11/10/2020
TSAKANIN ‘YAHOO YAHOO’ DA SARS: An Kashe Maciji Ko Biri Ya Kashe Mai Gona? Daga Ashafa Murnai 0
BI PREMIUM TIMES HAUSA A KAN OCTOBER 11, 2020RA'AYI
Ban so yin wannan rubutun ba, amma ya zama dole saboda ko mun ki ko mun so, duk wani dan Najeriya dan SARS ne.
Saboda su dai jami’an SARS din nan, kaf din su daga iyayen mu sai yayyen mu, sai abokan mu, sai kannen mu da kuma ‘ya’yan mu. A cikin su babu wanda ya fado daga sama, ko aka gino a cikin kasa aka ba shi bindiga aka yi masa horon damke masu muggan laifuka.
To amma bari na fara da korafe-korafen da ake yi kan ‘Yan Sandan SARS. Na hakkake, na tabbatar da cewa da yawan jami’an SARS maketata ne. Macuta ne. Mamugunta ne, kuma masharranta ne. Mun sha buga labarai na irin azabtar da mutane da su ke yi, sai kuma yadda su ke yafa wa wanda bai ji ba, bai gani ba alkyabbar sharri, su tsare shi, su rika tatsar makudan kudade.
Da yawan ‘yan Najeriya na cewa wani lokaci dan fashi ya fi wasu jami’an SARS saukin sha’ani. Wanda aka yi wa wannan mummunar shaidar kuwa, to idan ka kira shi dan fashi, ai kuwa ya ci sunan sa.
Idan mutum zai yi tsananin binciken irin yadda ake karakainar k**a Fulanin da ke kauyukan yankin Abuja a kan wata rigima ana kullewa a ofis-ofis na SARS, zai gane kawai wasu tsirarun jami’an tsaro sun maida harkar tsaro harkar kasuwancin kudancewa lokaci daya.
Na fi karfin yi wa wani jami’in tsaro sharri ko karya. Saboda ina bukatar tsaron lafiya ta da duniya ta da kasa ta a hannun jami’an tsaro. Dama aikin su ne. Kuma dole mu gode masu.
Amma na san Bafulatanin da matar sa ta fita, ya na ta gaganiyar yadda zai kara aure. Ana cikin haka wani ya kai shi kara ofishin SARS. Kafin dangin sa su karbo shi ‘beli’ a hannun SARS, sun kashe naira 470,000. Shikenan kuma ba zancen kai shi kotu, domin ba a k**a shi da kayan kowa ba.
Ko cikin watan Satumba da ya wuce, wasu jami’an SARS daga Jihar Kaduna sun dira garin Jiwa da ke karkashin Gundumar FCT Abuja, su ka k**a wasu Fulani, su ka tsare a wani karamin ofishin su da ke wajen Kaduna.
Na san yadda ‘yan uwan su su ka rika zaryar zuwa wurin da aka tsare su tsawon kwana uku. A karshe dai su ka sayar da katon bajimin sa, su ka karbo ‘beli’, kuma maganar ta mutu.
Ire-iren wadannan labaran marasa dadin ji, zan iya cika carbi ina jera su. Duk su na nuna dayan biyu – ko dai SARS na kin tura masu laifi zuwa kotu, su karbi kudade masu yawa su sake su, ko kuma su na yi wa wanda bai ji ba, bai gani ba sharri. Su k**a shi, su tatsi makudan kudade, a karshe su sake shi bayan sum talauta shi.
Babu abu mai ciwo k**ar wani labari da PREMIUM TIMES ta taba bugawa na wani dan kasuwa da SARS su ka k**a a Lagos. Sun tatse kudaden sa. Sun azabtar da shi. A karshe iyalin sa sun yi ikirarin cewa ya mutu a hannun SARS, domin akwai rekod da ya nuna cewa ya na tsare, amma babu rwkod da ya nuna cewa an sake shi. Kuma an rasa inda ya ke.
Babu abu mai ban-takaici k**ar yadda wasu ke bayar da labarin SARS sun k**a su, amma sun kwaci kan su ta hanyar yi masu tiransifa din kudi, ko su dauki mai tsautsayi zuwa akwatin ATM, ya ciri kudi ya ba su, su yi gaba, shi kuma ya ci gaba da Allah ya isa!
Na san wani karamin ofishin SARS a cikin Abuja, wanda idan da za Kungiyoyin Kare Hakkin Jama’a za su je su yi bincike, za su gano cewa an fi kamo Fulani ana tsarewa a wurin.
A dauka ma laifi Fulanin ke yi ana kamo su. To abin daure kai za ka rika ganin dattawan Fulani na yawan zirga-zirgar zuwa karbar ‘beli’ a wurin. Za ka ga wasu sun je yau, gobe, jibi, gata. Watakila ma jiya da shekaranjiya duk sun je, wai ‘belin mai laifi’ a hannun SARS.
Idan kuma ba wani laifin da za a dade ana walle-walle ba ne, kenan duk kokarin hada kudaden ‘beli’ ake yi kenan. Wai ‘beli’.
Tsakanin ‘Yan Yahoo Yahoo Da ‘Yan Sandan SARS:
Duk mazaunin manyan biranen kudancin kasar nan, ya san sharrin ‘yan yahoo yahoo, masu sace wa mutum kudaden ajiyar sa na banki ko kuma damfarar sa ta hanyoyin sadarwar zamani daban-daban.
Tabbas ‘yan sandan SARS su na bakin kokarin su wajen dakile ‘yan yahoo yahoo (Yahoo Boys). Mu na gani kuma mu na yaba masu.
To amma wasu na wuce-makadi-da-rawa wajen yi wa matasa da yawa mummunar fahimta ko mummunar fasaara, su na yi masu kallon ‘yan yahoo. Wani ko babbar waya mai tsada aka gani a hannun sa, sai SARS su k**a shi. Wani idan ya yi aski samfurin zanko, sai a k**a shi. Abin hauahin kuma, da yawa ba gurfanar da su ake yi ba. Sai dai a tatsi kudi a hannun su, ko a yi ta jibgar wanda ba a samu kudi a jikin sa ba.
Masu zanga-zanga na da dalilai da yawa na fitowa a kushe SARS. Kuma ni dai ban ga laifin su ba. Amma a gaskiya rushe Jami’an SARS wata babbar nasara ce ga ‘yan Yahoo Boys, yaran da a yau BA su da kudin sayen ‘pure water’, gobe kuma sai su mallaki kudaden sayen gida a Dubai da Abuja Lekki Island a Lagos.
Ya zama babban kalubale ga Gwamnatin Shugaba Buhari ta lalubo inda gaskiyar matsalar ta ke, ba sai an dauki lokaci ana sa rana, ana dagawa ba.
Matsalar SARS ba karama ba ce. Ba a taron shan shayi za a magance ta ba. Domin idan an rushe su, ne dai za su koma cikin game-garin ‘yan sanda. Duk dai ana jika kenan – an canja wa hula suna zuwa tagiya.