𝐊𝐀𝐍𝐎

  • Home
  • 𝐊𝐀𝐍𝐎

𝐊𝐀𝐍𝐎 Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from 𝐊𝐀𝐍𝐎, Digital creator, .

27/01/2025

"Darajojin Sahabban Manzon Allah S'A'W, tare da Khalifa Sayyadi Ahmad Imam Rabiu Ningawa

TARIHIN SHEIKH IBRAHIM INYASS RA....Babban Malamin Musulunci Sheikh Ibrahim Inyass RA Ya Cika gwarzo a duniyar Musulmi S...
27/01/2025

TARIHIN SHEIKH IBRAHIM INYASS RA.
...Babban Malamin Musulunci Sheikh Ibrahim Inyass RA Ya Cika gwarzo a duniyar Musulmi

Sheikh Ibrahim Inyass Al Khaulaq an haife shi a ranar (26/07/1900) a kasar Senegal, mahaifin sa Alhaji Abdullahi Tijjani, Sheikh Ibrahim ya kasance shugaba kuma jagoran sufanci da darikar Tijjaniyya a Senegal da yammacin Africa.

Ya tashi bisa kularwar mahaifinsa, ya haddace Alkur’ani mai girma a hannun mahaifinsa A cikin kananan shekaru Yafa wallafa littafi yana da shekaru 21 a duniya.

Sheikh Ibrahim Inyass yana da mabiya masu dumbin yawa a duniya, mabiya darikar Tijjaniya ya kasance mutun mai muhimmancin a cikin rayuwar mabiyan sa wurin koyi da halayensa da dabi'unsa a cikin rayuwar su. Anyi masa shaida da soyayyan Annabi ﷺ. Da kuma riko da sunnar Manzon Allah SAW.

Sheikh Ibrahim Inyass shi ne dan Afirka ta Yamma na farko da ya jagoranci sallar a babban Masallacin Al-Azhar a Masar , bayan da aka yi masa lakabi da "Sheikh al-Islam". Kuma malami na farko da Sarki Faisal na Saudiyya ya ziyarta a kauyen sa (Kaolack) a Senegal.

Sheikh Ibrahim Inyass mutumin Afirka ne, ya kasance dan gwagwarmayar neman ƴanci a Afirka ta Yamma, saboda gudummawar da ya bayar don samun' Ƴanci a Ƙasashen Afirka. Ya kasance aboki kuma mai ba da shawara ga Shugaban Ghana na farko, Kwame Nkrumah, da aboko Ga Gamal Abdel Nasser da Sarki Faisal na Saudi Arabia. Kuma Sheikh Ibrahim kasance Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya tare da Faisal a matsayin Shugaba.

A shekarar 1937 lokacin da s**a haɗu da Shaykh Ibrahim a lokacin aikin Hajj a Makkah, Sarkin Kano, A Najeriya, Alhaji 'Abdullahi Bayero ya yi mubaya'a ga shehin kuma ya bayyana kansa a matsayin almajirin Sheikh Ibrahim. Wannan lamarin ya sa Sheikh Ibrahim ya sami amincewar da yawa daga fitattun shugabannin Tijānīyyah A Arewacin Najeriya da ma wasu da dama wadanda ba Yan Darikar ba.

Alhaji Abdulmalik Atta basarake ne daga Okene kuma Babban Kwamishina na farko a Najeriya A Kasar Ingila, yana daya daga cikin manyan almajiran Sheikh Ibrahim da kuma surukin shehin ta hanyar ‘yarsa Sayyida Bilkisu. Shaykh Ibrahim ya zama sanannen kuma jagoran darikun sufaye) a ko'ina cikin yankunan Kasar Hausa na Yammacin Afirka. Yana da miliyoyin Almajirai a duniya, yayi rubuce-rubuce da dama kusan sama da 75 a rayuwar sa.

Sanadiyar Shehu Ibrahim Inyass RTA Ne Gwamnatin Najeriya Ta Sanya Hutun Maulidi Ya Zamo Doka A Kasa, Bayan Shehu Ya Zo Taya Najeriya Murnan Samun 'Yanci A Shekarar lokacin ya gana da Firar minista na farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa, sai Shehu ya bashi shawara cewa tunda kai Musulmi ne, ya kamata ka sanya ranar Maulidi ya zamo ranar hutu a Najeriya.

Sheikh Ibrahim Inyass mabiyin addinin Islama, Mazhabar Maliki, Akida Ash'ariyya, Darikar Tijjaniyya. Sheikh Ibrahim Inyass ya rasu ranar 26 Yuli 1975 (shekaru 74) a wani asibitin St Thomas' Hospital, London, dake kasar United Kingdom.

Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa ya jaddada rahma a gare shi Albarkacin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaili Wasallam. Amiin

Gausiyya
27/01/2025

Gausiyya

Nagartar mutum da kyawon zuciyarsa, basu hana munanta zato, da yi masa zargi da ƙazafi.Ka tuna cewa, an zargi Manzannin ...
27/01/2025

Nagartar mutum da kyawon zuciyarsa, basu hana munanta zato, da yi masa zargi da ƙazafi.

Ka tuna cewa, an zargi Manzannin Allah da tsafi da ƙarya da taɓin hankali

Kai kuma wanene ?

Alhamdulillah Taron Maulidin Tijjaniyya Na Shekarar 2025 Daya Gudana Yau Asabar a Birnin Kano.Taro Anyishi Cikin Aminci ...
25/01/2025

Alhamdulillah

Taron Maulidin Tijjaniyya Na Shekarar 2025 Daya Gudana Yau Asabar a Birnin Kano.

Taro Anyishi Cikin Aminci Da Jin Dadi, Duk Masu Neman Masifa a Jihar Kano Insha Allah Sai Dai Su Ganta a Kansu🤲

Alhamdulillah, Sheikh ❤️
25/01/2025

Alhamdulillah, Sheikh ❤️

Sponsored."A madadin mai girma jagoran NNPP da Kwankwasiyya na Kasa, Sen.Engr.Dr. Rabi'u Musa kwankwaso PhD, da mai girm...
25/01/2025

Sponsored.

"A madadin mai girma jagoran NNPP da Kwankwasiyya na Kasa, Sen.Engr.Dr. Rabi'u Musa kwankwaso PhD, da mai girma Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba kabir Yusuf (Abba Gida Gida).

"Muna taya yan uwanmu mabiya Darikar Tijjaniyya turnar zagayowar Maulidin Maulana Sheikh Ibrahim Inyass R.T.A, wanda yake gudana yau a Garin kano. Allah ya sanya albarka, yasa ayi taro lafiya a gama lafiya. Ya kuma maida kowa gida lafiya, Amin dan Hasken Zuciyar Manzon Allah (S A W)."

Sanarwa daga Shugaban Jam'iyar NNPP Na Arewa Maso yammacin Najeriya, Hon Shehu M. Bello (Shehun Garu)Sponsored.

"A madadin mai girma jagoran NNPP da Kwankwasiyya na Kasa, Sen.Engr.Dr. Rabi'u Musa kwankwaso PhD, da mai girma Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba kabir Yusuf (Abba Gida Gida).

"Muna taya yan uwanmu mabiya Darikar Tijjaniyya turnar zagayowar Maulidin Maulana Sheikh Ibrahim Inyass R.T.A, wanda yake gudana yau a Garin kano. Allah ya sanya albarka, yasa ayi taro lafiya a gama lafiya. Ya kuma maida kowa gida lafiya, Amin dan Hasken Zuciyar Manzon Allah (S A W)."

Sanarwa daga Shugaban Jam'iyar NNPP Na Arewa Maso yammacin Najeriya, Hon Shehu M. Bello (Shehun Garu)

Alhamdulillah, Kano garin masoya Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.
25/01/2025

Alhamdulillah, Kano garin masoya Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.

Mauludin Shehu Ibrahim Inyass KANO 2025: Hotunan yadda Sayyadi Shehu Isma’il Mai Diwani ya gabatar da karatun Rihlatul H...
25/01/2025

Mauludin Shehu Ibrahim Inyass KANO 2025: Hotunan yadda Sayyadi Shehu Isma’il Mai Diwani ya gabatar da karatun Rihlatul Hijaziyya da takaitaccen tarihin zuwan Shehu Ibrahim Inyass Fadar Kano a zamanin Sarki Abdullahi Bayero.

An gabatar da karatun ne a fadar Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, a yau Alhamis, 23 ga watan Janairun 2025 gabanin Mauludin Shehu Ibrahim na kasa da za a yi a ranar Asabar, 25 ga watan Janairu, 2025

Fitowar mai martaba sarkin kano malam muhammadu sanusi || zuwa wajen taron mauludi
25/01/2025

Fitowar mai martaba sarkin kano malam muhammadu sanusi || zuwa wajen taron mauludi

KANO :- Filin taro ya fara tunbatsa, Allah ya kara mana kaunar Annabi
25/01/2025

KANO :- Filin taro ya fara tunbatsa, Allah ya kara mana kaunar Annabi

MAULIDIN KASA :- Yadda take wakana anan birnin Kano a unguwar Kofar Mata wajan filin taron Maulidin Kasa, Allah ya shiga...
24/01/2025

MAULIDIN KASA :- Yadda take wakana anan birnin Kano a unguwar Kofar Mata wajan filin taron Maulidin Kasa, Allah ya shiga lamuranmu.

KANO A YAU :- Zikirin Juma'a a fadar mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi II
24/01/2025

KANO A YAU :- Zikirin Juma'a a fadar mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi II

24/01/2025
Za'a gudanar da taron Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass Al Khaulaq RA a jihar Kano kamar yanda aka tsara gobe asabar 25/01/...
24/01/2025

Za'a gudanar da taron Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass Al Khaulaq RA a jihar Kano kamar yanda aka tsara gobe asabar 25/01/2025.

Allah ya kawo mana zaman lafiya, Allah yasa ayi taro lafiya albarkan Annabi ﷺ. Amiiiin

24/01/2025

Uban Kuturu ma yayi kaɗan wallahi!

Wannan faɗan ba da gwamna ko Sarki za ku yi ba, da Tijjanawa ƴan Faidha za ku yi!

24/01/2025

Allah ya kyauta. Taron addini ma sai sun shigo da siyasa. Allah ya shiryi mutanen nan.

Address


Telephone

+2348063602957

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when 𝐊𝐀𝐍𝐎 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to 𝐊𝐀𝐍𝐎:

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share