Lajnar Tabligh Yola

Lajnar Tabligh Yola Domin yada manufofin Harkar Musulunci a Nigeria da jagoranta Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) musamman yan

Sallah a daren 5 ga watan Sha'aban - raka'a 2 Fatiha 1, Suratul Ikhlas 500x  kowace raka'a.Fa'idah :Allah zai biya masa ...
03/02/2025

Sallah a daren 5 ga watan Sha'aban - raka'a 2 Fatiha 1, Suratul Ikhlas 500x kowace raka'a.
Fa'idah :
Allah zai biya masa bukatun sa 1000 na duniya da lahira. Allah zai bashi gidaje a aljanna adadin Taurari da ke sama .

*Daren 3 ga Sha'aban*Sallah Raka'a 2 - Fatiha 1x, Suratul Ikhlas 15x a kowace Raka'a.Fa'idah 💎  Allah zai bude masa kofo...
01/02/2025

*Daren 3 ga Sha'aban*

Sallah Raka'a 2 - Fatiha 1x, Suratul Ikhlas 15x a kowace Raka'a.

Fa'idah

💎 Allah zai bude masa kofofin aljanna guda 8.

💎 Zai kuma rufe masa kofofin wuta 7

💎 Zai suturta shi da tufafi na ado guda 1000, da Kambi 1000.

®️SahibulAsrWazZamaanInstituteYola - 20250201/1446H0702_1302

[email protected]

🌹WATAN SHA'ABAN 🌖🌹Sallar daren 2🌹Raka'a  50🌹 Fatiha 1🌹Kulhuwa, Falaqi,Nasi 1A kowace Raka'a.*🌹Yazo a rayuwa cewa duk Wan...
31/01/2025

🌹WATAN SHA'ABAN 🌖
🌹Sallar daren 2
🌹Raka'a 50
🌹 Fatiha 1
🌹Kulhuwa, Falaqi,Nasi 1
A kowace Raka'a.

*🌹Yazo a rayuwa cewa duk Wanda yayi Allah zaiyi Umarni da kar a rubuta masa Zunubi har Shekara ta zagayo, zai canja masa Zunubansa zuwa Ladan masu Ibadar Sama da Kasa ,Manzon Allah (S) Yana cewa na Rantse da Wanda ya aiko ni da Annabata da gaskiya babu Wanda zai gujema Wannan Daren sai Shaqiyi, Munafiki ko Fajiri,An anbata falala mai yawa.*

An ruwaito Daga Manzon Allah sawa cewa : Wanda yayi azumi kwanaki 3 na farkon Watan Sha'aban, ya tsaya Sallah Raka'o'i 2...
30/01/2025

An ruwaito Daga Manzon Allah sawa cewa : Wanda yayi azumi kwanaki 3 na farkon Watan Sha'aban, ya tsaya Sallah Raka'o'i 2 yana karanta Fatiha 1x, Suratul Ikhlas 11; _"Allah zai kare shi daga sharrin wadanda ke sararin samaniya da wadanda ke doron ƙasa, da sharrin Iblis da rundunarsa tare da sharrin duk wani Mai ikon azzalumi. Na rantse da wanda Ya aiko nemi da gaskiya a matsayin Annabi, Allah Zai yafe masa laifuffukan sa 70,000 da ke tsakanin sa da Allah SWT. Kuma Allah zai kiyaye shi daga azabar kabari da tsanani da ke tattare da ita."_

- 20240130/14460730_1534

[email protected]

Sallah Raka'a 2, Za a karanta Fatiha 1x, Suratul Ikhlas 30 a kowace Raka'a. Sai mutum yace -  _"Ya Allah wannan alkawari...
30/01/2025

Sallah Raka'a 2, Za a karanta Fatiha 1x, Suratul Ikhlas 30 a kowace Raka'a. Sai mutum yace - _"Ya Allah wannan alkawari na gare Ka har ya zuwa ranar tashin kiyama"_

Fa'idah - *Kariya daga Iblis da rundunarsa*

💎 *_Allah zai ba shi ladan Siddiƙai._*

Daga Littafin Iqbalul A'amal

- 20250130/1446H0730_1430

[email protected]

*_Faidah_**_"Wanda ya yi Sallah raka'a 10 - Fatiha 1 Suratul Ikhlas 10 a kowace raka'a, Allah zai bashi Janatul Firdaws ...
29/01/2025

*_Faidah_*

*_"Wanda ya yi Sallah raka'a 10 - Fatiha 1 Suratul Ikhlas 10 a kowace raka'a, Allah zai bashi Janatul Firdaws Mai birane 7 . Zai fito daga cikin kabari fuskarsa na kyalli kamar farin Wata. Zai ketare Siraaɗi kamar walkiya tare da kubuta daga wutar jahannama. Godiya ta tabbata ga Allah"_*

WATAN RAJAB:Sallar daren 28Sallah raka'a 12Fatiha 1Suratul Aala 10×Suratul Qadr 10×a kowace rakaaZa'ayi salatin Annabi 1...
27/01/2025

WATAN RAJAB:
Sallar daren 28

Sallah raka'a 12
Fatiha 1
Suratul Aala 10×
Suratul Qadr 10×
a kowace rakaa
Za'ayi salatin Annabi 100×
Istigfari 100×
bayan kammalawa.

🌹Kwaidaitarwa

Yazo a ruwaya cewa duk wani wanda yayi wannan Sallar Allah zai rubuta masa Ladan Ibadar Mala'ika

🌹Domin karin bayani:
Littafin Dhiya'ussalihin.
Daga Iqbalul aamal

*Sallah a daren 27 ga watan Rajab* Raka'a 12 : Fatiha 1 da Surah 1💎 Idan an idar da Sallah, sai a karanta suratul Ikhlas...
26/01/2025

*Sallah a daren 27 ga watan Rajab*
Raka'a 12 : Fatiha 1 da Surah 1

💎 Idan an idar da Sallah, sai a karanta suratul Ikhlas 4, Suratul Falaq 4, Suratul Nas 4.

🟢 *_La'ilaha Allah Wallahu Akbar wal hamdulillah Wasu ya Allah Walahaula Waquwwata Illabillahil Aliyyil Azeem_* 4x

Sai mutum yayi addu'a yadda yake bukata.

- 20250126/1446H0726_1417

[[email protected]]

*Daren 27 ga Rajab, daren Yaumul Mub'ath* _(Daren da a aiko Manzon Allah sawa)_📌 Wannan dare na da muhimmanci matuƙa, Da...
26/01/2025

*Daren 27 ga Rajab, daren Yaumul Mub'ath* _(Daren da a aiko Manzon Allah sawa)_

📌 Wannan dare na da muhimmanci matuƙa, Dare ne Mai tarin Albarka; raya wannan dare na da lada tamkar na shekara 60 na kyawawan ayyuka.

💎 Karanta - Suratul Fatiha 7x, Falaq 7x, Nas 7x, Qadr 7x, Ayatul Kursy 7x

الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي لَمْ يَتَّخِذْ وَلَدًا وَلَمْ يَكُن لَّهُ شَرِيكٌ فِي الْمُلْكِ وَلَمْ يَكُن لَّهُ وَلِيٌّ مِّنَ الذُّلِّ ۖ وَكَبِّرْهُ تَكْبِيرًا﴾
[ الإسراء: 111]

- 20250126/1446H0726_1422

[[email protected]]

*Fa'idah*"Wanda ya yi wannan Sallah - Raka'a 12 da Fatiha 1 da Ikhlas 40 ko 4 , zai yi musafaha da Mala'ika; wanda ya yi...
25/01/2025

*Fa'idah*
"Wanda ya yi wannan Sallah - Raka'a 12 da Fatiha 1 da Ikhlas 40 ko 4 , zai yi musafaha da Mala'ika; wanda ya yi musafaha da Mala'ika zai tsallake tsayawa a Siraɗi, wurin hisabi da muhallin Mizani (Awon sakamako). Allah zai aiko Mala'iku 70 da za su roka masa gafara ana rubuta masa ladan. Kuma za su riƙa tsarkake Allah a madadin sa. Duk lokacin da ya motsa daga wannan muhalli sai su ce - _'Allah Ya gafarta masa.'_ "

- 20240125/1446H0725_1534

[email protected]

WATAN RAJAB:Sallar daren 25Sallah raka'a 20 ,Tsakanin Magrib da Isha'i  ,kowacce raka'a Fatiha 1 da Amanarrasulu zuwa ka...
24/01/2025

WATAN RAJAB:
Sallar daren 25

Sallah raka'a 20 ,Tsakanin Magrib da Isha'i ,kowacce raka'a Fatiha 1 da Amanarrasulu zuwa karshen Suratu Baqara 1, da Kuma Qulhuwallhu Ahad 1

🌹Kwaidaitarwa

An ruwaito cewa "Duk wanda yayi wannan Sallah bazai tashi daga inda yake ba face Allah ya gafarta masa Zunubansa, Sannan zai kare shi tare da Iyalansa da Kuma Dukiyarsa.

🌹Domin karin bayani:
Littafin Dhiya'ussalihin.
Daga Iqbalul aamal

_"Wanda ya yi Sallah a daren 24 ga watan Rajab raka'a 40 - Fatiha 1, Ayar Amanar Rasul 1 da Suratul Ikhlas 1, Allah Zai ...
23/01/2025

_"Wanda ya yi Sallah a daren 24 ga watan Rajab raka'a 40 - Fatiha 1, Ayar Amanar Rasul 1 da Suratul Ikhlas 1, Allah Zai rubuta masa lada 1000 kuma a kankare masa mummunan aiki 1000. Za a daukaka darajar sau 1000. Mala'iku 1000 za su sauka daga samaniya suna roka masa Allah. Allah zai azurta shi da aminci duniya da lahira kai ka ce ya riski daren_ *Lailatul Qadr*"

*Sallah a daren 23 ga watan Rajab*_"Wanda ya yi Sallah raka'a 2 bayan sallar Isha'i; ya na . Fatiha 1, Suratul Dhuha 7x,...
22/01/2025

*Sallah a daren 23 ga watan Rajab*

_"Wanda ya yi Sallah raka'a 2 bayan sallar Isha'i; ya na . Fatiha 1, Suratul Dhuha 7x, Allah zai bashi daraja da kowace harafi da ya karanta a Aljanna,tare da ladan Hajji 70x gami da ladar halartar jana'iza 1000 da ziyartar marasa lafiya 1000. Dadin dadawa har da ladar biyan buƙatar mabuƙata Musulmi 1000"_

Yazo a ruwaya cewa:Duk wanda yayi wannan Sallar, Allah zai umarci Mala'iku masu rubutun lada da zunubi kan cewa kada su ...
21/01/2025

Yazo a ruwaya cewa:Duk wanda yayi wannan Sallar, Allah zai umarci Mala'iku masu rubutun lada da zunubi kan cewa kada su rubuta masa zunubi har shekara ta zagayo, kuma su yi ta rubuta masa lada har Shekara ta zagayo".

WATAN RAJAB:Sallar daren 21.Raka'a 6Fatiha 1.Suratul Qadr 10a kowace raka'a🌹Kwadaitarwa:*_"Allah zai umurci Mala'iku ( K...
20/01/2025

WATAN RAJAB:
Sallar daren 21.

Raka'a 6
Fatiha 1.
Suratul Qadr 10
a kowace raka'a

🌹Kwadaitarwa:
*_"Allah zai umurci Mala'iku ( Kiraman Katibeen) da kar su rubuta mummunan aiki da ya yi har shekara ya kewayo. Na rantse da wanda ya aiko Ni a matsayin Manzo , duk masoyi na kuma wanda ke son Allah SWT ya yi kokarin yin wannan Sallah; idan ba zai iya tsayawa ba, toh ko a zaune ya yi su. Allah zai basu wannan kyautar, ya kuma sanar da Mala'iku ya gafarta mu su."_*

🌹Domin karin bayani:
Littafin Dhiya'ussalihin.
Daga Iqbalul aamal

Yazo a ruwaya ewa duk wani wanda yayi wannan Sallar Allah zai bashi ladan Annabi Ibrahim da Annabi Musa (As) da Annabi Y...
19/01/2025

Yazo a ruwaya ewa duk wani wanda yayi wannan Sallar Allah zai bashi ladan Annabi Ibrahim da Annabi Musa (As) da Annabi Yahaya da Kuma Annabi Isa (As) Kuma babu wani Aljanin da Zai Shafesa Kuma Allah zai dubeshi da Rahamarsa.

18/01/2025
WATAN RAJAB:Sallar daren 16.Raka'a 30Fatiha 1.Qulhuwa 10a kowace raka'a🌹Kwadaitarwa:Yazo a ruwaya Manzon Allah Yana cewa...
15/01/2025

WATAN RAJAB:
Sallar daren 16.

Raka'a 30
Fatiha 1.
Qulhuwa 10
a kowace raka'a

🌹Kwadaitarwa:

Yazo a ruwaya Manzon Allah Yana cewa duk wani wanda yayi wannan Sallar bazai Kammala Sallar ba harsai an bashi ladan Shahidai 70,Kuma Zaizo Ranar alkiyama Hasken sa na Haskaka Taron Kiyama Kamar abinda ke Tsakanin Makka da Madina, Allah zai Kubutar dashi daga Shiga Wuta Sannan zai Kubutar dashi daga Munafinci, zai Kuma dauke mishi azabar kabari.

🌹Domin karin bayani:
Littafin Dhiya'ussalihin.
Daga Iqbalul aamal

Address

Jimeta
16

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Lajnar Tabligh Yola posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Lajnar Tabligh Yola:

Videos

Share