Dr Idris Abdul-aziz Dutsen Tanshi Bauchi Fans

Dr Idris Abdul-aziz Dutsen Tanshi Bauchi Fans ABUJA

Ta wani bangaren Kiristoci sun fi ƴan shi'a hankali domin su ba su zagin wanda s**a rayu tare da Annabi Isa 'Alaihis Sal...
29/02/2024

Ta wani bangaren Kiristoci sun fi ƴan shi'a hankali domin su ba su zagin wanda s**a rayu tare da Annabi Isa 'Alaihis Salaam amma ƴan shi'a ba su da wanda s**a zagi kaman manya daga cikin Sahabban Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama.

Yaa ka raba mu da bata.

✍️ Umar Shehu Zaria (Hafizahullah)
19 Sha'aban, 1445
(29/02/2024).

Babu mai iya bin addinin shi'a face wanda ya rasa lafiyayyen hankali.✍️ Umar Shehu Zaria
28/02/2024

Babu mai iya bin addinin shi'a face wanda ya rasa lafiyayyen hankali.

✍️ Umar Shehu Zaria

"Masu Neman Pdf Na Rubutun Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah) Na (FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBN TAIMIYYA) Zasu iya sh...
28/02/2024

"Masu Neman Pdf Na Rubutun Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah) Na (FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBN TAIMIYYA) Zasu iya shiga Wannan Link dake Kasa domin Su Mallake Shi"

https://t.me/+uB0dT0rhgY5jMzdk

28/02/2024
28/02/2024

YA SO YA WANKE KANSA:

1. Wani da ya riki yada karya hanyar neman daukakarsa a gaban mutane ya so ya wanke kansa daga karyar da ake tuhumar shi da ita to amma Allah Ya hana yiwuwar hakan.

2. Wani saurayi ya sanya vidiyo tare da sauti nasa a lokacin da yake cewa: shi bai ce harsashai 38 ba, abin da ya ce shi ne: baraguzai 38! Sai kuma saurayin ya sanya wani vidiyo tare da sauti nasa a inda yake cewa harsashai ne guda 38!

3. Lalle wajibi ne shugabannin didi'ah su ji tsoron Allah su dawo kan gaskiya da lazimtar sunnar annabinmu cikin aqida da ibada da mu'amala iya karfinsu.

Dr Ibrahim Jalo Jalingo (Hafizahullah)

28/02/2024

"HUKUNCIN MACE TA AURI BARAWO"

~Dr Bashir Aliyu Umar (Hafizahullah)

27/02/2024

"Insha Allah zan Samar Da Pdf Na (FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBN TAIMIYYA) Wallafar Dr Aliyu Muh'd Sani (H) Na Hausa Daga Cikin Rubuce Rubucen sa" idan Na Gama Zan Sanar Daku Kuma zan Tura Muku domin Ku Amfana Insha Allah"

"Kada ka yiwa Wani Mahaluki Qage ko Sharri,domin Duka biyun Suna da Guba, Mai yiwuwa ne Kaine zaka Cutu da Gubar ba shi ...
27/02/2024

"Kada ka yiwa Wani Mahaluki Qage ko Sharri,domin Duka biyun Suna da Guba, Mai yiwuwa ne Kaine zaka Cutu da Gubar ba shi ba,Ka sani cewa:Allah yana kishin bayin sa"

Sheikh Murtadha Kabeer Annaesy (Hafizahullah)

25/02/2024

SANARWA DA KUMA TOGACIYA !!!;
Mu, al'majiran Imam Dr. Idris Abdulaziz muna gargadi dakuma Janhankali cewa: Kada wata kungiya ta kuskura tasa Baki a cikin matsalar Malaminmu da Gomnatin Kaura saboda gudun kada abinda ya faru a baya ya sake faruwa, Malaminmu ba Dan wata Kungiya ba ne; Manzon Allah (S.A.W) ya ce : من حسن إسلام المرء تركه ما لا يعنيه Ma'ana yana daga cikin kyawun Musuluncin Mutun ya bar abinda bai shafeshi ba, Malaminmu Dr Imam Idris Abdulaziz yana nan akan إياك نعبد وإياك نستعين

Dutsen Tanshi Majlis Bauchi

25/02/2024

"Nima Ina Cikin Wadan da Suke da Fahimtar cewar Kada Wani Malami daga ko wacce Kungiya yace zai saka baki cikin Mas'alar da take Faruwa da Malamin mu Dr idris Abdul-aziz Bauchi. (Hafizahullah) "

Tunda Kunce Ba Matsalar Addini bace ta siyasa ce to bai kamata wani ya tsoma baki kan Mas'alar ba kowa yayi abinda ke Gaban sa'

Don Haka bama rokon Ko wacce Kungiya ko Wani malami yace zai saka baki cikin Wannan Lamarin Bama neman agajin kowa cikin Wannan Al-amarin sai na Allah kadai إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ

Fatan Mu Allah ya Samawa Malam Mafita Kuma insha Allah Allah zai Kawo Mafitar

25/02/2024

"Tsokacin Dr Muh'd Sani Umar R/Lemo (Hafizahullah) Game Da Tatsuniyar Zakzaky Ta cewar An cire Alburushi 38 Akan Sa"

Ya kamata masu kiraye kirayen a daina ɗaukar nauyin tafsirin azumi da hujjar mutane ta cikinsu suke ba ta sauraron wa'az...
25/02/2024

Ya kamata masu kiraye kirayen a daina ɗaukar nauyin tafsirin azumi da hujjar mutane ta cikinsu suke ba ta sauraron wa'azi ba, su yi kira da babbar murya ga ƴan Film da tashoshin Arewa24 da makamantansu su karkatar da akalar kuɗaɗen da za su kashe wajan shirya fina finan Ramadan da entertainments zuwa ga ciyar da miskinai, domin fa mutane ta cikinsu suke ba ta kallon Film da shaƙatawa ba.

✍️ Muhammad Auwal Nuhu Allemawy (Hafizahullah)

Littafin malaminmu Dr Muhd Sani Umar  ضوابط الجرح والتعديل عند الحافظ الذهبيyana cikin litattafan da za a yi wa ɗaliban ...
24/02/2024

Littafin malaminmu Dr Muhd Sani Umar ضوابط الجرح والتعديل عند الحافظ الذهبي
yana cikin litattafan da za a yi wa ɗaliban matakin PhD na tsangayar kimiyyar hadisi, a jami'ar musulunci ta Madina jarrabawa a kansu.

Wannan nuni ne na ƙimar ilimin Malam da wallafe wallafensa - Allah ya ƙara masa daraja da ɗaukaka-.

Amma a gida Njry da yawa ba su san ƙimar waɗannan malamai na mu ba, ballantana su anfana da su.

MAGANI A GONAR YARO....
Mal Muhammad Auwal Nuhu Allemawy

قال الإمام ابن القيم رحمه الله:"يوم الجمعة يوم عبادة، وهو في الأيام كشهر ⁧‎ #رمضان⁩ في الشهور، وساعة الإجابة فيه، كليلة ...
23/02/2024

قال الإمام ابن القيم رحمه الله:
"يوم الجمعة يوم عبادة، وهو في الأيام كشهر ⁧‎ #رمضان⁩ في الشهور، وساعة الإجابة فيه، كليلة القدر في رمضان"

"Rashin wayewa ne Ace Annabi yace kayi ka ki yi, Rashin wayewa ne Ace Annabi yace ka Bari ka ki ka Bari"Sheikh Ahmad tij...
22/02/2024

"Rashin wayewa ne Ace Annabi yace kayi ka ki yi, Rashin wayewa ne Ace Annabi yace ka Bari ka ki ka Bari"

Sheikh Ahmad tijjani guruntum hafizahullah

Bin Musa Assalafeey Aljasaweey

"Idan Kaji Tsoron Bayyana Gaskiya Don Karkayi Bakin Jini Wurin Mutane Toh Zakayi Bakin Jini Wurin Allah"Dr Idris Abdul-a...
22/02/2024

"Idan Kaji Tsoron Bayyana Gaskiya Don Karkayi Bakin Jini Wurin Mutane Toh Zakayi Bakin Jini Wurin Allah"

Dr Idris Abdul-aziz Dutsen Tanshi (Hafizahullah)

"Hattara Mutanen Kaduna Muna Yi Muku Soyayya Irin ta Musulunci Kada ku bari Wani yaje iran ya dauko Muku Aqeedar Shi'a. ...
22/02/2024

"Hattara Mutanen Kaduna Muna Yi Muku Soyayya Irin ta Musulunci Kada ku bari Wani yaje iran ya dauko Muku Aqeedar Shi'a. Bamuce ya zama dan Shi'a ba Amman idan kaga Kare yana shin shina takalmi To dauka zaiyi"

Dr Idris Abdul-aziz Dutsen Tanshi (Hafizahullah)

UMURNI DA MUMMUNAN AIKI SIFA CE TA MUNAFUKAI'Yan Boko Aqida masu tsattsauran ra'ayin kyamar Addini sun zama 'yan fashi d...
22/02/2024

UMURNI DA MUMMUNAN AIKI SIFA CE TA MUNAFUKAI

'Yan Boko Aqida masu tsattsauran ra'ayin kyamar Addini sun zama 'yan fashi da makami a kan hanya, masu tsare bayin Allah zuwa ga da'a ma Allah, ta hanyar zayyana musu munanan aiyuka munkarai a Shari'a, na al'adun Turawa, da kuma tsangwamar masu aikin wa'azi da umurni da kyakkyawa da inkarin mummunan aiki.

A kullum aikinsu shi ne tsangwamar masu wannan aiki da ya kasance cikin ginshikan Addinin Muslunci, da yi masa zagon kasa, a bisa shubuhar -wai- wani ya ce:

"Musulmi na gaske ya shagaltu da cikar imanin shi.
Musulmi mai tsatssauran ra'ayi ya shagaltu da imanin sauran mutane bayan bai gama da nashi imanin ba".

Alhali umurni da kyakkyawa da hani ga mummuna aikin Annabi (saw) ne, Allah ya ce:
{ الَّذِينَ يَتَّبِعُونَ الرَّسُولَ النَّبِيَّ الْأُمِّيَّ الَّذِي يَجِدُونَهُ مَكْتُوبًا عِنْدَهُمْ فِي التَّوْرَاةِ وَالْإِنْجِيلِ يَأْمُرُهُمْ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَاهُمْ عَنِ الْمُنْكَرِ } [الأعراف: 157]

Kuma aiki ne na Muminai, Allah ya siffanta su da cewa:
{ وَالْمُؤْمِنُونَ وَالْمُؤْمِنَاتُ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ يَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنْكَرِ } [التوبة: 71]

Kuma ya ce:
{التَّائِبُونَ الْعَابِدُونَ الْحَامِدُونَ السَّائِحُونَ الرَّاكِعُونَ السَّاجِدُونَ الْآمِرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَالنَّاهُونَ عَنِ الْمُنْكَرِ وَالْحَافِظُونَ لِحُدُودِ اللَّهِ } [التوبة: 112]

Kuma ya ce:
{الَّذِينَ إِنْ مَكَّنَّاهُمْ فِي الْأَرْضِ أَقَامُوا الصَّلَاةَ وَآتَوُا الزَّكَاةَ وَأَمَرُوا بِالْمَعْرُوفِ وَنَهَوْا عَنِ الْمُنْكَرِ } [الحج: 41]

Kuma wannan aiki ne na Annabawa da Salihan bayi cikin al'ummomi da s**a gabata, sun kasance suna umurni da wannan babban aiki, Allah ya hakaito daga Luqman ya ce:
{يَابُنَيَّ أَقِمِ الصَّلَاةَ وَأْمُرْ بِالْمَعْرُوفِ وَانْهَ عَنِ الْمُنْكَرِ } [لقمان: 17]

Saboda haka ne Allah ya umurce mu da wannan babban aiki, ya ce:
{ وَلْتَكُنْ مِنْكُمْ أُمَّةٌ يَدْعُونَ إِلَى الْخَيْرِ وَيَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنْكَرِ وَأُولَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ } [آل عمران: 104]

Kuma da wannan aiki al'ummar Annabi (saw) ta fi sauran al'umomi:
{ كُنْتُمْ خَيْرَ أُمَّةٍ أُخْرِجَتْ لِلنَّاسِ تَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَتَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنْكَرِ وَتُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ } [آل عمران: 110]

Amma sabanin wannan aiki kuma fa, na umurni da munkari a Shari'a da munanan aiyuka da hani ga kyawawa a Shari'a, AIKI NE NA MUNAFUKAI, Allah ya ce:
{ الْمُنَافِقُونَ وَالْمُنَافِقَاتُ بَعْضُهُمْ مِنْ بَعْضٍ يَأْمُرُونَ بِالْمُنْكَرِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمَعْرُوفِ } [التوبة: 67]

Saboda haka duk wanda ka ga yana zayyana wa mutane munkarin aiki a Shari'a, kuma yana hana inkarin munkarin, yana tsangwaman masu inkarin munkari, masu hani a kan Shirka da Bidi'a, da aiyukan sabo da alfasha to ka sani yana da babbar SIFA TA MUNAFUKAI. K**ar yadda muke gani 'Yan Boko Aqida masu tsattsauran ra'ayin kyamar Addini suke yi, don koyi da Turawa wajen raba Addini da rayuwa.

Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)

Masha Allah Maki Gani ya Kauda Idon Sa
21/02/2024

Masha Allah Maki Gani ya Kauda Idon Sa

Masha Allah Maki Gani Ya Kauda Idon sa
21/02/2024

Masha Allah Maki Gani Ya Kauda Idon sa

" Mafi alherin Mata itace take faranta maka idan ka kalle ta, take kuma baka idan ka umurce ta, sannan ta kiyaye kanta d...
21/02/2024

" Mafi alherin Mata itace take faranta maka idan ka kalle ta, take kuma baka idan ka umurce ta, sannan ta kiyaye kanta da dukiyarka idan baka nan "

Asslm alkmAl-Imãmu Abdul-Aziz Bn Bãz (R) ya ce: "Wanda ya kiyaye lokacinsa da ambaton Allah (S.A.W), da karatun Alƙur'ãn...
20/02/2024

Asslm alkm
Al-Imãmu Abdul-Aziz Bn Bãz (R) ya ce: "Wanda ya kiyaye lokacinsa da ambaton Allah (S.A.W), da karatun Alƙur'ãni da abota da mutanen kirki da nesa da abota da gafalallu da ashararai; zuciyarsa za tayi daɗi za tayi TAUSHI."

*[ مجموع فتاوىٰ ومقالات (٣٤٤/٥) ]*

Sheikha Aliyu Said Gamawa (H)

"Nidai har cikin raina nafi tsammani Allah yana bamu Kariya a Arewa ne albarkacin majalisan fadin Allah da manzan sa na ...
20/02/2024

"Nidai har cikin raina nafi tsammani Allah yana bamu Kariya a Arewa ne albarkacin majalisan fadin Allah da manzan sa na Alqur'ani mai girma saboda tsananin makircin da ake kulla mana da yanzun ba wanan maganar ake ba".

Prof. Muhd Sani Umar R/lemo Kano.

Ciyar da ruhin mutane da ilimi da tsoron Allah,yafi ciyar da mutane abinci.Dr Muhd Sani Umar R/Lemo (Hafizahullah)
20/02/2024

Ciyar da ruhin mutane da ilimi da tsoron Allah,
yafi ciyar da mutane abinci.

Dr Muhd Sani Umar R/Lemo (Hafizahullah)

Ka'idar Ahlus Sunna mabiya Salaf ita ce; babu wani mutum da ake karbar maganarsa kowace iri sai Manzon Allah (saw).Haka ...
20/02/2024

Ka'idar Ahlus Sunna mabiya Salaf ita ce; babu wani mutum da ake karbar maganarsa kowace iri sai Manzon Allah (saw).
Haka babu wani mutum da za a yi masa biyayya, a bi shi a kan komai sai Manzon Allah (saw).

Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)

17/02/2024

"Yanda Suke Daukar Matsayin Allah Suna Baiwa Shehunan Su"

Sheikh Alqasim Bn Umar Hotoro (Hafizahullah)

17/01/2024

Yau anshiga Kotu Kan Shari'ar Dr Idris Anbada Umarnin K**a Dr Idris Bauchi. Sauran Bayani Nazuwa

08/01/2024

"Sanin Abinda zaka Rubuta. Yana da Muhimmanci domin akwai Ranar Kare shi A Gaban Allah...

16/12/2023

"Akwai Malamai Da yawa Wadan da Suke Da fahimta Irin Ta Dr Idris Abdul-aziz (H) Sai dai kila Duniya bata san su ba sabo kila basa yin Social media shi yasa ba'a san su ba. Wasu kuma An san su Amman yanayin yanda suke isar da sakon sai ka kai hankali nesa kafin ka fahimta.

"Shi kuma Dr Idris (H) Sai Allah ya bashi Wani irin Usulubi Wanda idan yayi magana kowa sai ya fahimta. da me ilimi da jahili. da sauaran Gama gari kowa yana fahimta shi yasa idan yayi maganar sai ayi masa ca.

Hakan Yana nuna isar sakon da kuma zuwa inda ya dace yaje to ai kuwa sai muce madallah da irin wannan usulubin tunda sako yana isa inda ya kamata.

"Wannan Bawan Allah Dr Idris (H) Ina kaunar sa sabo da Allah. Sabo da shi din kaifi daya ne za'a fada maka koda bazata yi maka dadi ba. ita kuma gaskiya daman haka take kaifi daya ce.

Ranim Alkanawiy

Address

Abuja
Kado

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dr Idris Abdul-aziz Dutsen Tanshi Bauchi Fans posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category

Nearby media companies


Other Kado media companies

Show All