Basiru s ketare

Basiru s ketare Assalamu alaikum fatan alkhairi ga yan uwa musulmi ban bude page dan cinzarafi ko cinma wani burina

13/03/2022

Zan kafa ma nigeria tarihin Da baa taba kafawa a nigeria ba. cewar shugaban kasar nigeria Gen.Muhammadu buhari.

15/11/2021

Ako da wane lokaci idan muka ji yunwa Abinci muke nema.
Idan bamu lafiya asibiti muke tafiya mu Nemo maganani kota wace hanya,to akan meye zaace matsalar najeriya,Allah xaya maganin ta idan munyi magana sai ace matsalar najeriya sai addua,ba nace a a ba Dan Babu abinda ya gagari ubangiji,Amma sai Naga akwai manyan kasashe na musulunci,kamar su saudiya, libiya,Iran, sunfimu musulmai da Kuma nuna kishin Addini,Dan me su basu shiga masallaci s**ayi addua ba, domin Allah yace tashi in taimakeka, Dan haka ba addua ce kadai maganin matsalar Nigeria ba, dole ne afarka mufa ba kaji bane, baba, YA KAMATA IN AN CIRA ARINKA HURAWA, BABA!!!

02/08/2021

Shugaba Joe Biden ya ce sojojin yaƙin Amurka za su fita daga
Iraƙi a ƙarshen wannan shekarar, amma wasu sojojin za su ci
gaba da horar da rundunar sojin Iraƙin.
Sanarwar tasa ta zo ne bayan da Mista Biden ya tattauna da
Firai Ministan Iraqi Mustafa al-Kadhimi a fadar White House.
A halin yanzu akwai dakarun Amurka 2,500 a Iraƙi da ke
taimaka wa dakarun ƙasar yaƙi da mayaƙan IS da s**a rage a
ƙasar.
Mai yiwuwa adadin dakarun Amurkar ya kasance yadda yake a
yanzu amma ana ganin matakin a matsayin wani yunƙuri na
taimakon Firai Ministan na Iraƙi.
Kasancewar Amurka a Iraƙi ya zamo wata babbar matsala tun
bayan da aka kashe babban kwamandan Iran Qasem Soleimani
da shugaban wata ƙungiyar Musulmi ƴan Shi'a da Iran ke mara
wa baya a wani harin Amurka a Bagadaza a shekarar da ta
gabata.
Jam'iyyun siyasa da ke goyon bayan Iran sun buƙaci a janye
duka dakaru daga haɗin guiwar da Amurka ke jagoranta don
yaki da Is, duk da barazanar da kungiyar mai iƙirarin jihadi ke
yi.
A wani ɓangaren kuma, Amurka ta zargi masu ta da ƙayar baya
ƴan Shi'a da kai hare-haren roka da na jirgi marar matuƙi kan
sansanin sojojin Iraƙi da ke karɓar baƙuncin sojojin haɗin
guiwa don matsa masu lamba su fice.
Ga shugaban Amurka, sanarwar na alamta ƙarshen wani yaƙin
da aka fara tun zamanin tsohon Shugaba George W Bush. A
wannan shekarar ce ya sanar da ficewar dakarun Amurka daga
Afghanistan.
Dakarun da Amurka ke jagoranta sun shiga Iraƙi a 2003 don
ɓarar da mulkin Shugaba Saddam Hussein da kuma kawar da
makaman ƙare dangi da aka gano cewa babu su.
Shugaba Bush ya yi alƙawarin samar da "zaman lafiya a Iraƙi",
sai dai hakan bai kasance ba illa mummunan yaƙi.
Sojojin yaƙin Amurka sun janye daga baya a 2011. Sai dai sun
sake komawa bayan da gwamnatin Iraƙi ta buƙaci su koma
bayan shekaru uku lokacin da mayaƙan IS s**a ƙwace yankuna
da dama na ƙasar.
Bayan da sojojin s**a ci galaba a kan IS a Iraƙi a ƙarshen 2017,
dakarun Amurka sun ci gaba da zama don tabbatar da cewa IS
ba ta farfaɗo ba.

02/08/2021

Sama da yara 300 da aka sace a makarantu a Najeriya har
yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane, da yawa ba a ji
ɗuriyarsu ba kusan watanni biyu ke nan, wasu daga cikinsu ba
su fi shekara biyu da haihuwa ba.
An kuma saki sama da yara 1,000 da aka sata, wadanda ake
karbar kudaden fansa akai-akai daga hannun iyayensu,
ɗaruruwan iyalai har yanzu suna jiran labarin halin da 'ya'yansu
ke ciki.
BBC ta tattauna da iyaye da yawa game da satar 'ya'yansu da
kuma tunanin yadda za su ci gaba da barin 'ya'yansu zuwa
makaranta lokacin da ake tsaka da wannan balahira.
'Ba 'ya'yan kowa ba ne su'
Hadiza Hashim na da yara biyar ta je bakin makarantar
Islamiyyar da ke Tagina a jihar Neja, ranar 30 ga watan Mayu
lokacin da aka sace ɗaliban makarantar 134.
Walida da Rahama na cikin yara mafi kankantar shekaru- daya
shekararta biyu daya kuma uku. Daga baya suma an sake su
tare da wasu 'yan yara da ba sa iya ko tafiya sosai. Amma
sauran yayyensu uku suna can a hannun 'yan bindiga.
Babbar ita ce Umma 'yar shekara 13 tana kuma son kallan fina-
finan yara kamar Tom and Jerry tare da kannenta biyu maza
da mata biyu. Har yanzu mahaifiyarsu da ke cike da damuwa
ba ta ji labarinsu ba daga wajen masu garkuwa da mutane.
Ranar Lahadin da aka sace yaran, ta ce ta yi maza ta hanzarta
zuwa makarantar bayan jin karar bindigar da aka rika harbawa.
Abin da ya tilasta mata buya a wani wuri bayan ta ga
gwamman masu dauke da makamai sun shiga makarantar.
"Sun karya kwaɗon kofar tare da yi wa yaran ihun su cire
takalmansu, domin hana su guduwa. Nan da nan yaran s**a
fara kuka suna kiran iyayensu.
"Ina ganin ɗana dan shekara biyu na kuka kusa da wani mutum
rike da bindiga. Ya daka wa yaron tsawa, ya ce masa ''yi mana
shiru!'' saboda yana kiran sunana. A matsayina na mahaifiyarsa
ba zan iya yin komai ba a kai," in ji Hadiza.Tashin hankali ya ruɗa sauran yaran biyu. Saboda a cewar
mahaifiyarsu cikin dare sai su tashi firgice suna ihu, suna ganin
kamar za a ƙara zuwa a ɗauke su.

Address

Ketare
Kankara

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Basiru s ketare posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share


Other Social Media Agencies in Kankara

Show All