Azzahara tv News 24

  • Home
  • Azzahara tv News 24

Azzahara tv News 24 Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Azzahara tv News 24, TV Channel, .

SULHU: Kungiyar jiya Hamas ta saki sojojin Isra’ila mata guda hudu da ta yi garkuwa da su a karo na biyu, bayan yarjejen...
26/01/2025

SULHU: Kungiyar jiya Hamas ta saki sojojin Isra’ila mata guda hudu da ta yi garkuwa da su a karo na biyu, bayan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu.

Inda Isra'ila ta saki Palasdinawa 200. Bayan kwashe kimanin watanni 15. Ana fafatawa tsakanin Hamas da Isra'ila.
Muhammad El-Musa
January 26th 2025

26/01/2025
*Bayan gabatar da sallolin Zuhuraini su Malam Yakub Yahaya Katsina* *sun yi bankwana da yan uwa na Da'irar Niamey sun k*...
24/01/2025

*Bayan gabatar da sallolin Zuhuraini su Malam Yakub Yahaya Katsina* *sun yi bankwana da yan uwa na Da'irar Niamey sun k**a* *hanyar su ta komawa gida.*
*Muna fatan Allah ya kaisu gida lafiya.*

*Niamey Media*
* Sayyid Zakzaky(H).*

20/01/2025
MUWASA ƘWAƘWALWA YAN UWA MAZA DA MATA 👇👇
16/01/2025

MUWASA ƘWAƘWALWA YAN UWA MAZA DA MATA 👇👇

Sidi uzairu Badamasi Yayinda Yake Gabatar Da Majalisi Agidan Jagoran Harkar Musulinci Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) . Bada...
14/01/2025

Sidi uzairu Badamasi Yayinda Yake Gabatar Da Majalisi Agidan Jagoran Harkar Musulinci Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) .

Badaru Rabiu Mai Sufi
Ug channel tv
14/1/2025

HARISAWAN AZZAHRA ZONE SUN KAMMALA PROGRAM DIN YAUMUZ-ZAHRA (S A)Harisawan Harkar Muslunci karkashin jagorancin Shaikh Z...
13/01/2025

HARISAWAN AZZAHRA ZONE SUN KAMMALA PROGRAM DIN YAUMUZ-ZAHRA (S A)

Harisawan Harkar Muslunci karkashin jagorancin Shaikh Zakzaky (H) na Azzahra zone Sun Kammala program din Mauludin Sayyeda Zahra (s a) Wanda s**a Saba shiryawa a duk shekara.

An fara program din ranar Juma'a 8/11/2024 a garin Charanci, inda akayi kacici-kacici, Gasar Al-qur'ani mai girma a daren juma'ar, Washe gari Asabar 9/11/2024 Kuma aka buga kwallon kafa tsakanin Unitotan Katsina, Kankia da Malunfashi, bayan an buga kuma aka fidda wadanda zasuyi final.

A ranar Asabar din Nan 11/1/2025 Kuma aka Ida buga wasan kwallon kafa inda aka buga final tsakanin Katsina Unit da Malunfashi Unit, inda aka tashi ci 3-4, Katsina ta Samu nasara akan Malunfashi Unit, Sai Kuma sauran wasanni k**ar; Gudun buhu, Gudun mita Dari (100 meter), sanya zare a Allura, Jan Igiya da sauransu. Sai Kuma Karate.

A jiya Kuma Lahadi akayi gaggarumin Faretin Girmamawa ga Sayyeda Zahra (s a) da safiya inda aka Yi Faretin tsakanin Unitotan Katsina, Daura, Malunfashi, Funtua, Maradi da Kankia.

Bayan an iso Filin fayis Kuma akayi display tsakanin Unitotan, bayan Nan Kuma aka rarraba kyaututtuka ga wadanda s**a samu nasara akan Gasar da akayi mabanbanta, daga karshe Kuma Malam Yakub Idris yayi jawabin rufewa.

Muna addu'ar Allah ya Kara ma jagoranmu Shaikh Zakzaky (H) lafiya da mai dakinsa Malama Zeenatu alfarmar Sayyeda Zahra (s a)





12/01/2025

13/01/2025
Arana mai k**ar ta yau neWato 13 ga Watan January 2018 Jagoran Harka musulinci a Nigeria Shekh ibraheem Zakzakiy  ya bay...
13/01/2025

Arana mai k**ar ta yau ne

Wato 13 ga Watan January 2018 Jagoran Harka musulinci a Nigeria Shekh ibraheem Zakzakiy ya bayyana karon Farko ga 'yan jarida alokacin da yake tsare a Hukumar Dss,
Yau Shekara 7 kenan.
Alokacin mulki Azzalumi Bahari.

Shekh Yakubu yahaya Katsina Akan Hanya su ta isar da sakon Allah,  Allah ta'ala ya kara maku lafiya da Juriya ya dawo ma...
08/01/2025

Shekh Yakubu yahaya Katsina
Akan Hanya su ta isar da sakon Allah, Allah ta'ala ya kara maku lafiya da Juriya ya dawo mana daku gida lafiya.

Sama'ila Sector Mai Zahra

GIRGIZA ƘASA 7/7/1446Tibet,  Chana /7/1/ 2025  yanzu wani ya kirani yana tambaya ta game da post din da nayi satin daya ...
07/01/2025

GIRGIZA ƘASA 7/7/1446

Tibet, Chana /7/1/ 2025

yanzu wani ya kirani yana tambaya ta game da post din da nayi satin daya wuce game da girgiza ƙasa da nace Akwai Hasashe yin ta a Ranar Talata 7 ga Rajab,

Da alama bai bin cika sosai ba a yau din domin yanzu Haka sama da mutum 150 ne s**a Rasu a sak**akon Girgiza kasar wace ta Faru a yau din nan Talata 7 ga watan Rajab a Garin Tibet na Kasar Chana,

"Afa amintum anyyakhsifa bikum jãnibil barri au yursila alaikum hãsibā, thumma la tajidu lakum wakílã"

Sai dai Akwai wani karin karatu game da Shi wanann Garin da Abun ya faru,

Wanda muke akai shin garin yana gefen garin Chena. Ne??

Domin ƙaruwa da wannan darasi. Domin Ayar cewa tayi

jãnibil barri, Wato girgiza kasa zata faru ne a Garin da yake gefen gari.

Yanzu karatun mu dan sanin wannan garin shin yana gefen chena??
Koko
Domin ƙaruwa da wani Ilimi gaba ɗaya,

Photon dake a kasa Rahoton Bbc ne na girgiza ƙasa da ya faru a yau ɗeen.

Sama'ila Sector Mai Zahra post.

HADUWAR DUNIYOYI YANA NUNA CEWA  DUNIYA ZATA SAMU ZAMAN LAFIYA DA ƘAUNAR JUNA. 25  Rajab 144625 January 2025,A wani Hasa...
06/01/2025

HADUWAR DUNIYOYI YANA NUNA CEWA DUNIYA ZATA SAMU ZAMAN LAFIYA DA ƘAUNAR JUNA.

25 Rajab 1446
25 January 2025,

A wani Hasashen da Nostradamus ya yi a Wata Wasika daya aika ma ɗansa Inda Yake cewa dashi: kuma bayan shekara 177, sauyi mafi girma zai kasance a duniya, Sannan kuma Hancinan duniya zasu ga mafi girman Konewa.....
A Wani Sabon Bincike na Yan Kimiya A wannan Qarni Sunyi amannar cewa haɗuwar duniyoyin na da alaƙa da wani gagarumin sauyi, da ke shigar da mutane wani yanayi na nutsuwa da kwanciyar hankali daga bala'o'in yaƙi. Hakan na nufin masifun da s**a addabi ɗan adam ka iya gushewa a samu soyayya da haɗin kai.

Niko a Nawa Hangen Banga Wanda Zai Kawo ma Wannan Duniya Sauyi ba Face MASOYAN MUMINAI MAULANA SAHIBUZAMAN (A. T F)

Abubuwa Biyu da masu Hasashe ke tunani Faruwar Su daga Ranar da Duniyoyi S**a wuce. mi Zai Faru bayan Kwana 45?? Da Gittawarsu Sa'anan kuma mafi Fata Su Shine Abinda Zai faru a Duniya Bayan kwana 130 Muna Fatan Alkairi da Tausayin Ubangiji ga Bayinsa Raunana Da Ake Zalinta a duniya Allah Gaggauta bayyanar imam MAHADI )

Jeruwar su zai kasance Ranar 25 ga Rajab 1446 nan da yan kwanika. Masu zuwa insha Allah.

Inason yin rubutu A kan Donal Troump Aman inajin tsoron ƴan kirifto,😳 A ranar 30 ga watan  Navember na ɗanyi Hasashen wa...
02/01/2025

Inason yin rubutu A kan Donal Troump Aman inajin tsoron ƴan kirifto,😳

A ranar 30 ga watan Navember na ɗanyi Hasashen wani Abu k**ar yadda yake a Photo na ɗaya cewa da Alama duniya zata samu kuɗi alokacin mulkinsa ta hanyar kirifto

sai gashi a Jiya naga labarin haka ya tabbata k**ar yadda Bbc s**a Wallafa Shafin su sun gasgata Hasashe na a kansa

k**ar yadda yake a Photo na Biyu
Magana gaskiya ya rage ma mai sonta yaje ya nemo Hadisin dake magana minene Annabi yace A kan wanda s**a ci kudin Dujal
Kamar yadda yazo a Hadisi sunna da shi'a an bayyana cewa Dujal yana da wani Jakki wanda zai rikayi ma mutane kashin kuɗi zai arzuta mutane dasu,

hasashe musumi da kirista duk ya tafi bai ɗaya a kan cewa Donal Tromp Shine Dujal a musulinci kenan k**ar yadda acikin littafin kiristoci sun bayyana sunan sa da Anty kiristiyanaty

In kai musulimi ne sai kayi bincike da kanka minene Annabi ya fada game da cin dukiyar sa sai ka yanke ma kanka Hukunci da kan ka
Faƙat.



Sama'ila Sector Mai Zahra

*YADDA TARON BIKIN MURNAR HAIHUWAR SAYYIDA ZAHRA S A YA GUDANA A ZONE D SISTERS KATSINA!*A jiya talata 1/07/1446 daidai ...
01/01/2025

*YADDA TARON BIKIN MURNAR HAIHUWAR SAYYIDA ZAHRA S A YA GUDANA A ZONE D SISTERS KATSINA!*

A jiya talata 1/07/1446 daidai da 31/12/2024 ne aka gabatar da kayataccen bikin tunawa da ranar haihuwar diyar Manzon Rahma SAW, wato Sayyida fadimatuz Zahra S A, wanda yan'uwa Mata (sisters) na zone din Sayyida Zahra S A (zone D) s**a gabatar.
An dai yi wannan taron ne sabuwar unguwa wajen asibitin Dr. Gambo,
A lokacin taron dai k**ar yadda aka saba an bude taron addu'a, sai karanta ziyarar Sayyida Zahra S A, akayi wake. Malama Mariya Zakariya ce ta gabatar da gudanarwar taron.
Malam Yakubu Idris Katsina shine babban bako mai jawabi a wajen taron, wanda bayan kammala jawabin nasa ne aka bayar da kyaututtuka wadanda s**a hada da hatsi da Certificates ga yan'uwa daban daban.
Daga ƙarshe wakiliyar zone din Malama Zulai ta gabatar da jawabin godiya a madadin daukacin yan'uwa na zone din, sannan aka yi addu'a aka sallami yan'uwa.

Ga wasu daga cikin hotunan da muka daukar maku a wajen taron.

01/01/2025

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Azzahara tv News 24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share