18/05/2025
Cibiyar "Beautiful Gate Centre" da haɗin gwiwar babban Sakataren Ma'aikatar jinkai na Tarayya, sun rarraba kekunan guragu 100 a Kano
Daga Ibrahim Muhammad Kano
Babban Sakataren Ma’aikatar jinkai na Tarayya, Alhaji Adamu Ƙofar Mata tare da hadin gwiwar "Beautiful Gate Handicapped People’s Centre"Jos sun raba kekunan guragu ga mutane 100 masu buƙata ta musamman ƙarƙashin ƙungiyar ci gaban Ƙofar Mata.
A yayin bikin rabon da aka gudanar a Unguwar kofar Mata, Kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Kano, Hon.Yusuf Ƙofar Mata ya yaba wa ƙoƙari da karamcin Sakataren din-din-din na Ma'aikatar jinkai na tarayya, Alhaji Adamu Ƙofar Mata, wanda ya zo da aikin da haɗin gwiwar "Beautiful Gate Centre"
Ya ce an yi wannan ƙoƙari ne ta hanyar zabo masu buƙata ta musamman daga Ƙofar Mata da kewayenta, kuma an yi nasarar ba su kekuna masu kafa uku guda 100, wanda hakan ya nuna cewa mutane da dama za su a ci gajiyar shirin.
Ya ce a madadin al’ummar unguwannin Ƙofar Mata, Zango, Zage, Dorayi A da B sun yi matukar godiya da irin wannan shiri da "Beautiful Gate Handicapped people's centre " da Sakataren dindindin na Ma'aikatar jinkai ta Ƙasa, Alhaji Adamu Ƙofar Mata. Suna kuma fatan sauran jama’a a cikin al’umma za su ci gaba da ba da gudumawa wajen ci gaban al’umma da ɗan abin da suke da shi domin kowane mutum yana da abin da zai ba da gudummawarsa ga ci gaban al'ummarsa, ko da nasiha mai kyau ne.
Saundra Yilgwan Darektan yaɗa labarai na "Beautiful Gate Handicapped people's centre " Jos, yayin da take zantawa da manema labarai ta ce, bikin rabon kekunan masu ƙafa uku na haɗin gwiwa ne tsakanin " Beautiful Gate Handicapped people's centre" da sakataren dindindin na Ma’aikatar jin kai da kula da bala’o’i, Dakta Yakub Ƙofar Mata don ba da kyautar kekunan guda 100 ga nakasassu a Ƙofar Mata da kewaye.
Ta ce irin haɗin gwiwar da s**a yi da sakataren na dindindin, wanda shine ya nemo mutanen da ke buƙatar kayayyakin sannan ya ba su jerin sunayen domin su samar da kayan ga waɗanda s**a ci gajiyar kuma sun ba su kekunan guda 100.
Sundra ta ce, suna ba da kayan kyauta ne ga waɗanda s**a ci gajiyar tallafin, saboda sun lura cewa mai buƙata ta musamman wasu daga cikin su da kyar suke zama, kuma ba su da lokacin zuwa makaranta ko wani abu, don haka abin da za su iya yi shi ne a ba agaji. Abin da ake bukata na farko shi ne ƙarfafa musu gwiwa, shi ya sa s**a bayar da wannan, an samar da dukkan kayayyakin a ofishinsu da ke Jos, sannan kuma kudin da suke hada kowane ɗaya ya kai N160,000
Jami'ar sashen watsa labarai ta "Beautiful Gate Handicapped people's center" Jos, Sandra Yilgwan ta ce ƙungiyar mai zaman kanta ce, kuma ta Kiristaci ce, amma ba sa nuna bambanci don haka ne ma ya sa kashi 80 cikin 100 na masu cin gajiyar shirin Musulmi ne, har ma suna da ma'aikata musulmi. Ba su damu da irin addinin da kake ba ko imanin ka ko kuma sashen da ka fito. Shekaru 20 kenan da kafa cibiyar da yanzu haka sun raba kekunan guragu sama da 40,000 kyauta da sauran kayayyaki ga masu buƙata ta musamman.
Hoto daga Sandra Yilgwan.