16/08/2023
Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri?
Daga Aliyu Ahmad
Cikakken sunansa shine Sheik Ahmad Aliyu Yarwa amma ana yi masa lakabi da Sheik Abul Fatahi. Ya rayu a duniya shekaru 82, kenan an haife shi a shekarar 1919. Da rasuwarsa yau shekaru 14 kenna, domin ya rasu ne a shekarar 2003.
An haife shi a wani kauye da ake kira Sandiya amma an fi saninshi da Shanduwa a yanzu, a gundumar Konduga ta jihar Borno. A nan ya taso har ya iya hawan doki da al'adun kauye.
NASABARSA: Sheikh Ahmad bin Aliyu bin Ahmad bin Aliyu bin Muh'd Mustapha bin Muh'd Mukhtar bin Adam bin Dawud bin Abdulganiyyu bin Zubair bin Abbas bin Hussain bin Suleiman bin Ishaq (ta kan wannan s**a hada kaka daya da Sheik Ahmad Tijjani) bin Aliyu Zainul Abideen bin Ahmad bin Muh'd Nafsu-Zakiyya bin Abdullahil-Khamil bin Hasanul-Musanna Bin Hassan bin Aliyu wa Fadima Bintu RASULILLAHI SAW.
Ta bangaren mahaifiya kuwa jikan Yarima Zubairu ne Sarkin Adamawa, sunanta Aishatu bintu Alh Muh'd wa Hauwa'u Sayyada Hamra 'yar Sarki Amir.
KARATUNSA ;- Ya fara karatu a gurin mahaifinsa tun yana da shekara 5 a duniya, a shekarar kuma babansa ya rasu. Shekara daya da rasuwar babansa aka taho da shi Maiduguri ya cigaba da karatu a gurin Sheikh Goni Garba, wato babansu Sheikh Abba Goni na qur'ani. Daga nan kuma ya tafi Gonori-Garuwa, inda a nan ya samu haddar Kur'ani cikakka, daga nan kuma ya doshi garin Bankure dake jihar Kano wurin Malam Abubakar Dawaki ya yi tafsiri da sauran ilimoma a gurin Maluman garin. Nan ya lakanci Larabci.
A kusa da kauyen bayan karatunsa ya fara kasuwanci, inda daga bisani ya dena kasuwancin ya cigaba da neman ilimi, inda ya dinga shiga lungu da sako na kasar nan gurin malamai domin samun ijaza da ilimai, ya je garuruwa irin su;- Katsina, Zaria da Kano. A Zaria ya je gurin Malam Na'iya da su Sheikh Ahmad bin Ibrahim da Shehu Ishaq Nama'aji. Ya kuma zauna a Kano tsawon lokaci a wurin Shehu Atiku Sanka, inda ya kara sanin shari'a da hakika.
Sheikh Aala shine ya ba shi Tijjaniyya a shekarar 1357 A.H. Sheikh Atiku Sanka ya ba shi mukaddamanci a Tijjaniyya.
Ya kuma samu ijazoji masu yawan gaske gun manyan malamai.
Shehu Adamu Azare ya ba shi ijazar karatun Kur'ani. Sheikh Muhammad Al'alawiy Al-malikiy ya ba shi ijazar karatun Hadisi. Sannan Sheik Ibrahim Nyass ya ba shi ijaza silsila Zahabiya wadda ya fi alfahari da ita. Kuma shine ya sa masa suna Abul-Fathi, wanda hakan ya sa yake son sunan.
Haka kuma marigayi Sheik Abul Fathi me kyauta ne da ba ya tsoron talauci. Yana da dalibai manya da kanana, maza da mata a fannoni daban-daban. Ya kuma bada rayuwarsa duka gurin koyarwar da matasa safe da marece a falonsa da lambunsa a dukkan fannin ilimi. A cikin azumi kuma yana tafsiri da safe.
Shine farkon wanda ya bude makarantar addini da boko me suna MADARASATUL-ANWARUL-ISLAM FI TA'ALIM WA NIZAM a Hausari a 1956 a Lamsila, Abba-ganaram ma ya bude a 1970. Makarantar ta bunkasa ya canza mata suna da MA'AHAD ALHAJ AHMAD ABULFATHI a shekarar 1991, har kwaleji ya bude me suna THANAWIYATU SHEIK ABULFATHI da ta haddar QUR'ANI a Yarwa. Shine kuma wanda ya jaddada mauludi a duk Maiduguri irin yadda ake yi yanzu.
TAFIYA-TAFIYENSA;- Tunda ya fara tafiye-tafiye bai daina ba har ya yi wafati don akan hanya ma ya rasu a gurin ziyara.
Ya je kauyuka da garuruwa da biranen jihohi da kasashe don karfafa guiwa da wa'azi da yada Tijjaniyya.
Tafiyarsa na farko yana da shekara 30 ya shiga yankin Sokoto da garuruwan kasar Nijar da Chadi da Kamaru domin yada Tijjaniyya/Faidha.
Haka kuma ya je garuwa irin su Gwandu, Jega, Gusau, Njawoy, Mayo, Ndaga, Gembu, Ngoroje, Mai-samari, Ganye, Yola da Gudummiya.
Sauran garuruwan sun hada da Zaria, Jos, Bauchi, Gombe, Akko, Bajoga, Biriyel da Yom. Haka kuma an karbe shi a Bidda a fadar Sarkin Bidda, Umar Sanda Ndiyako, ya kuma je agaye da Abuja.
Ba wai wadannan ne kadai tafiye-tafiyensa ba, sai dai su wadannan da aka ambata duk akwai kaset din su kuma suna nan ana samu a kasuwa.
A Chadi Shehu ya yi wa'azi a Ndjemena, Ammad-timan, Abashah, Bull da Bongura da sauransu.
Kafin ya isa Chadi ya biyo ta Kamaru ya yi wa'azi a kauyukan Banki, Dibili, Kusri, Gilfe. Sannan a cikin birnin Marwa da Garwa ma ya yi.
A shekarar 1432.A.H ya je Sudan a matsayin murshid, shi ma akwai kaset.
Tafiye-tafiyensa na karshe ya je Makka sau biyu ya ziyarci Annabi SAW.
Tafiya ta farko ya tafi da Muridansa 55. Tafiya ta biyu ya tafi da muridansa 66, inda a wannan tafiyar ne ya gabatar da wa'azi a cikin Madinatul-Munawaara, ya kuma je cikin Makkah ya yi, a Jiddah ma ya yi, a tafiyar sa Shehu yana gabatar da wa'azin akan sharuddan ziyarar Annabi SAW, a otal din Abu-Khalid dake cikin Madina, inda nan ma yayi wa'azi, ya gabatar da wa'azi a gidan babban Mlamin Makkah Sheikh Al'alawiy Almalikyi Alhasaniy, sannan a gidan Sheikh Hilal Hadramy ma yayi, a wani otal mai suna AL-ANBAR a Jiddda nan ma ya yi. Sayyadi Habib Badali ya gayyace sa kofar gidansa nan ma ya yi wa'azi duk a cikin garin Makka da Madina.
Shehin Malamin ya yi rubuce-rubuce masu yawa, wasu an buga wasu kuma ba a buga ba, ba fannin ilimin da be yi rubutu a kai ba, musamman Tijjaniyya da Faidha.
Ya bar ya'ya irin su Khalifa Sheikh Aliyu da sheikh Arabiy, wanda shine National Chairman Munazzama.
Ya rasu a 2003 a hadarin mota. SHEIKH EL-MISKIN ne ya yi masa sallah aka rufe shi a Yarwa.
ALLAH JADDADA MASA RAHAMA.
Cc. Khalid Yunusa Faruk Ikara