30/03/2024
YIMA WANI YIWA KAI
Yana daga cikin abun takaici da muka tsinci kammu aciki musamman matasa.
Idan da wani hatsari zai abku (ALLAH YA KIYAYE) sai kaga mutane dayawa suna kokarin ciro wayoyinsu don daukar hatsarin maimakon kai musu dauki.
Abun mamaki kuma shine wani zaka ga yaje yana taimaka ma wadanda hatsarin ya ritsa dasu amma shima yana dakarsu a wayarsa.
Mafi munin abun shine zaka ga suna daukarsu ba tare da lura da halinda suke ciki na tsiraici ba koda kuwa mata ne.
ALLAH KA SHIRYAR DAMU HANYA MADAIDAICIYA.
Sheikh Ahmad Tijjani Gurumtum Hafizahullah