayewar Yammacin duniya, inda ya ce: “Yammacin duniya na da abubuwa da dama da zai koya daga Musulunci.”

Ya bayyana irin tasirin da wayewar Musulunci ta yi a fannoni k**ar kimiyya, falsafa, gine-gine, da al’adu, tare da kira da a ƙara fahimta da kyakkyawar alaƙa tsakanin Al’ummomin Musulmi da Yammacin duniya.

Address

Rijiyar Zaki Kano
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dan Bello Fans. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share