Khamis Rigasa

Khamis Rigasa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Khamis Rigasa, News & Media Website, Dattawa Road Rigasa, Kaduna.

LABARI DA ƊUMI ƊUMIN SA: Har yanzu Bazom shine shugaban ƙasar Nijar. Daga Comrd Abba Sani Pantami.Har yanzu shugaban kas...
26/07/2023

LABARI DA ƊUMI ƊUMIN SA: Har yanzu Bazom shine shugaban ƙasar Nijar.

Daga Comrd Abba Sani Pantami.

Har yanzu shugaban kasa Muhammad Bazoum yana hannun sojojin da ke kokarin yin juyin mulki a kasar, kuma fadar shugaban kasar na cigaba da tafiyar da shafukan ta na sada zumunta.

Bugu da ƙari harr zuwa yanzu babu wata sanarwar da ta bayyana cikakken halin da ake ciki a fadin kasar baki daya.”

“Abubuwa guda biyu ne kawai aka tabbatar, na farko shine jaridar "Air-Info Agadez" ta ruwaito cewa har zuwa yanzu shugaban kasar Bazoum bai sanya hannu kan takaddar ajiye mulki ba.

“Na biyu shine shugaban ECOWAS Bola Tinubu, ya tura tawagar jami'an tsaro na musamman da kuma shugaban jamhuriyar Benin Patrice Talon, da wasu tawagar tsoffin Gwamnonin Najeriya sun isa Yamai domin fara tattaunawa da sojin kasar Niger da suke tsare da Bazoum.

“Wasu gidajen Rediyo da talabijin na kasar suna cigaba da gudanar da shirye-shiryen su kamar yadda s**a saba.”

Har zuwa yanzu sojojin da ke cigaba da tsare Bazoum basu ce uffan ba, bayan sunce za su gudanar da jawabi yau da misalin karfe 8 na dare.”

“Abunda ya kamata mu cigaba da yiwa mutanen Niger shine, mu cigaba da musu Addu'a, Allah ya kare su daga makircin da ake kokarin kulla musu. Wata kila zuwa cikin dare ko zuwa da safe su bayyana halin da ake ciki a kasar.

Address

Dattawa Road Rigasa
Kaduna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Khamis Rigasa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share