Tijjaniya online tv

Tijjaniya online tv Annabi muhammadu yasangaibu

https://youtu.be/D7C8RGmVVGw

19/12/2020

MATA 10 WAINDA ALLAH YA
TSINE MUSU: -
ﺍﻟﻮﺍﺷﻤﺎﺕ
ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻮﺷﻤﺎﺕ
1. Mata masu
tsaga
fuskokinsu. -
ﺍﻟﻨﺎﻣﺼﺎﺕ
ﻭﺍﻟﻤﺘﻨﺼﻤﺎﺕ
2. Mata masu
aske gashin
gira. -
ﺍﻟﻤﺘﻔﻠﺠﺎﺕ
3. Mata masu
kankare hakori
(wushirya). -
ﺍﻟﻮﺍﺻﻠﺔ
ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻮﺻﻠﺔ
4. Mai 'karin
gashi da wadda
ake karamata
gashin. -
ﺍﻟﺘﻲ ﺳﺨﻂ ﻋﻠﻴﻬﺎ
ﺯﻭﺟﻬﺎ
5.Matar da
mijinta yayi
fushi da ita. -
ﺍﻟﻤﺘﺸﺒﻬﺎﺕ ﺑﺎﻟﺮﺟﺎﻝ
6. Mata masu
shigar maza. -
ﺯﻭﺍﺭﺍﺕ ﺍﻟﻘﺒﻮﺭ
7. Mata masu
yawan
ziyartar
kabur-bura
(makabarta).
- ﺍﻟﻨﺎﺋﺤﺎﺕ
8. Mata masu
kururuwa akan
mamaci. -
ﺍﻟﻤﺤﻠﻞ ﻟﻪ
9. Mata masu
auren kashe
wuta. -
ﻛﺎﺳﻴﺎﺕ ﻋﺎﺭﻳﺎﺕ
ﻣﺘﺒﺮﺟﺎﺕ
10. Mata masu
bayyana
tsiraicinsu.
Kada ku manta TSINUWA itace
nisanta daga
rahamar Allah!
ﻗﺎﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : " ﻳﺎ
ﻣﻌﺸﺮ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ
ﺗﺼﺪﻗﻦﻭﺃﻛﺜﺮﻥ ﻣﻦ
ﺍﻹﺳﺘﻐﻔﺎﺭﻓﺈﻧﻲ
ﺭﺃﻳﺘﻜﻦ ﺃﻛﺜﺮ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻨﺎﺭ " ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ
Manzon Allah (SAW)
ya ce: 'Yaku
taron mata! ku
yi sadaqa,
kuma ku yawaita neman
gafara.
(Istigfari)
domin lallai
ninagan ku
mafiya yawanku
'yanwuta
ne."Allah yakaremu. Send it to ur family n frndx

Assalamu alaikum. Manzon Allah (S.A.W) yace:kuyi kokarin danne abubuwa uku:

(1) fushi (2) Sha'awa (3) Maganganunku.

Ku himmatu danyin abubuwa 2:
(1) Ayyukan Alkhairi (2) Abokai nagari.

Kuci moriyar abubuwa 2:
(1) Lokaci (2) Karfi.

Ku nemi abubuwa 3:
(1) Gafaran Allah (2) ilmi (3) Hikima.

YA ALLAH KABAMU IKON KIYAYEWA.

Ba'a gajiya da aikin alkhairi. Daure turawa 'yan uwa musulmi domin samun lada.

25/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 27

Daga: Yaseen Bin Hussain

FATHU MAKKA (YAKIN BUDE MAKKA)

Cikin Shekara ta 8 bayan Hijiran Annabi SAW daga Makka zuwa Madina, Kafiren Makka s**a janye Kan sharudan Sulhu Hudaibiyyah. janyewarsu keda wuya, sai karfin Musulmai ya karu.

Annabi SAW ya kusanto Garin Makka da Kimanin Mayaka Dubu Goma 10,000. Yayinda labari ya isawa Kafiren, s**aga Bazasu iya yaki da Musulmai ba saboda yawansu, dayawa daga cikinsu sai s**a Musulunta cikinsu harda Sarkin Makkah wato Abu-Safiyanu.

Cikin Zikiri Sahabbai s**a Shiga Garin Makka bayan Anyi Shela an sanarda Mutanen Makka cewa duk wanda yashiga Gidan Abu-Safiyanu ya tsira, duk Wanda yashiga Gidansa shima yatsira, Amma duk Wanda yafito da Niyyan yayi fada to a bakin ransa.

Shigansu keda wuya, Annabi SAW yayi Dawafi sannan ya Shiga Dakin Ka'abah ya Rusa Dukkanin abubuwan bautarsu da Gumakan da Kafiren Makka ke bautawa wato gumaka 360, Sai sahabban Annabi SAW Suma s**ayi Dawafi akayi ta Shela acikin Makka cewa 'Gaskiya ta bayyana, Karya ta gushe.

Daga wannan Lokacin yazama Musulunci ya tsaya da kafafunsa, Musulmai a Garin Makka da Madina da Sauran garuruwa suna Addinin su cikin daular Larabawa cikin kwanciyar hankali.

National Editor
Fityanu Media

25/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 26

Daga: Yaseen Bin Hussain

SULHU HUDAIBIYYAH

Wasu daga cikin Malamai suna cewa Yakin Hudaibiyyah, wannan ya farune cikin Shekara ta 6 bayan Hijiran Annabi Muhammad SAW daga Makka zuwa Madina.

Annabi Muhammad SAW ne yafito da Sahabbansa adadinsu kimanin Dubu daya da Dari biyar 1,500, sun fita daga Madina zuwa Makkah domin suyi aikin Umura.

Yayin da Kafiren Makka s**aji labarin haka, sai s**ayi gangami, a Karshe sai s**a nemi zasuyi sulhu da Annabi Muhammad SAW, inda s**a tura mutane daban-daban cikinsu harda Khalid Bin Walid, Amma Annabi Muhammad SAW bai yarda dasu ba, saida s**a tura Suhailu Dan Amr tukunna, Annabi Muhammad SAW ya yarda da ayi sulhu dasu bisa wasu sharuda.

Sudai Kafiren Makka abunda Sukeso shine Annabi SAW karya gabatar da aikin Umura wannan Shekarar, ya Bari sai a shekara ta gaba, sai yazo yayi, Annabi SAW ya amince musu akayi sulhu Akan hakan.

Allah muna tawassuli da wannan Sulhu da akayi, Ka tabbatar damu cikin yimaka da'a da bin koyarwan Annabi Muhammad SAW. Amin.

National Editor
Fityanu Media

19/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 25

Daga: Yaseen Bin Hussain

YAKIN KHANDAQ

Yakin khandaq na daga cikin yakuna da Annabi Muhammad SAW yaje, yafaru ne shekara 5 bayan Hijiran Annabi SAW daga Makka zuwa Madina.

Wannan yakin Kafurai sun shiryashi ne domin su murkushe Musulmai Baki daya suga bayan Musulunci. bayan yanke hukunci da Kafiren Makka s**ayi da hadin bakin Yahudawa cewa, zasu Shiga garin Madina batare da Musulmai sun Shirya ba, s**ai musu farmaki su kashesu Baki daya.

Kimanin Mutum dubu Goma 10,000 ne adadin mayakan da Kafurai s**a Tara, karkashin Jagoranci da Shugabancin Abu-Safiyanu, inda a bangaren Musulmai kuma ko rabin hakan bas**ai ba.

Dajin labari cewa Kafurai suna zuwa Garin Madina, hankalin Sahabbai ya tashi domin Jin yawan Adadin mayakan Kafiren da kuma Rashin shiri da s**ayi. Annabi SAW yakira Sahabbansa domin suyi shawari, sai Salmanul-Farisi ya bada shawari da atona Rami Mai zurfi, a kewaye Madina ta yadda abokan gaba bazasu samu damar Shiga garin ba, sai aka dauki shawarinsa.

Nan take akayi gangami domin fita wajen gari a tona Rami k**an Yadda Salmanu ya bada shawari. Gamawarsu keda wuya, sai rundunar Kafurai s**a iso inda s**a Kasa Shiga Madina, akayi musayen kibiya, Kafurai s**a koma baya.

Sun Kara Dawowa abun Bai yiwu ba, har sai da s**ayi shigan bazata nan ma basuyi nasara akan Musulmai ba. Allah ya aikowa Kafurai wata Iska ta zame musu bala'i, sai s**a gudu s**a koma gida. Da ganin janyewar Kafurai, sai Musulmai ma s**a koma Madina.

Allah ya daukaka Addinin Musulunci da Musulmai ya Kaskanta Kafurci da Kafurai Albarkan Annabi Muhammad SAW. Amin

National Editor
Fityanu Media

19/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 24

Daga: Yaseen Bin Hussain

YAKIN UHUDU

Yaki na biyu Kenan da Annabi Muhammad SAW da Sahabbansa s**ayi, bayan Yakin Badar da Shekara 1, (Shekara ta 3 bayan hijira) Kafiren Makka s**ayi shiri domin daukan fansa ga wadanda aka kashe musu a Yakin Badar.

Kafiren sun fita da Runduna Mutum dubu uku 3,000 Annabi Muhammad SAW da Sahabbansa kuma Basu wuce Mutum dubu daya 1,000 ba. A hanyarsu tazuwa Filin yaki daga Madina, Munafukai Dari Ukune 300 s**a fita a cikin Musulmai s**a koma gida karkashin Jagorancin Babban Munafukinnan wato Abdullahi Dan Ubayyu. Sai ya saura Musulmai 700.

Da isarsu Uhudu Mutum 50 daga Sahabban Annabi SAW s**a hau Kan Dutse domin tabbatar da tsaro ga Musulmai, sai Annabi yayi Musu izini da cewa karsu bar Kan wannan Dutsen, koda sunga ba Musulmai ne s**ayi nasara ba. Daganan sai aka fara yaki.

SAHABBAI SUN MANTA DA UMARNIN ANNABI SAW, SUN SAUKO DAGA KAN DUTSE.

Fara yaki keda wuya, Kafiren Makka s**a Fara komawa baya, suna guduwa. Musulmai s**a bisu a baya suna yakarsu, ganin haka sai Sahabbai s**a dauka yaki ya kare anyi Nasara, s**a Shagala da kwasan Ganima, ganin haka Wanda suke Kan Dutse s**a manta da Umarnin da aka musu, s**a sauko domin samun Ganima.

Saukowansu keda wuya, Ashe rundunar Khalid dan Walid na tabayan Dutsen, kawai sai s**a kewayo da rundunarsa s**a afkawa Musulmai ta baya, ganin haka sai Wandanda ke gudu daga Kafurai s**a juyo, Nan take akasa Annabi SAW da Sahabbansa a tsakiya yaki ya koma sabo.

Basu gusheba suna fatawa a Filin Yakin ba, har Saida aka kashe dayawa daga cikin Sahabban Annabi SAW, aka raunata dayawa daga cikinsu, yakasance har shima Annabi SAW da kansa yaji raunuka.

A Wannan, Yakin Sahabbai sama da 70 ne s**ayi Shahada, daga ciki harda Baffan Annabi SAW Sayyidina Hamza, a bangaren Kafurai kuma an kashe Mutum 23. Haka Yakin Uhudu ya kasance atakaice.

Allah yayi hakane domin ya koyar damu cewa wata Rana zamuyi farin ciki wata Rana kuma Bakin ciki, wata Rana nasara wata Rana rashinta, Allah ya Kara mana Imani da juriya ya shiryar damu Hanya Madaidaiciya. Amin

National Editor
Fityanu Media

19/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 23

Daga: Yaseen Bin Hussain

YAKIN BADAR

Ranar Juma'a 18 ga watan Ramadan bayan hijira da Shekara 2 ne akayi wannan yaki, Wanda shine ya Zama yaki na Farko cikin tarihin Addinin Musulunci.

Annabi Muhammad SAW ya fita tareda Sahabbai 313, sun fita cikin Shirin yaki domin su kwace kayaki, da Dukiyoyinsu da aka kwace musu yayin barinsu Makka, yayinda Fataken ('yan Kasuwa) Quraishawa suke hanyarsu ta Dawowa daga Sham (Syria) domin kasuwanci.

Kafiren Makka dajin labarin abunda ke faruwa s**ayi Kiran gaggawa domin ayi gangami a fita yakin kare Dukiya da Mutanensu. Manyan Masu kudi cikin Kafiren Makka sune s**a dauki nauyin duk wasu wadanda zasu fita wannan Yakin.

Kimanin Kafiren Makka dubu dayane 1,000 s**a fita domin yikin kare fatake da Dukiyarsu. Annabi Muhammad SAW da Sahabbansa 313 ne kadai da Bangaren Musulmai.

Fara yaki keda wuya, sai Allah SWT ya bawa Annabinsa Nasara yakuma durkusar da Makiyan Addininsa. Kafurai 70 aka kashe a Wannan Yakin ciki harda Abu-Jahal, aka k**a Fursinonin yaki 70. cikin ikon Allah Musulmai 14 ne s**ayi Shahada.

Annabi Muhammad SAW yayi musu umarni cewa karsu cutar da Fursinonin yaki, Wanda keda Kudi fansarsa Kimanin Dirhami dubu Hudu 4,000 ne, wadanda Basuda komai kuma, Idan sun yarda zasu koyar da Yara Goma 10 a Madina Karatun Larabarci da dabarun Yaki to zasu fanshi kansu.

Wannan a takaice kenan, yadda Yakin Badar Babba ya kasance. Allah ya Kara mana lafiya da Kaunar Annabi Muhammad SAW Amin.

National Editor
Fityanu Media

19/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 22

Daga: Yaseen Bin Hussain

SHIRI DOMIN YAQI.

Annabi Muhammad SAW yayi shekara 13 Yana Kiran Al'ummah zuwa ga Allah, duk da cutarwa mai tsanani da ake Masa da Sahabbansa, Allah Bai masa izini da yayi yaqi ba, sai da yayi Hijira zuwa Madina.

Wannan Izini yabiyo bayan ganin yadda Addinin Musulunci yasamu karbuwa matuka wajen Al'ummah, Amma Manya daga Kafiren Makka da Madina sunyi dafifi domin ganin sun dakatar da Addinin Allah. Wanda Allah SWT bazai bar haka yafaru ba har sai ya cika haskensa.

Kafiren Makka sunyi Mamaki kwarai dagaske domin ganin yadda suke dayawa Musulmai kuma 'yan Kadan, suna ganin yadda sukeda Kudi da guzuri, Musulmai kuma Basuda komai, Amma sunada Allah SWT. Kuma suna ganin 'yan uwantaka na dangi da yare dake tsakaninsu, Abun kunyane ace Larabawa musamman Quraishawa suna Yaqin junansu.

Domin ganin an karya Kafiren, an nemi Kai musu Hari domin raunata harkan kasuwancinsu ne Wanda hakan shine yayi sanadiyar yakin Farko wato Yakin Badar Babba.

Annabi Muhammad SAW ya halarci yaki dakansa guda 27, daga ciki harda; Yakin Badar Babba, Yakin Uhdu, Hudaibiyyah, Fathu Makkah, Hunain da sauransu. yakinda yayi wakilci kuma baije dakansa ba 47. zanyi bayanin kadan daga cikin yakokin da Annabi SAW yaje dakansa.

Allah ya daukaka Addinin Musulunci da Musulmai, a duk inda suke, Allah ya Kaskanta Kafurci da Kafurai a duk inda suke, Amin.

National Editor
Fityanu Media

19/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 21

Daga: Yaseen Bin Hussain

HIJIRAN ANNABI SAW DAGA MAKKA ZUWA MADINA (isar Annabi SAW garin Madina)

Annabi Muhammad SAW ya isa garin Madina inda Ansar (Musulman Madina) s**a kewayeshi suna Murna suna masa Maraba da zuwa garinsu Madina, suna rera masa wannan Sananniyar wakar 'Tala'al Badru Alaina...'.

Kowa naso Annabi SAW ya sauka a gidansa, Amma Annabi SAW yayi musu ishara cewa zai Gina Masallaci da gidansa Amma a duk inda Taguwarsa tayi zango cikin Garin Madina. Bada jimawaba, bayan sake Linzamin taguwar, tayi zango a gefen Gidan Abi-Ayuba Al-Ansari.

A Gidan Abi-Ayuba Al-Ansari Annabi SAW ya zauna kafin a Gama gina Masallaci da gidansa. Aikin gayya akayi tsakanin Muhajirun (Wadanda s**ayi hijira daga Makka zuwa Madina) da Ansar (Musulman Madina) Annabi Muhammad SAW dakanshi ba'a barshi a baya wajen wannan aikin ba.

Mafi yawancin Sahabbai sun dawo Madina, wadanda s**a rage a Makka saidai Nakasassu, ko wadanda aka dauresu ko aka Kullesu. Nan take aka kafa Kasar Musulunci a Madina inda Annabi Muhammad SAW da Sahabbansa suke zaune cikin Aminci.

Ganin haka yasa Yahudawan Madina s**a Fara bayyana Gaba, Fushi da Hassada ga Musulmai da Musulunci. Annabi SAW ya kulla Alqawari dasu cewa kowa bazai cutar da kowa ba, kuma kowa zaiyi Addininsa cikin Aminci. Yahudawan Madina sune; Banu Nathir, Banu Qainuqa'a, Banu Kuraiza.

National Editor
Fityanu Media

18/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 20

Daga: Yaseen Bin Hussain

HIJIRAN ANNABI SAW DAGA MAKKA ZUWA MADINA (tafiyarsa zuwa Madina)

Annabi Muhammad SAW da Sayyidina Abubakar sun zauna a Kogon 'Saur' na tsawon kwanaki 3 domin bincike akansu ta tsagaita. Bayan Dan jagoransu wato Abdullahi Dan Uraiqidil-Laisi ya kawo musu ababen hawansu, sai s**a cigaba da tafiya har s**a isa Quba'a.

Sun isa Quba'a ne ranar 20 ga watan Rabi'il-Auwal, bayan Aiken Annabin Rahama SAW da Shekara 13, Lokacin Annabi Muhammad SAW nada Shekaru 53 a rayuwarsa na Duniya. Sunyi zango A Quba'a na wasu kwanaki inda Annabi SAW ya Gina Masallaci.

Masallacin Quba'a shine Masallaci na Farko da Annabi Muhammad SAW a Assasa, bayan sun cigaba da tafiya sai s**a haduda Jama'a masu yawa da s**azo tariyar Annabi SAW daga Madina, anan s**a hadu s**ayi sallar Juma'a. Wanda itace Juma'a ta Farko a tarihin Addinin Musulunci bayan hijirasa SAW.

National Editor
Fityanu Media

18/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 19.

Daga: Yaseen Bin Hussain

HIJIRAN ANNABI SAW DAGA MAKKA ZUWA MADINA (Fitan Annabi SAW daga garin Makka)

Annabi Muhammad SAW tareda Sayyidina Abubakar sun fita daga Makka a Wannan darenda Quraishawa s**ayi niyyan kashe Annabi SAW, tare dasu da Amiru Dan Fuhairata, da Dan jagoransu kuma Abdullahi Dan Uraiqidil-Laisi.

Sun tafi cikin wannan dare zuwa Kogon 'Saur', sun bawa Dan jagoran nasu abun hawansu yatafi dasu, amma yadawo musu dasu bayan kwana 3.

Yayinda Quraishawa s**a wayi gari s**a tabbatar da Sayyidina Ali shine a kan gadon Annabi SAW, kuma Annabi SAW ya fita a Makka zai tafi Madina, sai s**a saka Taguwa 100 (Mecen Rakumi) kyauta ga duk Wanda ya kawo Annabi SAW a Raye ko a mace. Haka s**a Gama nemansu Basu ga Annabi SAW da Sahibinsa Sayyidina Abubakar ba Tsawon wannan kwanakin.

Bayan sunyi kwana 3 a cikin Kogon 'Saur', sai Dan jagoran nasu ya dawo, yazo musu a ababen hawansu k**an Yadda s**a fada masa s**a dauki hanya domin cigaba da Hijirarsu zuwa Madina.

Tsayawa da s**ayi kwana uku a Kogon'Saur' sunyi ne domin su batar da kafa, Quraishawa suyi tunanin sun isa Madina, su daina nemansu sukuma sai su tafi a tsanake.

National Editor
Fityanu Media

18/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 18

Daga: Yaseen Bin Hussain

KAFIREN MAKKA SUNYI NIYYAN KASHE ANNABI SAW.

Bayan ganin yadda Addinin Musulunci yake Kara samun karbuwa da yaduwa a sashin Larabawa, musamman yadda mutanen garin Madina suke Shiga Addinin Musulunci da kuma Alwashin Musulman Madina na kare Annabi Muhammad SAW daga duk wata cutarwa, sai Kafiren Garin Makka s**ayi ittifaqin Kashe Annabi Muhammad SAW.

Sun zartar da wannan hukunci ne bayan Zama da s**ayi da qabilun dake Makka, inda s**a yanke hukunci cewa kowace Qabila zata bada Mutum daya sai suyi masa rubdugu gaba dayansu tayadda baza'a gane Dan wata Qabilane ya kasheshi ba. Idan ba'a gane Wanda ya kasheshi ba kuma, baza'a zargi Qabila daya ba, b***e a dauki Mataki a kanta, saidai a zargi dukkan Qabilun.

Da Annabi Muhammad SAW yasamu labarin wannan Makircin nasu, sai Allah SWT yayi masa Umarni yayi hijira cikin wannan daren zuwa Madina, nan take yayiwa Sayyidina Aliyu bin Abi-Talib izini daya kwanta a makwancinsa, shikuma ya fita domin Hijira zuwa Madina Kaman yadda Allah SWT yayi masa Umarni.

Allahu Akbar Allah maiyin yadda yaso, Allah ya Kara mana kaunar Annabi Muhammad SAW da iyalen gidansa Amin.

National Editor
Fityanu Media

18/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 17

Daga: Yaseen Bin Hussain

MUBAYA'AR MUTANEN MADINA A KARO NA BIYU

Wadanda s**a Musulunta daga mutanen Madina Basu gushe suna Kiran Yan uwansu zuwaga Addinin Musulunci bah har sai da wasu dayawa s**a Musulunta a Madina.

A karo na biyu, Mutane 75 ne daga Madina s**ayiwa Annabi SAW Mubaya'a 73 Maza Mata 2. Sunyi Imani da Allah SWT dakuma yin Alqawarin cewa zasu kareshi daga Sharri da cutarwan Kafiren Makka. Sun bukaci Annabi SAW da Sahabbansa dasu kauro Madina zasu basu Kariya.

Bayan komawarasu Madina dayawa daga cikin Sahabban Annabi SAW sun bisu Madina s**a tare a Madina Baki daya, sai ya kasance Annabi SAW da wasu kadan daga cikin Sahabbai ne suke Makkka.

Haka akaci gaba da kira zuwaga Addinin Musulunci a Makka da Madina Baki daya.

National Editor
Fityanu Media

18/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 16

Daga: Yaseen Bin Hussain

MUBAYA'AR MUTANEN MADINA A KARON FARKO.

A cikin Shekara ta 12 bayan Aiken Annabi Muhammad SAW, Mutane 12 daga Madina s**a hadu da Annabi SAW a wajen (Aqabatul Ula) Aqaba ta Farko a Ranakun Mina.

Wannan mutane 12 daga Madina sun yiwa Annabi SAW mubaya'a cewa bazasu hada Allah SWT da kowaba, bazasuyi Sata ko Zina ba, da Sauran munanan ayyuka na zunubi duk bazasuyi ba. Sun Musulunta kuma zasuyi aiki irin na Musulunci.

Dazasu koma Madina Annabi SAW ya hadasu da Sahabinsa dazai cigaba da koyar dasu Alqur'ani Maigirma da Sauran abubuwan da s**a shafi Addini. Haka s**aci gaba da kiran Yan uwansu zuwa ga Addinin Musulunci.

National Editor
Fityanu Media

17/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 15

Daga: Yaseen Bin Hussain

TAFIYAR ANNABI SAW ZUWA 'DA'IFAH

Bayan Wafatin Matarsa Sayyada Khadija wacce take taimaka masa da Dukiyarka da shawarwari masu kyau domin cigaban Addinin Musulunci, dakuma Rasuwar Baffansa Abu-Talib wanda shine Mai kareshi daga cutarwar Kafiren Makka, sai cutarwar tayi tsanani sosai domin yanzu babu Wanda zai tsaya masa. Ganin haka sai Annabi Muhammad SAW ya fita zuwa 'Da'ifah.

Annabi SAW yaje 'Da'ifah tare da Zaidu Bin Harisata. Da isar Annabi SAW Garin'Da'ifah, ya kirasu zuwa ga Addinin Musulunci yakuma nemi suyi Imani da Allah, su bashi Kariya daga cutarwar Kafiren Makka. Bayan haka yakuma nemi da zai zauna tare dasu, domin ficewa daga wahalar da Musulmai Kesha a Makka.

Mutanen 'Da'ifah sunyi watsi da Kiran Annabi Muhammad SAW s**a kuma Walakantashi. Sukasa bayinsu da 'yan iskan garin 'Da'ifah dasuyita Zagin Annabi SAW harda Jifan Annabi SAW da Duwarwatsu. Innalillahi Wa'innan Ilaihir-Raji'un!!! _"Ina ace inanan Lokacin in Dada rayuwata domin kare Annabi SAW"_

Sunyita Jifan Annabi SAW har s**aji masa raunuka, jini na fita daga jikin Annabi SAW. Mala'ika yazo masa Yana butakar Annabi yayi izini a hallaka mutanen garin, Amma Annabi SAW yace "Allah ka shirya mutanena domin basusan wayeniba".

Wannan duk yafarune a shekara ta 10 bayan Aiken Annabin Rahama SAW. A hanyarsa ya hadu da Aljanu 8 wadanda s**a Musulunta.

Allah Ka daukaka Addinin Musulunci a dukkan fadin Duniya, Allah kaga bayan duk Wanda ke cutar da Musulmai da Musulunci. Amin.

National Editor
Fityanu Media

17/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 14.

Daga: Yaseen Bin Hussain

RASUWAR MATARSA KHADIJA DA BAFFANSA ABU-TALIB.

A shekara ta 10 bayan Aiken Annabin Rahama SAW, Qabilu 5 na Quraishawa s**a yanke hukuncin janye alqawarin da s**ayi na sanyawa Annabi SAW da Sahabbansa Takunkumi. Sai Annabi Muhammad SAW ya Sahabbansa s**a fita daga Takunkumin da suke ciki na Kimanin Shekaru 3, (Abinci ko wani abun more rayuwa baya zuwa musu, har Saida s**a Fara cin ganyayen bishiya.) Subhanallah!. A Wannan Lokacin Shekarun Annabi Muhammad SAW 49 wasu sunce 48.

Bayan fitarsu daga wannan Takunkumin da watanni, Baffansa Abu-Talib yarasu, bada jimawaba Matarsa Sayyada Khadijatul Kubra itama tayi Wafati. Annabi Muhammad SAW yayi jimami kwarai da gaske na rashinsu domin irin gudumawar dasuke bayarwa wajen daukaka Addinin Musulunci, Har yakirayi wannan Shekarar da Aamul-Huzni (Shekarar Bakin Ciki).

Jim kadan bayan Rasuwar Baffansa da Matarsa, sai cutarwar Kafiren Makka yayi yawa gareshi, Wanda hakan Shi yajawo fitarsa zuwa Garin 'Da'ifah.

Allah muna rokonka kabamu juriya musamu nasara Kan dukkanin jarabawar daka jarrabemu. Amin.

National Editor
Fityanu Media

17/11/2020

MAULUD 2020 Kashi na 13

Daga: Yaseen Bin Hussain

HIJIRA NA BIYU ZUWA HABASHA.

Yayinda Kafuren Makka s**a Kara tsananta cutarwa ga Annabi Muhammad SAW da Sahabbansa, sai Annabi SAW ya sake musu umarni dasu kara yin Hijra zuwa Habasha Karo na biyu.

Maza 83 ne da Mata 18 zukayi hijira a karo na biyu zuwa Habasha daga cikinsu harda Ja'af Bin Abi-Talib. Sarkin Habasha Najashi ya karramasu ya kuma karbesu cikin mutuntawa.

Yayinda Kafuren Makka s**aji labarin hijirar das**ayi sai tura Amr bin Al-As da Abdullahi bin Zubair Al-Makzumiy da tarin kyauta domin su kaiwa Sarki Najashi ya koro musu Musulmai da s**a Musulunta daga garinsa, Amma Sarki Najashi yaqi ya karba Kyautar nasu yakuma qi ya Bari su tafida Sahabban Annabi SAW.

Ganin haka sai s**a Kara matsa lamba wajen cutar da Annabi SAW da Sahabbai a Makka, har takaiga sun yake duk wata alaqa da Wanda ya Musulunta ba'a sayar musu da Abinci, ba'ayin duk wani Abu dasu, s**ace inda anaso su janye wannan cutarwar dasukewa Annabi SAW da Sahabbai sai an Sallama musu Annabi SAW sun kasheshi. (Subhanallah). Dukkanin Qabilar dake Makka sun yarda s**a rubuta s**a rataye a Dakin Ka'abah.

Wannan duk ya farune a shekara na 9 bayan Aiko Annabi Muhammad SAW. Allah Ka dauke mana dukkanin wahalar damuke ciki zahiri da boye, Alfarman Annabi Muhammad SAW. Amin

National Editor
Fityanu Media

17/11/2020

MAULID 2020 Kashi na 12

Daga: Yaseen Bin Hussain

HIJIRAN FARKO ZUWA HABASHA

Cikin Shekara ta 5 bayan Aiko Annabi Muhammad SAW, yayinda Kafuren Makka s**aga Addinin Musulunci ya fara daukaka bayan Musuluntar da Sayyidina Hamza da Sayyidina Umar s**ayi. s**aga cewa yanzu bazasu iya cutar da Annabi SAW cikin sauki ba, sai saka fara cutar da Sahabbansa musamman wadanda ba 'ya'yan manya bane. ganin haka sai Annabi Muhammad SAW yayi musu izini dasuyi Hijra zuwa Habasha.

Sahabban Annabi SAW 12 ne Maza da Mata 4 s**ayi Hijirar Farko zuwa Habasha, cikin su harda Sayyidina Usman bin Affan, da Matarsa Sayyidatuna Rukiyyah 'yar Annabi Muhammad SAW. Sunyi tafiyar Hijirar daga Makka zuwa Habasha.

Sarkin Habasha na Lokacin Najashi mutumin kirki ne, mai Adalci, son mutane da son Zaman Lafiya. Ya karbesu hanu bibbiyu yakuma Kula dasu batare da cutar dasu ko Bari wani Abu ya cutar dasu ba.

Allah domin wannan Hijirar da Sahabbai s**ayi Kasa mu samu saukin wahalar damuke cikin kabamu lafiya da Zaman Lafiya Amin.

National Editor
Fityanu Media

30/10/2020

MAULID 2020 Kashi na 11

Daga: Yaseen Bin Hussain

BAYYANA DA'AWAR ANNABI MUHAMMAD SAW.

Bayan Allah SWT yayi masa irizini daya kirayi Danginsa Makusanta a Farko kafin ya bayyana Da'awar Addinin Musulunci. Cikin Shekara ta Uku (3) sai Allah yai masa izini daya bayyana Da'awar Addinin Musulunci ga daukacin Al'ummah.

Annabi Muhammad SAW ya bayyana Da'awarsa yakira Quraishawa zuwa ga kadaita Allah SWT dasu daina Bautar Gumaka, su daina Bautar abubuwan da bazasu amfanesu Duniya da Lahira ba, suzo zuwaga Halal su bar Haram, subar Ayyukan Sharri suyi ayyukan Alheri. Daga cikinsu wasu sunyi Imani dashi wasu kuma sunqishi, sunyi gaba dashi, sun kuma cutar dashi cikinsu k**ar; Baffansa Abu-Lahab Abu-Jahal da sauransu.

Annabi SAW yacigaba da jure walaharwa, cutarwa makircin da s**ayita masa, yacigaba da Kiran Al'ummah zuwa ga Allah SWT har Lokacin da yayiwa Sahabbai izini dasuyi Hijra zuwa Habasha (Wannan itace Hijira ta Farko).

National Editor
Fityanu Media

30/10/2020

MAULID 2020 Kashi na 9

Daga: Yaseen Bin Hussain

FARKON ANNABTAR ANNABI MUHAMMAD SAW (Aikoshi a Matsayin Annabi da Wahayin Farko)

Yayinda Annabi SAW ya kusanci Shekara 40 sai ya yanke saduwa da mutane ya kasance yana Kebewa yana bautar Allah (Halwa) a Kogon Hira. Wani Lokaci Yana Kwana goma zuwa wata daya, duk sanda ya fito sai ya koma gida wajen Matarsa Sayyada Khadijatul Kubra domin ya karbo Abinci, sai ya Kara komawa. haka Annabi SAW yakasance cikin bautar Allah har Allah ya Aikoshi a Matsayin Annabi.

Yayinda yakai Shekara 40, sai Mala'ika Jibrilu yazo masa Yana ta bautar Allah cikin Kogon Hira, sai yace Masa "Iqra'a" (Yikaratu) ya fada masa sau uku, Annabi SAW yana mayar masa da Amsar cewa "Ni bamai karatu bane". Sai ya saukar masa Ayoyi biyar da farkon Suratul Alaq.

Bayan nan Annabi SAW ya koma gida wajen Matarsa Sayyada Khadijatul Kubra ya fada Mata abunda yafaru, Zuciyarsa na tuna ganin Mala'ika Jibrilu yadayi. Sai Matarsa Sayyada Khadijatul Kubra tace tana tsammanin wannan Mala'ika ne Wanda yake kawo sakon Allah zuwa Annabawa. Daga wannan Wahayin Annabi SAW yacigaba da karban wahayi na Alqur'ani Maigirma daga wajen Mala'ika Jibrilu.

Allah ya bamu Albarkacin Alqur'ani Maigirma yakuma samu muyi koyi da koyarwansa. Allah Kasa Alqur'ani ya cecemu. Amin.

National Editor
Fityanu Media

30/10/2020

MAULID 2020 Kashi na 10

Daga: Yaseen Bin Hussain

DA'AWAR ANNABI MUHAMMAD SAW CIKIN SIRRI.

Yayinda Allah yai masa wahayi cikin Suratul Muddassir "Tashi Kayi Wa'azi..." Sai Annabi SAW ya fara kira zuwaga Allah cikin sirri ya fara a iyalansa da wasu daga cikin Abokansa.

Wanda ya fara Musulunta cikin Maza shine Sayyidina Abubakar, A Yara Maza kuma Sayyidina Ali bin Abi-Talib, a Mata Sayyada Khadijatul Kubra Matar Annabi Muhammad SAW, a bayi kuma Sayyidina Bilal.

Sayyidina Abubakar yayi kira ga Abokansa domin Shiga Addinin Musulunci, dayawa daga cikinsu sun amsa masa. Daga cikin harda Sayyidina Usman bin Affan, Zubair Bin Auwam, Abdulrahman Bin Auf, Sa'adu Bin Abi-waqqas da sauransu.

Haka Annabi SAW yacigaba da Kira cikin sirri wa Danginsa da Abokansa har yakai Shekara 3 Yana Da'awar, Sai Allah yai masa izini daya bayyana Da'awar Addinin Musulunci.

Muna Tawassuli da Kiran da Annabin Rahama SAW yayi da Imani sahabbai Allah ya Kara mana shiriya da Imani Amin.

National Editor
Fityanu Media

26/10/2020

MAULUD 2020 kashina 8

Daga: Yaseen Bin Hussain

AUREN ANNABI SAW DA SAYYADA KHADIJA (RTA)

Bayan Dawowar Annabi SAW Makka daga Kasuwanci da yaje garin Sham, ganin ribar da aka samu Wanda ba'a taba samu bah, dakuma gaskiya da Amanarsa SAW, Sayyada Khadijatul Kubra ta nemi Annabi SAW daya Aureta. Wannan Lokacin Sayyada Khadijatul Kubra nada Shekaru 40 shikuma Annabi SAW nada Shekaru 25.

Annabi SAW ya amince yakuma Aureta. Ta zauna tare da Annabin Rahama SAW cikin ladabi da biyayya, tayiwa Addinin Musulunci hidima irin wacce ba'a taba samun Mace datayi irinta bah. Bata taba batawa Annabi SAW Rai ba.

Yayin zamansu da Annabin Rahama SAW, itace Matarsa ta Farko kuma Bai Auri wata bah sai bayan Rasuwarta. Sayyada Khadijatul Kubra ita ta haifi 'ya'yan Annabi SAW duka BANDA Ibrahim.

Ta haifi Maza 2 Mata 4 k**ar haka: Abdullahi, Alqasim, Mata sune: Fadimatu, Rukiyyatu, Zainabu. Ummu-Kulsoom. dukkanin su sun rasu kafin Wafatin Annabi SAW BANDA Sayyada Fadima AS.

Allah ya bamu Albarkacinsu bijahi Nabiyina Muhammad SAW. Amin

National Editor
Fityanu Media

26/10/2020

MAULIDI 2020 Kashi na 7

Daga: Yaseen Bin Hussain

TAFIYARSA ZUWA SHAAM

Yanada Shekaru 18 a rayuwarsa ta Duniya Baffansa Abu-Talib yayi tafiya dashi zuwa sham domin Kasuwanci, yayinda s**a isa 'Busra' Wani Malamin Yahudawa 'Bahira' ya ganshi (SAW) sai yayiwa Baffansa Abu-Talib isahara da yakoma dashi Makka domin Karda Yahudawa suganshi zasu cutar dashi. Ya kuma bawa Baffansa Abu-Talib labarin cewa zai Zama wanni Babban Mutum nan gaba, sai s**a koma Makkah.

Yana da Shekaru 25 Annabi (SAW), sai Sayyada Khadijatu Bintu Khuwailid taji labarin Aminci, Amana da Gaskiyar Annabi SAW, sai taso suyi kasuwanci tare. akayi kasuwanci akasamu ribar da ba'a taba samu bah Albarkacin Annabi SAW.

Sunyi tafiyar tareda wani bawanta 'Maisarah' Wanda yake Kula da irin Mu'ujizozin dake faruwa da Annabi SAW yayin tafiyar tasu. Bayan sun dawo da riba mai yawa kuma bawanta yabata labarin abubuwan Al'ajabi das**a faru yayin tafiyar, sai Sayyada Khadijatul Kubra tayi kwadayi domin Auren Annabi SAW.

National Editor
Fityanu Media

24/10/2020

MAULIDI 2020 Kashi na 6

Daga: Yaseen Bin Hussain

TARIHINSA (SAW) KAFIN ANNABTA.

Annabi SAW yayi fice cikin matane kafin Annabta da Gaskiya, Kaskan dakai, da Rikon Amana. Sun kasance suna bawa Annabi SAW kudadensu da Sauran abubuwa domin ya ajiye musu saboda Amanarsa. Tsagwarar Amanarsa ce tasa s**a saka masa suna 'Al-Amin' "Amintacce".

Shi Annabi SAW bai taba Shan giya ba, bai taba bautar gunki ba, bai taba c**a, ko Zina ba, Annabi SAW baitaba sabawa Allah ba.

Yanada Shekaru 35 a rayuwarsa ta Duniya quraishawa s**a sabunta ginin Dakin Ka'abah, sai s**ayi jayayya Kan Wanda zai maida 'Hajarul-Aswad' wajensa, Annabi SAW sai ya shinfida Mayafinsa aka daura 'Hajarul-Aswad' akai sai yace Shugaban kowace Qabila ya k**a sai aka daga, da aka isa wajen sai Annabi SAW yasa hanunsa mai Albarka ya dauki Hajarul-Aswad aje a wajen da yake yau. Shikenan ya raba fada.

Haka Annabi SAW ya kasance kafin Annabta da halaye masu matukar kyau. Allah ya bamu irin wadannan halayya Alfarman Annabi SAW. Amin

National Editor
Fityanu Media

23/10/2020

MAULIDI 2020 Kashi na 5

Daga: Yaseen Bin Hussain

TASHIN (girman) ANNABI SAW

Annabi Muhammad SAW ya tashi yasamu mahaifinsa ya rasu a Madina kafin haihuwarsa, kuma mahaifinsa Sayyidina Abdullahi baibar masa dukiya Mai tarin yawa bah. Yana Dan Shekara Shida (6) mahaifiyarsa Sayyada Aminatu ta rasu a hanyar Dawowa daga Madina sai aka bunneta a wani gari 'Abwa'a' (garine tsakanin Makka da Madina).

Kakansa Abdul-Mutallib shiyaci gaba da renonsa da kulawa dashi, Abdul-Mutallib yana son Annabi Muhammad SAW sosai tsabar so da kulawa da yakewa Annabi SAW duk inda zaije tare suke zuwa, bayan shekara biyu (2) Allah yayiwa Abdul-Mutallib Rasuwa Annabi SAW nada Shekaru Takwas (8).

Banyan rasuwar Kakansa Baffansa Abu-Talib ne yaci gaba da Kula dashi. Abu-Talib ya kasance ba mai yawaitar Arziki bane Amma saboda daukan reno da kulawa da yayi na Annabi SAW, Allah ya yawaita masa Arzikinsa, yasamu Akhairai da yawa.

Muna Tawassuli da Annabin Rahama SAW Allah ya yawaita mana Akhairai Duniya da Lahira. Amin.

National Editor
Fityanu Media

23/10/2020

MAULIDI 2020 part 4

Daga Yaseen Bin Hussain

SHAYARWA DA RENONSA SAW

Mahaifiyarsa Sayyada Aminatu ta shayar dashi na tsawon kwanaki, sai kuma Suwaibah baiwar Baffansa Abu-Lahab, sannan s**a Sama masa Mai shayarwa k**an yadda Al'adar Larabawa take wajen shayarwa.

Halimatus-Sadiya itace ta karbi shayar da Annabin Rahama SAW zuwa garinta domin ya samu fasaha da dabarbaru na mutanen kwauye.

Garin da Halimatus-Sadiya take garine Mai karancin abubuwan more rayuwa da Albarka na kayan Noma, Kiwo da Kasuwanci, Albarkacin daukan Annabi Muhammad SAW da Halimatus-Sadiya tayi zuwa wannan garin Allah ya saukar da Albarka Mai yawa a garin, s**a samu Albarka da Arziki Mai yawa sosai.

Ta shayar dashi tsawon Shekaru biyu, sai ta nemi Alfarma wajen Mahaifiyarsa Sayyada Aminatu cewa tanaso Annabi SAW yacigaba da Zama a wajenta, Sayyada Aminatu ta amince Mata, ya Kara Shekaru biyu a wajen Halimatus-Sadiya. Yanada Shekaru Hudu (4) Halimatus-Sadiya ta Mayar dashi wajen Mahaifiyarsa Sayyada Aminatu.

Allah muna tawassuli da Annabinka SAW ka nama Fatahi na dukkanin Albarka zahiri da badini. Amin.

National Editor
Fityanu Media

Address

Jos

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tijjaniya online tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Tijjaniya online tv:

Share

Category


Other TV Channels in Jos

Show All

You may also like