Kankara First News

Kankara First News An Kafar Kankara First News domin samar da ingantun,sahihai labarun cigaba.

SAKON GODIYA ZUWA GA MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR KATSINA MAL. FARUK LAWAL JOBE|||Sakon Godiya Daga Kungiyar Multipurpose Co...
21/03/2024

SAKON GODIYA ZUWA GA MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR KATSINA MAL. FARUK LAWAL JOBE|||

Sakon Godiya Daga Kungiyar Multipurpose Cooperetive Society Kankara Zuwa Ga Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina His Excellency Faruk Lawal Jobe.

Kungiyar 'yan kasuwa masu gudanar da hada Hadar kasuwanci a mazaunin su dake Kan titin gidan Marigayi Alhaji Babajo Lawal Sarkin Pauwa mai suna Multipurpose Cooperative Society kankara tana isar da sakon godiyar ta abisa basu tallafin kudi da Mataimakin Gwamnan Katsina Malam Faruk Lawal Jobe Ya basu.

Tallafin kudin N50,000 ya biyo ta daya daga cikin mahima kuma nawakin Mataimakin gwamnan jihar katsina M20, ya damkashine ga hannun shugaban Kungiyar Malam Bilya Hamisu Kamshi.

Ajawabin shugaban godiyar Bilya amadadin yan kungiyar ya nuna farin cikin shi abisa wannan Abun arziki da aka turo masu dashi.

Yayin mika wanna tallafi Mawakin Jobe M20 ya yace wannan tallafi ne domin a gudanar da al'ammuran na rayuwa.

Shuwagabani da 'yan kungiyar sun nuna farin cikin su gamida godiya zuwa ga Mataimakin Gwamnan abisa basu wannan abub arziki da yayi masu.

Sponsored By
M20

Dan-majilisar Dattawa Sen. Muntari Mohammed Dandutse Ya Gwagwaje Al'ummar Karamar Hukumar Kankara Da Kudade.Daga: Mannir...
21/03/2024

Dan-majilisar Dattawa Sen. Muntari Mohammed Dandutse Ya Gwagwaje Al'ummar Karamar Hukumar Kankara Da Kudade.

Daga: Mannir Idris Kankara

A yau Laraba Dan-majalisar Dattawa yankin Katsina ta kudu Sen. Muntari Mohammed Dandutse ya rabawa mutane 400 N10,000 a karamar hukumar kankara.

Hon. Abubakar Nuhu wanda shine jagoran wakilan da s**a gudanar da rabon kudaden wadanda s**a zo daga garin Funtua ya fara da bayyanawa Mutanen das**a amfana da sakon godiya daga Danmsjilisar ga Al'immar karamar hukumar ta kankara bisa nuna kauna da goyon bayan da suke nuna mashii.

Sannnan ya kuma tabbatar da akwai wasu ayyukan alheri dake tafe zuwa garin na kankara Wanda Sanatan yasamo daga tarayya daga bisani ya lissafawa al'umma yadda tsarin rabon kudin yake zuwa kaso 4.

Kason farko akwai Malamai 100, 50,50 daga Darika da Izala, Mata 100,Dattawa 100 sainkuma matasa 100 Wanda jimillar s**a kai 400 Inda kowa yasamu kunshin N10, 000 hannu da hannu.

Malam Hamisu Donawa na daya daga cikin kwamitin rabon ya bayyana sun kasa rabon shiyyoyi 11 na mazabun da karamar hukumar ta kunsa, wanda Hakan yasa mutanen wajen gari sun amfana matuka.

Daya daga cikin Malaman da s**a amfana Malam Abdulrashid ya yaba sosai da wannan tsari domin zai ragewa mutane radadin halin da ake ciki, shima Malam Isah ya godewa Danmajilisar gamida yin addu'a ta Kara samun cigaba.

Mata da Maza dama ne s**a kasance cikin farin ciki.

Nazir Isiya wanda shine mai taimakawa wajen biyan Malamai Addini ya yaba da halin dattakon da aka nuna.

Haka zalika shima Aliyu shehu dake bangaren biyan mata ya nuna godiya da yadda matan s**a nuna yayin tantacewa.

Sauran Yan kwamitin tafiyar da rabon kudin sun hada da Bature Omo, Shamsuddeen Magaji, Abdulbasir Maihoto, Danjuma Direba da Kuma Sadiq Pauwa.

Anyi rabon batare da samun Wani tarnakiba.

MACE MAI KAMAR MAZA : Mai Baiwa Gwamnan Jihar Katsina Shawarma Akan Huddatayyar Gwamnatoci Excmo. Hadiza Hassan Maikudi ...
18/03/2024

MACE MAI KAMAR MAZA : Mai Baiwa Gwamnan Jihar Katsina Shawarma Akan Huddatayyar Gwamnatoci Excmo. Hadiza Hassan Maikudi Ta Rabawa Al'umma Buhunnan Shinkafa 40.

Honorable. Hadiza Hassan Maikudi wadda itace maibaiwa Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ta bayar da manyan Buhunnan shikafa masu nauyin 50 ga al'umma.

K**ar yadda wakilin mu ya tabbatas anyi rabon shinkafar ne Farfajiyar sabuwar Kasuwar Kankara wadda akafi sani da Modern Market dake kan titin Zuwa garin Dutsinma cikin garin Kankara. Shinkafar buhunna 40 masu nauyin 50 kowannanen su.

Ayayin jawabin shi Wakilin Rabon Shinkafar Ingr. Abdulbasir Gambo Kankara ya bayyana "Wannan rabon shinkafa Hajiya Hadiza tayine domin tallafawa al'umma domin Allah da zummar ragewa jama'a wahalhalin alfarmar wantan wata na Ramadán.

Al'umma sun Yaba da yadda Ingr. Abdulbasir ya tsaya Kai da fata tun daga farko rabo har karshen rabon wantan shinkafa.

Maitaimakawa gwamnan jihar Katsina ta fannin samar da labarai daga karamar hukumar kankara Muhammad Sale OC (Manga) wanda shima dayane daga masu rabon wannnan shinkafa Kuma daga cikin matasan da suke goyawa Excmo. Hadiza Baya ya tabbatar cewa wantan kadan ne daga cikin alkairan da Hajiyar keda zummar samawa al'umma.

Wasu daga cikin wadanda s**a amfana da wantan shinkafa sun yaba da wantan taimako datayi musanman acikin irin want yanayi da ake ciki na rayuwa. Sun Kuma Yi addua'ar Allah ya jikan iyayenta yasa agama da duniya Lafiya.

Daga cikin wadanda s**ai aikin rabon sun hada da Malam Ibrahim Gerente, Excmo. Aminu Suleiman da Sauransu

📷Rana24

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Faruk Lawal Jobe Ya Kai Ziyarar Ta'azziyar Ga Iyalan Shugaban Hukumar Tsaron C-Watch Na...
23/02/2024

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Faruk Lawal Jobe Ya Kai Ziyarar Ta'azziyar Ga Iyalan Shugaban Hukumar Tsaron C-Watch Na Karamar Hukumar Kankara.

✍️Mannir Idris Kankara

A ranar Alhamis 22/2/2024 Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Maigirma Malam Faruk Lawal Jobe yakai Ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi Malam Sanusi Hassan Kankara Shugaban hukumar Tsaro ta jihar Katsina.

Malam Sanusi ya yagamu da ajalin shi tahanyar harbin bindiga awata musayar wuta da aka gwabza da Yan ta'addar daji ajiya Laraba.

Ayayin ziyarar ta'aziyyar maigirma mataimakin Gwamnan Faruk Lawal Jobe ya jajantawa Iyalan Marigayin haka zalika yayi Addu'ar naman gafara ga mamacin da fatan Aljanna ce makomar shi.

Waɗanda s**a rufa mashi baya sun hada Kwaminshinan Ayyuka na musanman Alhaji Isah Mohammed, Shugaban gudanarwar na Babban Asibitin Garin Katsina Dr. Mohammed Umar Zango da sauran Al'umma.

Yakumayi Addu'ar Allah ya kawo tabbatacen zaman lafiya a karamar hukumar Kankara, Jihar Katsina da Najeriya baki daya.

📷 Rana24

Dan Majilasar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Kankara, Faskari Da Sabuwa Ya Samawa Al'ummar Motocin Dauka Marasa ...
26/01/2024

Dan Majilasar Tarayya Mai Wakiltar Kananan
Hukumomin Kankara, Faskari Da Sabuwa Ya Samawa Al'ummar Motocin Dauka Marasa Lafiya

A ranar Alhamis 25/1/2024 Dan Majilasar , ,, mai Kananan hukumomin Kankara, Faskari Da Sabu,,wa ac tarayya Hon. Jamilu Mohammed Lion ya samar da motocin Asibiti a Kananan hukumomin dayake wakilta.

Hon. Jamilu Mohammed Lion Yana daya daga Cikin Yan Majilasar Wakilai da s**a ionsamu nasarar akarkashin Jam'iyyar PDP ga Jihar Katsina azaben gama gari daya gudana a Shekarar 2023.

Dan Majilasar Wakilan ya fara Ƙaddamar da mika motar Asibitin ne da karamar Karamar Hukumar Kankara ayau m alokacin Gudanar bikin Hon. Lion ya kuma samar da motar daukar Marasa Lafiya kirar Golf sabuwa gadagal ga Al'ummar Mazabar Garagi ta Kankara.

Haka zalika ya samar da Fayib Fayib na rijiyar tuka tuka kimanin guda 250 domin gyaran wasu rijiyoyin burtsatsen da s**a Samu matsala gamida hannuwan buga rijiyoyin burtsatsen Guda Biyu.

Hon. Jamilu lion Baitsayana Nan ba ya Samar da Buhunnan Shinkafa guda 80 dukka ga al'umma Mazabar Garagin ta Karamar Hukumar Kankara Jihar Katsina.

Shugaban Jam'iyyar PDP a karamar hukumar Kankara Hon. Amadu Mai kanananzir yayiwa mahalarta taro barka da zuwa sannan yayi kira ga al'ummar Mazabar Garagi da kada su biye wani ya rudesu ayayin gudanar da Zaɓen Cika gurbin da za'a ayi nan GABA.

Comr. Nuraddeen Adam Tina Yayi kira da jan kunne ga al'umma yankin Garagi dasu tsaya tsaf su zabi Jam'iyyar PDP a Zaɓen mazabar domin cigaba da sharbar romon demokariya.

Shugaban Matasan Jam'iyyar PDP a Mazabar Garagi Alhaji Nura ya Tabbatarwa Dan Majilasar Wakilai da yardar Allah zasu Tabbatarwa duniya Mazabar Garagi ta PDP ce, yakuma godewa Waɗannan abubuwan Alheri da Hon. lion yasamar ayankin su.

Danmajilisar inda Zaku Iya tunawa bayan Zaɓen da ya gudana abonkin takararshi na Jam'iyyar APC Hon. Dalhatu Tafoki ya garzaya kutun sauraran kararraki zabe domin kalubalantar yanda aka gudanar da Zaɓen Saboda rashin yin zabw awasu rumfunan Zaɓe daga

Lambobin Karramawa (CERTIFICATES) kuWaɗanda S**a Karasa mana karin maganar  mu na Jiya. Ku Duba Acikin CERTIFICATES  Yan...
05/01/2024

Lambobin Karramawa (CERTIFICATES) ku
Waɗanda S**a Karasa mana karin maganar mu na Jiya.
Ku Duba Acikin CERTIFICATES Yanzu.

Muna baku barka da shiga sabuwar Shekarar 2024

Daraktan Babban Asibitin Garin Katsina Dr. Mohammed Umar Zango Ya Yabawa Kungiyar Kankara APC Social Media.Shuagaban bab...
30/11/2023

Daraktan Babban Asibitin Garin Katsina Dr. Mohammed Umar Zango Ya Yabawa Kungiyar Kankara APC Social Media.

Shuagaban babban Asibitin garin Katsina Dr. Mohammed Umar Zango ya nuna farin cikin shi duba da yadda kungiyar matasa masu amfani da kafar Zamani Mai suna Kankara APC Social Media Forum ta shirya taron karrama wasu zakakuran mutane.

Taron da aka gudanar a babban dakin taron hukumar Ilmin Karamar Hukumar dake kan hanyar zuwa Funtua a garin Kankara.

Dr. Mohammed Zango ya nuna gudanar da irin wannan taron Mai hada Al'ummar daga Ma'aikatu daban daban, yakuma Kara tabbatar da cigaba da kawowa Karamar hukumar Kankara abubuwan cigaba.

Bugu da kari Dr. Zango ya godewa Al'ummar das**a baro aiyukan su zuwa wannan taro Hadi da godema wadanda s**a shirya taron har karramawa ga Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal Jobe.

Kimanin matasa 6 yasamawa abunyi acikin Yan makonni kalilan da zamanshi zama matsayin dayake Kai ahalin yanzu.

28/11/2023


Za'a Gina Filin Wasa Na Zamani A Garin Kankara Insha Allah. - Inji Alh. Surajo Mika'ilu.

✍️ Mannir Idris Kankara

Sakataren din -din-din a hukamar matasa da wasanni ta jihar Katsina Alhaji Surajo Mika'ilu ya bayyana kokarin Gwamnatin jihar Katsina afannin ganin ta habaka rayuwar matasan Jihar Katsina.

Alhaji Surajo Mika'ilu ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi daya gudanar ataron da wata kungiya ta shirya domin karrama wasu zakakurarrun mutane da s**a taka muhimmiyar rawa a fannoni daban daban ga al'uma 'Yan Asalin Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina.

Alhaji Surajo Mika'ilu wanda shine Sakataren din din din ahukumar matasa da wasanni ta Jihar Katsina ya bayyana geamnatin Jihar ta Katsina karkashin Jagorancin Malam Dikko Umar Radda Gwagwaren Katsina tareda Mataimakin shi Malam Faruk Lawal Jobe na bakin kokari domin ganin habakawa matasa hanyoyin more rayuwa a fannoni da dama na rayuwa a duk fadin Jihar.

Bugu da kari, Surajo Mika'ilu yace Akwai wata kungiya ta cigaban Kankara data kaimashi ziyara inda s**a roki Gwamnatin jihar Katsina data ginama Karamar Hukumar Kankara filin wassanni na zamani, abisa hakan Akan wannan bukatuwa yanzu haka tuni akasa saka aikin na Karamar Hukumar Kankara cikin kasafin Kuɗin kasafin Kuɗin wannan Shekarar.

Inda kara dacewa "Za'a gina Filin Wasa Na Zamani A Garin Kankara Insha Allah."

📷 Rana24

Masu zanga-zangar da aka yi haya a ofishin EU Abuja ba za su iya rubuta 'zamba' ba
07/07/2023

Masu zanga-zangar da aka yi haya a ofishin EU Abuja ba za su iya rubuta 'zamba' ba

07/07/2023

BODIYON:
Bayan Kai Ziyarar Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Faruk Lawal Jobe Da Kwana Daya.

Dubi Yadda Aka Fara Aikin Hanyar Ruwa A Gadar Kofar Kaura Under-Pass Bayan Matsalar Ambaliyar Ruwa Da Aka Fuskanta A Ranar 4/7/2023

Da Duminsa; An tabbatar da za a yi Jami'ar University Of Health Science Katsina a FuntuaA zaman da wasu masu ruwa da tsa...
05/07/2023

Da Duminsa; An tabbatar da za a yi Jami'ar University Of Health Science Katsina a Funtua

A zaman da wasu masu ruwa da tsaki na shiyar Funtua s**a yi da mai girma gwamman jihar Katsina yau Laraba a birnin tarayya Abuja, sun rika kuma gwamman ya amsa za a gudanar da Jami'ar Health Science a garin Funtua.

K**ar yadda wata majiya mai karfi ta tabbatar wa Katsina Daily News 'Yan tawagar daga shiyar ta Funtua da s**a ziyarci gwamma Radda don neman ganin an kafa Jami'ar a shiyar Funtua, sun kuma cimma matsayar da a aje jami'ar a yankin Funtua, kuma gwamma Radda ya amince da bukatunsu, kamar yadda majiyar ta tabbatar mana.

Daga cikin wadanda s**a halarci zaman da gwamna a Abuja akwai dan majalisar wakilai na mazabar Funtua/Dandume Hon Muntari Dandutse, da tsohon dan majalisar mazabar Hon Dr Mansur Abdulkadir, da ɗan Majalissar Funtua Hon Total.

Sauran sune dan majalisar Faskari Engr Samaila Muazu Bawa da shugaban karamar hukumar Faskari Hon Musa Ado da na Sabuwa Hon Faruk Hayatu da Engr Tukur Lawal da ɗan Masanin Funtua Alh Dr Umar da Amiru Sunusi da sauransu da dama.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta sa wa jami'ar hannu inda wasu takardu dake yawo a yanar gizo sun nuna yadda har gwamnatin tarayyar ta fara nada mukamai ga shuwagabannin da za su gudanar da jami'ar

Idan jami'ar ta tabbata, za ta zama ita ce jami'a ta farko a shiyar Funtua wadda ke da kananan hukumomi 11 daga cikin ƙananan hukumomi 34 da muke da su a jihar Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Ya Gana Da Kamfanonin Kwararru Akn Samar Da Kudaden Shiga.An gudanar da wannan tattaunawar aranar ...
05/07/2023

Gwamnan Jihar Katsina Ya Gana Da Kamfanonin Kwararru Akn Samar Da Kudaden Shiga.

An gudanar da wannan tattaunawar aranar Laraba, 5th Juli, 2023 a masaukin Gwamnatin Jihar Katsina dake Abuja.

Gwamnan ya karbi bakuncin kamfanoni 7 na kwarru kan harkar karbar haraji domin tallafar hukumar tattara kudaden haraji ta jihar Katsina wajen inganta kafar samun kudin shigar jihar.

Da yake jaddada kudirinsa na inganta hanyoyin samar da kudaden shiga ga jihar ba tare da ta dogara da daunin gwamnatin tarayya ba, Malam Dikko Umaru Radda ya ce gwamnatinsa ta kuduri gayyato kwararre daga cikin wadannan kamfanonin domin zamanantar da harkar samar da kudaden shiga.

Ya ce idan aka yi hakan, zai ba da dama a iya biyan albashin ma'aikata ba tare an jira dauni daga gwamnatin tarayya ba.

K**ar yadda ya ce, "mun gani da idanunmu irin alfanun yin garambawul ga hanyoyin samar da kudaden shiga, amma mun gamsu cewa za mu iya yin fiye da haka."

Malam Dikko Umaru Radda ya yi godiya ga kamfanonin kwararrin da s**a ji cewa za su taimaka wa jihar Katsina wajen ganin ta inganta hanyoyin samar da kudaden shiga a jihar.

Daya daga cikin kamfanonin mai suna Rentech Solution, lokacin da suke gabatar da irin fasahar da Allah Ya huwace musu, sun ce sun kudiri aniyar samar da hanyoyi masu sauki da shawarwarin yadda za a inganta hanyoyin samar da kudaden shiga ga jiha.

Kazalika, kamfanin, ya ce a shirye yake ya tallafi jihar Katsina ta fuskar yin garambawul ga hukumar tattara kudaden haraji ta jihar ta yadda za ta rika gudanar da aikinta a saukake da kuma tattara kudaden yadda ya dace.

Kamfanin ya yi alkawarin ba da shawarar yadda za a toshe duk wasu kofofi dake sa kudin gwamnati na zurarewa. Sauran kamfanonin kwararrin da s**a baje hajarsu gaban Gwamna Dikko Radda hada Interliwork Technologies da Primegauge Solutions, Astond Cunsult, Touch & Pay Technology LTD, da kuma Rahza Tech.

Zaman ya samu halartar Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Arc. Ahmed Musa Dangiwa; Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Hon. Jabiru Tsauri; Sakatare na Musamman, Hon. Abdullahi Turaji; Farfesa Sani Mashi, Dakta Sabiu Sani Bariki Malumfashi da sauran manyan jami’an gwamnati.

SSA Isah Miqdad,
Ofishin Daraktan Yada Labarai.
5/7/2023.

05/07/2023

KARIN BAYANI AKAN KAMFANIN ELEPHANT GLOBAL SERVICES

Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina  Faruk Lawal Jobe Ya Ziyarci Unguwannin Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Cikin Bi...
05/07/2023

Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Faruk Lawal Jobe Ya Ziyarci Unguwannin Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Cikin Birnin Katsina.

Daga : Mannir Idris Kankara

Mai girma mataimakin Gwamnan na jihar Katsina Faruk Lawal Jobe yakai wannan ziyarar ne aranar Talata 4 ga watan Yuli na shekarar 2023 mintoci kadan bayan tsayarwar ruwan sama kamar da bakin kwaryar da Allah ya saukar a birnin Katsina wanda hakan yasa jawo wasu Unguwannin s**a fuskanci ambaliyar ruwan.

Mataimakin Gwamnan Faruk Jobe ya nuna alhinin shi gamida jajanta ma al'umma mazauna yankin hadi da yan Kasuwan dake gudanar da Kasuwancin su awurin da ambaliyar ruwan ta shafa.

Haka zalika maigirma Jobe yakuma tabbatar masu gwamnati zata dauki matakin ganin hakan bai kara faruwa domin zasu bi dukkanin hanyoyin dakile wanzuwar hakan da yardar Allah.

Unguwannin da mataimakin Gwamnan na jihar Katsina Faruk Lawal Jobe ta kaiwa ziyarar sun kunshi Kofar Kaura Under-Pass, Kofar Marusa da Tudun Katsira.

Gwamna Radda Yasa Hannu Kan Dokar Samar Da Asusun Bai-Daya Na TSAGwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda a ranar T...
03/07/2023

Gwamna Radda Yasa Hannu Kan Dokar Samar Da Asusun Bai-Daya Na TSA

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda a ranar Talata 3 ga watan 7, 2023, ya sa hannu kan dokar da za ta kafa asusun bai-daya da jihar za ta rika amfani da shi.

Gwamnan ya yi hakan ne bisa ikon da doka karkashin sashe na (5) karamin sashe na (2) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima da dukkanin sauran karfin doka da Gwamna ke da ita s**a bashi.

Kan haka ne, dukkanin wasu kudaden shiga da duk wasu hakkokin jihar, ciki hada daunin daga gwamnatin tarayya da duk wasu kudade da za a ba jihar a matsayin gudunmuwa, za a rika tura su ta wannan asusu na bai-daya, wanda ta nan ne kuma za a rika cire duk wasu kudaden da jihar za ta yi duk hidimar dake gabanta.

SSA Isah Miqdad
Ofishin Darktan yada Labarai.
3/6/2023.

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Shirya Daukar Matasa Aiki Tareda Basu Horo Daga Kananan Hukumomi 8 Da 'Yan Bindiga S**a Addab...
01/07/2023

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Shirya Daukar Matasa Aiki Tareda Basu Horo Daga Kananan Hukumomi 8 Da 'Yan Bindiga S**a Addaba Domin Magance Matsalar Rashin Tsaro

Daga: Mannir Idris Kankara

Rahoton da wakilin mu yacruwaito ya tabbatar da cewa Mataimakin gwamnan jihar Malam Farruk Lawal Jobe ne ya bayyana haka jim kadan bayan idar da Sallar Juma’a 30/6/2023 a babban masallacin JIBWIS na garin Kankara.

Malam faruk Lawal Jobe ya ziyarci garin na kankara inda nan ne mahaifarshi domin gabatar da gaisuwar Sallah ga abokan ’yan uwa da abokan arziki.

Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewa, magance matsalolin tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, don haka akwai bukatar hadin kan al’umma don kawo karshen matsalar.

Daga nan sai ya yi kira ga shuwaganin gargajiya da su taimaka a cikin wannan tsari don tabbatar da cewa matasan da za a dauka suna da kyawawan halaye.

Malam faruk Lawal Jobe ya jaddada cewa Malaman addinin Musulunci Hadi da Sarakunan gargajiya suna da mutuntawa a cikin al'umma wanda hakan ya sa ya zama dole su shiga harkar zabar matasan da za a dauka.

Ya yi kira gare su da su ji tsoron Allah a cikin aikin da aka ba su.

Mataimakin gwamnan ya jaddada cewa gwamnati ta damu matuka da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar baki daya.

Ya kuma tabbatar ba maganar zancen yin sulhu atsakanin Gwamnatin jihar ta Katsina da'yan bindiga, saidai wanda ya ajiye makamin amatsayin mikawuya.

Hon. Jobe ya bayyana Gwamnan Jihar Malam Dikko na daya da wannan Ta'addanci yashafa domin su s**a Kashe yayanshi, haka zalika shima sanin kowane Yan Ta'addar sun sace mashi shanun dayake kiwo agarin na kankara.

Mannir Idris Kankara

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hon Faruk Lawal Jobe Ya Gwangwaje Al'ummar Mahaifar Shi Da Abun Alheri.Kasa da makonni ...
27/06/2023

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hon Faruk Lawal Jobe Ya Gwangwaje Al'ummar Mahaifar Shi Da Abun Alheri.

Kasa da makonni bakwai da karbar madakon mulki Hon. Faruk Lawal Jobe wanda shine mataimakin Gwamnan jihar Katsina Dr Dikko Umar Radda, ya gwagwaje daruruwan mutanen karamar hukumar shi ta kankara da dubunnan nairori.

Hon. Jobe ya rabawa Al'ummomin kankara wannan abun arzikin nea ranar Litinin 26/6/2022 agarin Kankara inda nan garin mahaifarshi.

Yakuma raba Waɗannan Kuɗi ne bisa tsarin kungiyoyin siyasa da Waɗanda bana siyasa ba iri daban - daban dake yankin, Ayayin rabawar kongiyoyi da s**a shafi siyasa kimanin 50 amatakin kanana da kuma manya s**a amfana.

A rahoton da muke samu ya tabbatar da Kananan kungiyoyin siyasa sun amfana da naira dubu Hamsin -Hamsin N50,000 kowanen su Waɗanda s**a hada Kungiyar Yada labarun Jam'iyyar APC a Karamar hukumar Kankara,Kungiyar siyasar matasan Dandutse, Sabon gari,kunyangizo dadai sauran su.Inda su kuma manyan kongiyoyin s**a amfana da N100,000:00 kowace Kungiya.

Abangaren kungiyoyin daba na siyasa Akwai irin su Kungiyar Derebobi reshen Karamar Hukumar Kankara da dai sauransu.

Hon. Faruk Lawal abangaren Addini nanma yarabawa Dukkanin Limaman Darika da JIBWIS dake yankin, Haka zalika ya rabawa daidaikun mutane gari N5000wasu kuma N10,0000 kowane.

Atabakin daya daga cikin hadiman Mataimakin Gwamnan ya bayyana mana cewa wannan abun Alheri Hon. Jobe yayi ne domin mutane su samu gudanar da shagulgulan Sallah lafiya cikin farin ciki.

Daga karshe ta roki Al'umma na Karamar hukumar ta Kankara,jihar Katsina da Kasa baki muyi amfani da wannan lokaci wurin yin Addu'a samu zaman lafiya akasa baki daya

Shugaban Karamar Hukumar Kankara Ya Dauki Nauyin Rubuta Jarabawar Shiga Makaratun Kimiyya Da Fasaha Na Jihar Katsina.(KS...
25/06/2023

Shugaban Karamar Hukumar Kankara Ya Dauki Nauyin Rubuta Jarabawar Shiga Makaratun Kimiyya Da Fasaha Na Jihar Katsina.(KSTEB) Ga Daliban Kankara.

Aranar Asabar 24/6/2023 Hon. Anas Isah Kankara wanda shine shugaban karamar hukumar Kankara Jihar Katsina ya daukin nauyin biyan rubuta jarabawar dalibai 'yan asalin Karamar hukumar.

Daliban daga karamar hukumar Kankara su kimanin 63 s**a rubuta jarabawar ajiya Asabar karkashin tallafawar shugaban karamar hukumar.

Sakataren Karamar hukumar Hon. Ibrahim Yakubu Kasko wanda aka gudabar da tafiyar da wannan aiki akarkashi, ya baiyana cewa karamar hukumar Kankara ce ta yanke hukuncin tallafawa dalibai yara kanana Waɗanda s**a kunshi Waɗanda ke aji 6 a matakain makaratun firamare.

Haka zalika kuma akwai dalibai amatakin karamar sakandire Waɗanda dukkanin su aka tattaro daga Makarantun lungu da sakon karamar hukumar ta Kankara batare da nuna wani banbanci Siyasa,yamki ko na addini ba.

Hon. Kasko yace makasudin yin hakan shine domin Kara farfado da martabar ilmi ga yara masu tasowa musanman ayankin karamar hukumar Kankara Jihar Katsina.

Kamsilan nadi mai kula da fannin ilmi Hon. Ibrahim Badamasi Pauwa ya kara dacewa karamar hukumar Kankara ta zartar da wannan tallafine duba targaden da akaiwa ilmi musanman afannonin kimmiya abaya asakamakon abinda ya faru a Sakandiren GSSS Kankara wanda ayanzu komi ya wuce abangaren Tsaro.

Hon. Pauwa yakuma bayyana tundaga sayen tikitin, hotuna,abinci,sha Kuɗin mota zuwa da dawowa kyauta ne.

Idan zakutuna karamar Hukumar Kankara dake yankin Katsina ta kudu dai na daya daga cikin manyan kananan hukumomin Jihar wanda inka cire karamar hukumar Katsina babu wadda takai yawan Al'umma.

Kana akyawon gari inbanda Funtua, Malumfashi,Daura da Dutsinma babu wadda tafita.

Tanada ishasshen filin kasar noma gami da dabbobi hadi da 'ya'ya masu kaifin basira, wanda asakamakon hakane ashekarar 1999 Gwamnatin jihar Katsina karkashin mulkin marigayi Malam Umar Musa 'Yar'adua ya Kafa makarantar Sakandiren kimiyya ta GSSS Kankara,wadda take taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaratan dalibai na kimiyya amatakin Jiha da Najeriya baki daya.

Har yazuwa Yanzu wannan makarata na cigaba da yaye dalibai dakeda hazaka duk da wata matsalar da akasamu asheru biyu da s**a gabata, wanda ayanzu Allah cikin ikonshi asamu nasarar samar da zaman lafiya, wanda ake saran cigaba ayyukan koyo da koyarwa a makarantar dake da mazaunin a garin na kankara kamar yadda akasaba.

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Ya Cika Alkawarin Babur Dayiwa Wani Masoyin shi mai Suna GarbaAranar Juma'a 23/6/2023 m...
23/06/2023

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Ya Cika Alkawarin Babur Dayiwa Wani Masoyin shi mai Suna Garba

Aranar Juma'a 23/6/2023 mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hon. Faruk Lawal Jobe ya damkawa wani masoyin shi babur na hawa sabo dal.

Malam Garba Ma'azu wanda dan asalin garin 'yartsamiya Sarkine dake Karkashin mulkin Karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina,ya kasance masoyi ga Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina ne wato Hon. Faruk Lawal Jobe ne.

Awata zantawa da wakilin mu yayi da Malam Garba Ma'azu ya bayyana cewa soyayyar Hon. Faruk Lawal Jobe abune dadadde wanda Allah ya dasa acikin zuciyar shi tun Lokacin da yayi takarar kujerar Sanatan Katsina ta kudu,har yazuwa lokacin daya tsaya takarar Gwamnan Jihar Katsina har zuwa wannan lokaci.

Garba Ma'azu yakara dacewa soyayyar ce tasa bayan kammala zaben gwamnoni inda Dr. Dikko Umar Radda ya lashe yayi alkawarin yin tattaki tun daga Garin 'Yar tsamiyar Sarki dake Karkashin mulkin Karamar hukumar Kankara Zuwa birnin Katsina aranar Karbar Mulki daga tsohon Gwamnan Masari zuwa Dr. Dikko,Inda Allah cikin ikonshi ya cika wannan Alkawari.

Bayan kimanin mokonni buyu wata kungiya Mai Suna Kankara Unity Forum ta gudanar da taron karramawa ga Mataimakin Gwamnan Hon. Faruk bikin daya gudana afarfajiyar Sakatariyar mulkin Karamar Hukumar Kankara a ranar 10/6/2023 wanda Malam Garba yakara takowa daga Garin'Yar tsamiyar Sarki zuwa garin domin ganawa da Masoyinshi Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina.

Malam Garba yasamu ganawa da mataimakin Gwamnan inda Nan take Hon. Faruk Lawal Jobe ya alkawaruntawa Garba sabon babur domin sauwaka mashi tafiya kasa.

Kasantuwar dan adam ajazine, Duba da yawan ayyukan da mataimakin Gwamnan suke ciki shida Gwamnan Jihar sai ayau ne Hon. Faruk ya damkawa Malam Garba Ma'azu wannan sabon babur kamar yadda kuke Kallon awadanan hotuna.

Duk dacewa lokacin da aka dauka sun fara jawo Cece kuce gawasu a kafar sada zumunta ta Zamani.

Maimakon Elrufai ya je ya ajiye kudinmu a banki, sai ya je ya gina duk wannan abubuwanElrufai Barnar ka ba ta misaltuwa....
25/05/2023

Maimakon Elrufai ya je ya ajiye kudinmu a banki, sai ya je ya gina duk wannan abubuwan

Elrufai Barnar ka ba ta misaltuwa.......

Inji Imran Wakili

Shin Kun goyi bayan Wakili?

Daga Ƙarshe An K**a Ɓarawon Dake Shiga Maƙabarta Yana Sace Allunan Alama Dake Jikin Ƙabubura A Jihar Kano
25/05/2023

Daga Ƙarshe An K**a Ɓarawon Dake Shiga Maƙabarta Yana Sace Allunan Alama Dake Jikin Ƙabubura A Jihar Kano

1st KANKARA FACEBOOK CONNECT Wannan Kwamiti Suke Da Alhakin Wallafawa Da Yada Ayyuka Da Shirye Shiryen 1st Kankara Faceb...
24/05/2023

1st KANKARA FACEBOOK CONNECT
Wannan Kwamiti Suke Da Alhakin Wallafawa Da Yada Ayyuka Da Shirye Shiryen 1st Kankara Facebook Connect.

Dafatan Zamu Basu Hadin Kai Idan Kaga Sunanka Kayi Magana Da Lambar Ka Zuwaga Lambobin Dake Kasa Domin Sakaka Zaure (Group)

Kwamiti Nagaba Bayan Awa 12 Insha Allah Mungode

Signed
Mannir I. Kankara
Media And Publicity Kankara Facebook Connect✅

Ana Tsamnin Za'a Fara To ZagawaMatan Robot da ake tsammanin za su yi zagayawa a watan Satumba - Billionaire Elon MuskBil...
21/05/2023

Ana Tsamnin Za'a Fara To ZagawaMatan Robot da ake tsammanin za su yi zagayawa a watan Satumba - Billionaire Elon Musk

Billionaire Elon Musk da kamfaninsa suna kan matakin karshe na yin matar Robot. Ana sa ran za a fitar da samar da matan Robot a watan Satumba na 2023 kuma za su isa Afirka nan da Nuwamba 2023.

Mutumin da ya kera matar Robot zai yi amfani da batura masu ɗorewa daidai da yanayin al'ada. Za a yi cajin batura na tsawon kwanaki uku kawai kuma za su yi aiki na wata guda. Yin Jima'i da Matar Robot zai buƙaci Kalmar wucewa, tsari ko sawun yatsa don guje wa fushi.

Yan Jarida

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya dawo Najeriya inda ya sauka a birnin tarayya Abuja.Daga cikin waɗanda s**a t...
21/05/2023

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya dawo Najeriya inda ya sauka a birnin tarayya Abuja.

Daga cikin waɗanda s**a tarbi zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar har da Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

21/05/2023

Hon. Ibrahim Yakubu Kasko Shugaban Gidauniyar Tallawa Al'umma Mai Suna Gwagware Foundation A Karamar Hukumar Kankara Jihar Katsina

A Karo Na Biyu Hon. Nasir Rulwanu Gurbi Kamsilan Mazaɓar Pauwa A & B Dake Karamar Hukumar Kankara Ya Kara Gwangwaje Wasu...
20/04/2023

A Karo Na Biyu Hon. Nasir Rulwanu Gurbi Kamsilan Mazaɓar Pauwa A & B Dake Karamar Hukumar Kankara Ya Kara Gwangwaje Wasu Marayun Ayau.

K**ar Yadda Wakilin mu ya ruwaito mana Hon. Nasir Rulwanu Gurbi wanda shine kamsilan yankin mazabar Pauwa A&B dake Karkashin mulkin karamar hukumar Kankara Jihar Katsina yakara rabawa yara da matasa Waɗanda Iyayen su S**a rigamu gidan gaskiya tufafi domin gudanar da Shagalin Sallah karamar dake tafe.

Idandai masu Karatu zasu tuna,yau kimani mako guda kenan da wannan Kamsila ya rabawa wasu marayu hadi da marasa galihu dake Garin Gurbin kayayyakin Sallah, to yauma Hon. Nasir Rulwanu Gurbi ya kara tatraro wasu daga cikin marayun inda ya Gwangwaje su da tufafi domin su gudanar da Sallah kamar yadda masu iyaye zasuyi walwala su.

A jawabin shi Hon. Kamsilan ya bayan bayyana godiyar shi ga Allah Daya Bashi damar Gudanar da wannan gagarumin aiki wanda wasu ke ganin kamar bazaiyuyuba duba da ganin asati baya ya gudanar da irin wannan aiki inda bayan nan ya cigaba da cewa yana kuma isar da godiyar shi ga Jam'iyyar APC wadda itace wadda akarkashinta ne ya samu damar zama kamsilan.

Bugu da kari Hon Nasir ya kuma kara isar da godiyar shi zuwa ga Al'umma mazabar shi abisa goyon bayanshi ya wakilce su amatsayin kamsilan duk da akwai Waɗanda kila s**a fishi ayankin na Pauwa A &B.

Kamsilan ya tabbatar da cigaban tallafawa marayu da marasa karfi ayankin koda baya kan wannan Kujera.

Rahuton namu ya binciko mafi yawan Marayun da s**a samu amfana da tallafin sun rasa iyayensu ne ta hanyar kisa gilla daga Hannun ysn bindiga asamakon rashin tsaro wanda yawan sunkai kimanin 43 inda maza 23 s**a samu yadudduka mata 20 atamfuna.

Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara Hon. Bashir Isah Kankara wanda yasamu wakilcin Malam Aliyu Shehu ya nuna farin cikin shi da kuma tabbatar da bada goyon bayanshi akan Waɗannan ayyukan alheri dayake shimfidawa Al'ummar dayake wakilta ya kumayi fatan Alheri.

Shima Shugaban Jam'iyyar APC na karamar hukumar Kankara Hon. Mansir Jerry wanda ya samu wakilcin Sakataren Jam'iyyar Hon. Busari Kankara ya bayyana fatan Alheri duba da wani aiki ne da ake gudanawa amatakin tarayya Amma gashi Kamsila ya na gudanar da hakan ga Al'ummar Shi.

Daya daga cikin na kusada da Kamsilan Malam Sadiq Pauwa ya godewa kamsila Nasir Rulwanu bisa taimakon iri daban daban dayake Al'umma wannan yankin nasu.

Waɗanda s**a halarci taron sun hada Shugabar mata ta yankin mazabar Pauwa Malama Juma Bello Pauwa, Shugaban Kungiyar Yan APC social media forum ra Kankara,Comr. Isah Abdullahi, da Sauran Exco nayankin baki dayansu.

Zababben gwamman jihar Adamawa Fintiri da zaɓaɓɓar mataimakiyarsa Farfesa Katetapwa Farauta sun karbi takardar lashe zab...
19/04/2023

Zababben gwamman jihar Adamawa Fintiri da zaɓaɓɓar mataimakiyarsa Farfesa Katetapwa Farauta sun karbi takardar lashe zabensu a Abuja

15/04/2023
Kamsilan Mazaɓar Dan-maidaki Kankara Hon. Hassan Sufiyanu 'Yargoje Ya Gwangwaje Marayu Da Kayan Sallah.A  ranarJuma'ar  ...
15/04/2023

Kamsilan Mazaɓar Dan-maidaki Kankara Hon. Hassan Sufiyanu 'Yargoje Ya Gwangwaje Marayu Da Kayan Sallah.

A ranarJuma'ar data gabata 14/4/2023 kamsila mazabar Dan-maidaki karamar hukumar Kankara Jihar Katsina Hon. Hassan Sufiyanu 'Yargoje ya Gwangwaje marayu da kayan Sallah.

Taron raba kayan ta gudana a Farfajiyar Sakandiren Al'umma (COMMUNITY DAY SECONDARY SCHOOL) 'Yargoje dake Kan titin Zuwa garin Kankara da misalin karfe 2:30 na rana.

Yayin taron bayar da wannan kaya Mai gayya Mai aiki Hon. Hassan Sufiyanu Yargoje ya fara da bayyana godiya ga iyayen kasa da irin gudumuwar da suke bayarwa ga Al'umma,sannan ya cigaba da bayyana Nasarorin da Daya samu Acikin Shekara guda Dayayi Akan mulkin ka1msilan wannan mazaba.

Kamsilan yacigaba da bayyana Inda acikin Shekara guda yayi gyaran Riyojin burtsatse Dayayi awasu kauyukan das**a hada da Garin Yargoje,Gureta, Sabon gida,hadi da gyaran hanyar Gidan gwanki,Gidan Damo da sauran we wurare.

Bugu da kari Hon ya bayyana cewa kafin zuwa Shekara mai zuwa da yardarb Allah duk inda basu samu daya daga cikin aikin ba to da yarda
cikin Shekara daya data rage zasu maida hankali garesu domin suma su amfana.

Hon. Kamsila yayi kuma rabawa marayu su 30 Waɗanda s**a rasa iyayensu awannann mazaba kayan Sallah dinkakku domin suma suji dadi kamar yadda takwatorinsu masu iyaye da rai zasu kasance.

Abangaren shuwaganin Jam'iyyar APC ma awannan mazabar Hon. Hassan ya Rabama L.G Exco #5000 ko wannen su suma Exco mazabar ta Dan-maidaki su 26 kowane ya samu N2000

Afannin mahalarta taron sun hada da Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hon Faruk Lawal Jobe wanda yasamu wakilcin Dr. Mohammed Umar Zango,Dan-maidaki,Limamai ba garin Yargoje,shugaban Jam'iyyar APC na Mazabar Dan-maidaki,Women Leader Ra mazabar Dan-maidaki matasa na kauyukan dake karƙashin mazaɓar.

Address

Behind Lawal Primary School Kankara Jihar Katsina
Kankara

Telephone

+2347035655275

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kankara First News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kankara First News:

Videos

Share


Other Media/News Companies in Kankara

Show All

You may also like